"Babu Mai Dakatar da Mu," An Shirya Kawo Wa Tinubu, APC Miliyoyin Ƙuri'u a Kano a 2027

"Babu Mai Dakatar da Mu," An Shirya Kawo Wa Tinubu, APC Miliyoyin Ƙuri'u a Kano a 2027

  • Fa'izu Alfindiki ya bayyana cewa yana da yaƙinin jam'iyyar APC za ta samu nasara a zaɓukan 2027 tun daga sama har ƙasa a Kano
  • Jigon APC ya ce ƴan Arewa sun waye, ba za su yarda wasu ƴan siyasa su yaudare su da kalaman ƙabilanci ko lɓangaranci ba
  • Ɗan siyasar ya ce duk masu yunkurin daƙile tazarcen Shugaba Tinubu sun makara domin ƴan Najeriya sun gamsu da salon mulkinsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Jigon APC a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya, Fa'izu Alfindiki ya bayyana cewa lokacin yaudarar jama'a da zargin ƙabilanci ya wuce a siyasa.

Ya ce masu ƙoƙarin gurɓata tunanin ƴan Arewa da ƙabilanci don hana shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu tazarce a 2027 sun makara, domin mutane sun waye.

Kara karanta wannan

Sabuwar rigima ta ɓarke a haɗakar su Atiku, jigon ADC ya naɗa kansa shugabanci

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da Faizu Alfindiki.
Jigon APC ya ce yana da yaƙainin Tinubu zai yi nazarce a 2027 Hoto: Fa'izu Alfindiki
Source: Facebook

Alfindiƙi ya jaddada cewa babu wanda zai yaudari Arewacin Najeriya cikin sauƙi kamar aka yi a baya, in ji rahoton Tribune Nigeria.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alfindiki ya hango nasarar APC a Kano

Ya ce zaɓen 2027 zai zama na musamman a Kano da ɗaukacin jihohin Arewa, yana mai tabbatar da nasarar Shugaba Tinubu da duka ƴan takarar APC a 2027.

Alfindiki ya ce waɗanda ke amfani da wasu kalamai na ƙabilanci don su samu mulki su sani an wuce nan, ƴan Arewa sun waye kuma sun san bukatunsu na siyasa da kyau.

“Wannan tsohon tsarin siyasa na son kai ba ya amfanar da kowa sai wasu tsirarun mutane da iyalansu. Lokaci ya yi da za mu daina duba ƙabila wajen zaɓen shugabanni.”

Yadda aka shirya tarawa Tinubu kuri'un Kano

Ya tabbatar da cewa jam’iyyar APC ta shirya tsaf domin lashe ƙuri’un Kano don nasarar Shugaba Tinubu a zaɓen 2027, kamar yadda Daily Post ta kawo.

Kara karanta wannan

Ana shirya yadda za a shigo Arewa a kayar da Atiku, Kwankwaso da wasu jiga jigai a 2027

Alfindiki ya bayyana hakan ne a wata liyafar cin abinci da aka shiryawa tawagar masu tallata Tinubu ta kafafen sada zumunta a Kano ranar Laraba.

A taron, ya yaba da ƙoƙarinsu na watanni shida da suka gabata wajen bayyana ayyukan da shugaban ƙasa ya aiwatar ga miliyoyin masu kada ƙuri’a a yankin Arewa.

A cewarsa:

“Taron da muka yi da ku safiyar yau na da nufin farfado da ayyukanku da kuma warware ƙalubale da ka iya tasowa.
"Ina farin cikin cewa watanni shida da suka wuce sun kasance masu ƙalubale amma cike da jarumtaka, kuma sun taimaka wajen ɗaga darajar ƙoƙarin sake zaɓar Tinubu a Kano da Arewa gaba ɗaya.”
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Alfindiki ya sha alwashin tabbatar da nasarar Tinubu da APC a Kano Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Yadda ake tallata Tinubu a Kano da Arewa

Alfindiki, wanda shi ne tsohon shugaban karamar hukumar birnin Kano, ya ɗauki fitattun masu amfani da kafafen sada zumunta domin tallata Tinubu da ayyukansa.

Ya tabbatar da cewa jam’iyyar APC za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin Shugaba Tinubu ya samu ƙuri'un da ake buƙata don lashe zaɓen 2027 cikin sauƙi.

Kwankwaso ya ce Kano ta Kwankwasiyya ce

Kara karanta wannan

"Lokaci ya yi" Gwamnatin Tinubu ta yiwa ƴan bindiga 'tayi' a Arewacin Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Rabiu Kwankwaso ya karbi dubunnan magoya bayan APC da suka sauya sheka zuwa NNPP a Kano.

Tsohon gwamnan nuna cewa NNPP tana da shugabanci na gari, wanda haka ne daya daga cikin dalilan da jama'a ke tururuwa zuwa cikinta.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da APC ta nuna alamun za ta karɓi Kwankwaso hannu bibbiyu idan ya yarda ya baro NNPP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262