2027: Kungiyar ATT Ta Samo Mafita ga Arewa kan Tazarcen Shugaba Tinubu
- Kungiyar Arewa Think Thank (ATT) ta gamsu da kamun ludayin gwamnatin mai girma Bola Ahmed Tinubu
- Ta bayyana cewa shugaban kasan ya aiwatar da ayyuka masu muhimmanci a yankin Arewacin Najeriya
- Kungiyar ta nuna cewa ya kamata a shekarar 2027 yankin Arewa ya rama biki ta hanyar goyon bayan tazarcen Tinubu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Kungiyar Arewa Think Tank (ATT) ta bayyana cewa babu wani dalili da zai hana yankin Arewa goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Kungiyar ATT ta ce Arewa za ta goyi bayan Shugaba Tinubu, duba da ci gaban da gwamnatinsa ta kawo a fannin tsaro da ababen more rayuwa a yankin.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jagoran kungiyar, Muhammad Alhaji Yakubu, ya fitar a ranar Laraba, 30 ga watan Yulin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ATT ta shawarci 'yan Arewa
Muhammad Alhaji Yakubu ya ce mayar da hankalin da Shugaba Tinubu ke yi wajen ci gaban yankin Arewa ya haifar da sakamako mai kyau, wanda ya cancanci ci gaba da goyon bayansa.
"Arewa Think Tank na kira ga mutanen Arewa da su tsaya tsayin daka tare da shugaban kasa kuma su sake zaɓensa a 2027."
"Dole ne mu faɗa wa kanmu gaskiyar magana cewa a halin yanzu, Arewa ba ta buƙatar mulki, sai dai ababen more rayuwa da ci gaban ɗan Adam wanda Shugaba Tinubu ke ci gaba da kawo wa mutanenmu."
- Muhammad Alhaji Yakubu
Wannan sanarwar na zuwa ne bayan wani taron shugabanni da aka gudanar a Kaduna, inda shugabannin siyasa daga Arewa suka yi nazari kan mulkin Tinubu.
Yayin da wasu ke nuna damuwa da talauci da matsalolin tsaro, wasu kuwa sun yaba da wasu manyan shirye-shiryen gwamnatin tarayya da ke mayar da hankali kan Arewa.
ATT ta yabawa Shugaba Bola Tinubu
Muhammad Alhaji Yakubu ya kare nasarorin gwamnatin Tinubu, yana mai cewa matsalolin tsaro da wahalar tattalin arziki, matsaloli ne da aka gada tun kafin zuwan wannan gwamnati, rahoton The Nation ya tabbatar.
"Shawarar mu ga shugabannin Arewa ita ce su daina zagin kowa, su mayar da hankali kan watsi da yankin da aka dade ana yi, wanda Shugaba Tinubu ya zo da niyyar gyarawa."
"Wadannan matsalolin sun dade suna addabar mu, har ma a lokacin da shugabanni 'yan Arewa ke kan mulki.”
- Muhammad Alhaji Yakubu
Ya jaddada cewa ayyuka kamar hanyar Abuja-Kaduna-Kano da layin dogon Kano-Katsina-Maradi na daga cikin hujjar da ke nuna yadda Shugaba Tinubu ke da kishin Arewa.
Yakubu ya ce manufofin Renewed Hope na Shugaba Tinubu sun kawo sabon salo a harkar mulki da ci gaban Arewa.
An bukaci 'yan Arewa su zabi Tinubu
Ya roƙi masu zaɓe na Arewa da su ba wa shugaban kasan ƙarin dama a 2027 domin a samu cikakken sauyi.

Kara karanta wannan
'Yadda Tinubu ya ɗauko gagarumin aiki tun na zamanin Shagari saboda ƙaunar Arewa'
"Arewa ba za ta iya rasa wannan damar ba. Shugaba Tinubu ya nuna kishin yankinmu, kuma dole ne mu mayar masa da alherin da ya yi mana ta hanyar goyon baya.”
- Muhammad Alhaji Yakubu

Asali: Facebook
Onanuga ya magantu kan masu adawa da Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya yi magana kan masu adawa da Shugaba Bola Tinubu.
Bayo Onanuga ya bayyana cewa wasu mutane suna adawa da Shugaba Tinubu ne kawai saboda ya fito daga yankin Kudu.
Ya nuna cewa ya kamata a bar shugaban kasan ya yi wa'adin mulki na shekarar takwas kamar yadda marigayi Muhammadu Buhari ya yi.
Asali: Legit.ng