Shugaban Matasa Ya Fito da Ƙarfi, Zai Nemi Takarar Shugaban Ƙasa a Zaɓen 2027
- Shugaban matasan LP na ƙasa, Kennedy Ahanotu ya bayyana shirinsa na neman kujera lamba ɗaya a Najeriya a zaɓen 2027
- Ahanotu ya ce galibin shugabannin Najeriya da suka yi mulki bayan samun ƴancin kai, sun hau madafun iko ne suna matasa
- Ya ce yana da yaƙinin cewa ya cancanci zama shugaban ƙasa, kuma ya shirya kawo sauyi na zamani a Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban Matasan Jam’iyyar LP, Kennedy Ahanotu, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027.
Hakan ya sa Ahanotu ɗan kimanin shekara 41 ya shiga jerin mutanen da suka nuna sha'awar neman shugabancin Najeriya a zaɓe mai zuwa.

Source: Twitter
Ahanotu ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da ya yi da jaridar The Punch a ranar Talata, 29 ga watan Yuli, 2025.
Shugaban matasa ya shirya canza Najeriya
A cewarsa, Najeriya na matuƙar buƙatar sauyin zamani da rabuwa da tsohon tsarin siyasar da aka jima ana amfani da shi wajen tafiyar da harkokin mulki.
“Na fito takarar kujerar shugabancin ƙasa ne domin gina sabon tubali a Najeriya ta hanyar canza salon shugabanci zuwa na zamani, domin mu gudu tare mu tsira tare."
“A matakin da muke a yau, abubuwa sun rikice matuƙa, dole ne mu latsa maballin farawa daga farko don gina dimokuraɗiyya mai ɗorewa da za ta amfani kowa da kowa a ƙasar nan.”
- Kennedy Ahanotu.
Ahanotu ya tuno matasan da suka mulki Najeriya
Shugaban matasan ya tunatar da cewa mafi yawan shugabannin farko na Najeriya bayan samun ‘yancin kai sun hau madafun iko ne tun suna ƴan shekaru 20 zuwa 30.
Daga cikin ya kafa hujja da tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Yakubu Gowon, wanda ya hau mulki yana da shekaru 29.

Kara karanta wannan
'Ban da Peter Obi': An yi wa Malami wahayi game da mutum 3 da za su fatata a 2027
"Ina da yakinin cewa ina ɗauke da nauyin jagoranci mai tasiri, don haka babu lokaci mafi dacewa da zan fara bin wannan mafarki da burina fiye da yanzu,” inji Ahanotu.
Shugaban matasan ya shirya murabus a LP?
Duk da cewa shekarunsa sun wuce matakin tsofaffin shugabannin Najeriya suka hau mulki, Ahanotu ya ce ya cancanci zama shugaban Najeriya idan aka duba ɗabi’a, ilimi, kundin tsarin mulki, zuciya da hankalinsa.

Source: Twitter
Dangane da batun murabus daga kujerar shugaban matasan LP saboda ya fito takara, Ahanotu ya ce babu wani tanadi a kundin tsarin mulkin jam’iyyarsu da ke tilasta hakan.
“Kundin tsarin mulkin jam’iyyata bai tilasta mani ajiye matsayi na don kawai na tsaya takara ba. Duk da haka, zan yi murabus idan lokaci ya yi ko kuma idan mun je wani mataki," inji shi.
Tsagin LP ya sallama Peter Obi ga ADC
A wani labarin, kun ji cewa tsagin Julius Abure a jam'iyyar LP ya umurci Peter Obi da ya fice daga jam’iyyar cikin sa’o’i 48 saboda ya shiga kawancen ƴan adawa.
Tsagin jam'iyyar karkashin Abure ya ce LP ba za ta taɓa shiga kawancen ADC ba kuma tana kallon mambobin kawancen a matsayin masu neman mulki da son kai.
LP ta kuma soki matakin da Obi ya ɗauka na shiga haɗakar adawa a ADC, tana mai cewa haka ba zai kawo sauyi a Najeriya ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
