"Ƴan Arewa ba Su Yi Nadama ba," Minista Ya Faɗi Abin da Ke Faruwa a Gwamnatin Tinubu

"Ƴan Arewa ba Su Yi Nadama ba," Minista Ya Faɗi Abin da Ke Faruwa a Gwamnatin Tinubu

  • Ministan kasafin kudi, Atiku Bagudu ya bayyana cewa Arewa na da wakilci a gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
  • Bagudu, tsohon gwamnan jihar Kebbi ya ce ƴan Arewa ba su yi nadamar zaɓen Shugaba Tinubu ba domin yana mutunta wakilansu
  • Ministan ya kuma musanta zargin nuna wariya da ake wa gwamnatin Tinubu, yana mai cewa da ƴan Arewa ake tafiyar da mulkin Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare, Sanata Atiku Bagudu, ya tabbatar da cewa yankin Arewa na da cikakken wakilci kuma da shi ake tafiyar da harkokin mulkin Najeriya.

Atiku Bagudu ya bayyana cewa babu wani dalilin da zai sa Arewa ta yi nadamar marawa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen da ya gabata.

Ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Atiku Bagudu.
Atiku Bagudu ya ce Arewa ba ta yi nadamar goyon bayan shugaban ƙasa, Bola Tinubu ba Hoto: @Atikuabagudu
Source: Facebook

The Nation ta ruwaito cewa ministan ya faɗi haka ne a wurin taron tattaunawa tsakanin gwamnatin Tinubu da ƴan Arewa da aka shirya a Kaduna.

Kara karanta wannan

"Lokaci ya yi" Gwamnatin Tinubu ta yiwa ƴan bindiga 'tayi' a Arewacin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu ta yi watsi da Arewa?

Bagudu ya yi watsi da zargin da wasu ke yi cewa ana nuna wariya ga Arewa, yana mai jaddada cewa babu wani tsarin nuna bambanci a gwamnatin Tinubu.

Idan baku manta ba, ɗan takarar NNPP a zaɓen shugaban kasar 2023, Rabiu Kwankwaso ya zargi gwamnatin Tinubu da yin watsi da Arewa wajen ayyukan raya ƙasa.

Kwankwaso ya ce a bayanan da suka riske shi, gwamnati mai ci tana karkatar da albarkatun ƙasa mafi tsoka zuwa yankin Kudu, wanda shugaban ƙasa ya fito.

Atiku Bagudu ya yaba da salon mulkin Tinubu

Sai dai Atiku Baugudu, ya ce gwamnatin Tinubu na tafiyar da harkokinta bisa gaskiya da adalci.

"Mu da muka samu damar shiga gwamnatin Shugaba Tinubu muna kula da kuma tsayawa wajen kare muradun Arewa. Babu wani yunkurin ware kowa, kuma babu wani abin nadama.”

Bagudu ya bayyana Shugaba Tinubu a matsayin dan kasa na gari wanda ke ɗaukar matakai da naɗa mukamai bisa cancanta da hangen nesa, ba la’akari da kabila ko yankin da mutum ya fito ba.

Kara karanta wannan

"Ya cika su": Minista ya yi bayani kan alkawuran da Tinubu ya yi wa Arewa

“Duk wani da ke cikin muƙarraban shugaban kasa ana mutunta shi ba tare da la’akari da wurin da ya fito ba. Wannan gwamnati ce ta adalci da haɗin kai,” inji shi.
Shugaba Tinubu tare da Atiku Bagudu.
Atiku Bagudu ya ce Shugaba Tinubu na tafiyar da mulki bisa adalci Hoto: @atikuabagudu
Source: Twitter

Ministan Tinubu ya ja kunnen manyan Arewa

Ya ja kunnen shugabanni da al’ummar Arewa da kada su bar kansu su fada tarkon da aka ɗana domin raba kansu, wanda ke nuni da cewa an bar Arewa a baya.

A ruwayar Vanguard, Atiku Bagudu ya ci gaba da cewa:

“Eh, ba zaka raba mutane da tunani da saƙe-sake irin wannan ba amma a zahirin gaskiya ba haka abin yake ba, ba a bar Arewa a baya ba, da mu ake komai a kowane mataki."

Hadimin Tinubu ya yiwa Kwankwaso raddi

A wani labarin, kun ji cewa mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin jaridu, Abdulaziz Abdulaziz ya ce zargin da Rabiu Kwankwaso ya yi kan gwamnatin Tinubu ba gaskiya ba ne.

Ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa gwamnatin Bola Tinubu na aikin tituna ne a matakin kasa kuma babu wani yanki da take nuna wa wariya.

Abdulaziz ya musanta zargin da Kwankwaso ya yi cewa gwamnatin Tinubu ta yi watsi da aikin titin Abuja-Kaduna-Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262