Siyasa: Rikici Ya Yi Kamari a SDP, An Tura Mutanen El Rufa'i Kurkuku

Siyasa: Rikici Ya Yi Kamari a SDP, An Tura Mutanen El Rufa'i Kurkuku

  • Wata kotu a Keffi ta tsare wasu jiga-jigan SDP masu biyayya ga tsohon gwamnan Kaduna bisa zargin tayar da hankali
  • Magoya bayan bangaren Adamu Modibbo a jam'iyya sun ce an kitsa kama su ne domin bata sunan sabon shugabancinsu
  • Rikicin cikin gida na ci gaba da kamari yayin da bangaren Shehu Gabam ya kori El-Rufai daga jam’iyyar na tsawon shekara 30

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wata kotun majistare da ke Keffi, jihar Nasarawa, ta bayar da umarnin tsare wasu mutum biyar daga cikin magoya bayan tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

Rahotanni sun nuna cewa hakan ta faru ne sakamakon rikicin da ke kara ta’azzara a jam’iyyar SDP.

Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i
Kotu ta rufe mutanen El-Rufa'i saboda rikicin SDP. Hoto: Shehu Musa Gabam|Nasir El-Rufa'i
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa wadanda kotun ta tsare sun hada da manyan jam’iyyar, kuma su ne ke cikin sabon bangaren shugabanci karkashin Adamu Abubakar Modibbo.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban ADC ya fadi yadda APC ta so rusa hadaka da raba mukaman minista

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bincike ya nuna cewa Adamu Modibbo ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban SDP ne tun ranar 22 ga Yuli, 2025.

SDP: Mutanen El-Rufa'i da aka tsare

A zaman kotun ranar Talata, an tsare shugaban SDP na Abuja, Nuradeen Bisala da mataimakinsa, Humphrey Onwukaeze.

Haka zalika an tsare shugaban matasan SDP, Eluwa Ifeanyi Henry, lauyan SDP na kasa, Solsuema Osaro; da sakataren jam’iyyar Dr Ekpenyong Ambo.

An tsare su ne har zuwa ranar Juma’a mai zuwa yayin da za a saurari bukatar neman belinsu a gaban kotun.

Sun fito ne daga sabon bangaren shugabanci da ke da alaka da El-Rufai kuma suka sha alwashin sake gyara jam’iyyar kafin zaben 2027.

Martanin tsagin jam'iyyar SDP

Mai magana da yawun tsagin Modibbo, Jakadiya Judith Shu’aibu, ta ce zargin da aka yi na kutsawa ofishin SDP karya ne, kuma ‘yan sanda sun je bincike ba su ga komai ba.

Trust Radio ya rahoto ta shaida cewa:

Kara karanta wannan

2027: APC ta tsorata da ake shirin kawo sauyi kan zaɓen shugaban ƙasa, gwamnoni

“An kama su ba bisa ka’ida ba, an kuma ki ba su beli,”

Ta kara da cewa wadanda ake zargin yanzu suna tsare a gidan gyaran hali na Keffi kuma za su gurfana da kotu ranar Juma’a mai zuwa.

Ta bayyana cewa bangaren Shehu Gabam na kokarin bata sunan sabon shugabanci ta hanyar yada karya a kafafen sada zumunta domin su samu hujjar cafke su.

Shehu Musa Gabam da Aisha Binani
Shehu Musa Gabam da Aisha Binani. Hoto: SDP National Update
Source: Facebook

Maganar korar El-Rufa'i a SDP

Bangaren El-Rufai ya yi watsi da matakin korar shi, inda tsohon kwamishina a gwamnatinsa, Malam Ibrahim Husseini, ya ce wannan abin dariya ne.

“Kafin Malam ya shiga SDP, wanene ya san da su?”

= Inji shi.

Tsohuwar kwamishina a gwamnatin El-Rufai, Hafsat Muhammad Baba, ta tabbatar da cewa El-Rufai cikakken dan jam’iyyar ne a Unguwar Sarki, Kaduna.

Martanin SDP a Kaduna kan korar El-Rufa'i

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar SDP a jihar Kaduna ta yi martani kan korar da aka ce an yi wa Nasir El-Rufa'i.

Kara karanta wannan

'Yan Zamfara sun huro wuta, suna so Dauda Lawal ya sauka daga kujerar gwamna

Shugaban jam'iyyar ya ce babu wani da ke da hurumi wajen korar tsohon gwamnan daga jam'iyyar.

A cewar shugaban, an riga an sallami wadanda suka ce sun kori El-Rufa'i tsawon shekara 30 saboda cin amanar SDP da suka yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng