Peter Obi Ya Shirya Rabuwa da Atiku, ADC don Ya Koma Jam'iyyar PDP? An Samu Bayanai
- 'Dan takarar LP a zaɓen shugaban kasa na 2023, Peter Obi ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa a soshiyal midiya cewa yana shirin komawa PDP
- Mista Obi ya jaddada cewa yana nan daram a haɗakar ƴan adawa watau ADC domin cimma burinsu na gina sabuwar Najeriya
- Tsohon gwamnan ya buƙaci magoya bayansa su yi fatali da wannan jita-jita, su jajirce kan cika burinsa na kawo sauyi mai amfani a ƙasar nan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Mr. Peter Obi, ya musata jita-jitar da ake yaɗawa cewa yana shirin komawa jam'iyyar PDP.
Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya jaddada cewa yana nan daram tare da haɗakar manyan ƴan adawar Najeriya, waɗanda suka rungumi jam'iyyar ADC.

Source: Twitter
NTA Network ta wallafa rahoton cewa Mista Obi ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Peter Obi ya karyata jita-jitar da ake yaɗawa yana mai cewa ya shiga haɗakar ƴan adawa watau ADC domin gina sabuwar Najeriya, sannan ba shi da wani shiri na komawa PDP.
Peter Obi na tare da haɗakar adawa, ADC
Ya ce wannan kawance yana da burin hada kan dukkan ‘yan Najeriya masu kishin kasa domin gina sabuwar Najeriya da ke da gaskiya, adalci da ci gaba.
Idan baku manta ba, ƴan adawa sun ƙulla haɗaka ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar domin kwace mulki daga APC a 2027.
Peter Obi na ɗaya daga cikin manyan ƙusoshin wannan haɗaka, tare da wasu manyan jagororin adawa kamar tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.
Yadda aka fara jita-jitar Obi zai koma PDP
A kwanakin baya, jam'iyyar PDP ta bayyana cewa za ta jarabawa rarrashin Peter Obi domin ya dawo cikinta kafin zaɓen 2027, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da suka kara rura wutar jita-jitar cewa tsohon gwamnan na Anambra ya fara shirin sauya sheka zuwa PDP.
Sai dai Peter Obi ya fito ya musanta, ya bayyana cewa ba zai koma PDP ko wata jam’iyyar siyasa da ba ta da cikakken daidaito da burinsa na kawo sauyi ba.

Source: Twitter
Peter Obi ya musanta shirin komawa PDP
Obi ya kalubalanci masu yada jita-jita da su bar siyasar rikita tunanin jama'a, yana mai cewa a halin yanzu abin da Najeriya ke bukata shi ne hadin kai da gaskiya, ba rikice-rikicen siyasa ba.
"Wannan ba lokaci ba ne na wasan siyasa ko kirkirar labaran da ba su da tushe. Lokaci ne na haɗin kai, daidaito, aminci da yiwa Najeriya hidima," inji shi.
Ya kuma bukaci mambobin jam’iyyar LP da sauran masu goyon bayansa su kasance masu jajircewa da natsuwa.
Obi ya tuna kyautar N120 da aka yi masa
A wani labarin, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ce an taɓa masa kyautar kadarar Naira miliyan 120 amma ya ƙi karɓa.
Peter Obi ya ce ya ƙi karɓar kyautar gida mai darajar N120m da aka shirya ba shi a bikin zagayowar ranar haihuwarsa ta shekaru 50 lokacin yana matsayin gwamna.
Ya kara da cewa bayan wannan, akwai wata ƙungiya da ta taɓa ba shi kyautar N20m amma ya ƙi karɓa, ya nemi su sanya kudin a ɓangaren ilimi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


