Sabon Shugaban APC Ya Kada Hantar 'Yan Adawa, Ya Sha Alwashi kan Zaben 2027
- Sabon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya fara dauko batun zaben shekarar 2027
- Nentawe Yilwatda ya sha alwashin tabbatar da nasarar Bola Tinubu da sauran 'yan takarar da APC za ta tsaida lokacin
- Shugaban na APC ya nuna cewa gwamnatin Bola Tinubu ta bullo da shirye-shirye masu yawa don tallafawa matasa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sabon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya sha alwashi kan zaben shekarar 2027.
Farfesa Nentawe Yilwatda ya sha alwashin yin aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, 'yan takarar gwamna, na majalisar tarayya da na majalisun jihohi a zaɓen 2027.

Source: Twitter
Yilwatda ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin da yake jawabi ga daruruwan magoya bayan jam’iyyar karkashin kungiyar 'APC League of Professionals', cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan kungiyar dai sun kai masa ziyarar nuna goyon baya ne a sakatariyar jam’iyyar APC ta ƙasa da ke Abuja.
Me Yilwatda Nentawe ya ce kan APC?
Ya yi watsi da ikirarin da jam’iyyar ADC da sauran jam’iyyun adawa ke yi, yana mai cewa nasarorin da aka samu karkashin shirin “Renewed Hope” na gwamnatin Tinubu sun karade ko ina a faɗin ƙasar nan.
"Yaron talaka a Najeriya yanzu yana iya zuwa makaranta har matakin gaba ba tare da karɓar bashi daga ko ina ba. Gwamnati ta tanadi wannan dama."
"Wannan shi ne karo na farko da hakan ya faru a tarihin Najeriya. Gwamnati ta ajiye Naira biliyan 1.5 a bankin noma (BOA) domin tallafa wa matasa masu sha’awar shiga harkar noma."
"Ba a taɓa samun irin wannan dama ba a baya. Akwai kuɗin matasa da ake bayarwa don tallafa musu. Babu wata gwamnati da ta taɓa yin hakan. Kuma zan iya gaya muku cewa wannan dama ga matasa tana a karkashin jagorancin shugabanmu."
"Abin da zan fara nuna muku shi ne godiya bisa goyon bayanku, godiya bisa tsayuwar ku tare da jam’iyyarmu, godiya saboda kun yi amanna da wannan jam’iyya.”
- Farfesa Nentawe Yilwatda

Source: Twitter
Jam'iyyar APC na son ci gaban matasa
Shugaban jam’iyyar na kasa ya jaddada cewa manufar APC ta fi karkata ga matasa.
"Shirin Renewed Hope an yi shi ne don mutane irin ku. Kuma ina fatan yin aiki tare da ku domin tabbatar da cewa zaɓen 2027 zai samar da nasara ga shugaban kasa, ga gwamnoni, ga Sanatoci, ga 'yan majalisar tarayya da ta Jihohi."
- Farfesa Nentawe Yilwatda
Mambobin APC sun yi zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu mambobin jam'iyyar APC a jihar Legas sun gudanar da zanga-zanga a gaban majalisar dokoki.
Mambobin na APC sun gudanar da zanga-zangar ne don neman shugaban jam'iyyar na jihar ya sauka daga kan mukaminsa.
Masu zanga-zangar sun zargin Cornelius Adejobi da yin karfa-karfa kan mutanen da za a ba mukamai a gwamnatocin kananan hukumomin jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

