ADC: Wata Sabuwa Ta Taso a Haɗakar Atiku, Peter Obi da El Rufai tun kafin Zaben 2027

ADC: Wata Sabuwa Ta Taso a Haɗakar Atiku, Peter Obi da El Rufai tun kafin Zaben 2027

  • Ɗaya daga cikin ƙusoshin haɗaka, Salihu Muhamma Lukman ya gargaɗi ADC kan yunƙurin wasu ƴan siyasa na mamaye komai a jam'iyyar
  • Tsohon mataimakin shugaban APC ya ce wasu daga cikin shugabannin haɗaka sun fara ƙoƙarin sanya mutanensu a shugabancin ADC da karfi da yaji
  • Lukman ya ce hakan na nuna nan gaba, sai wanda suke so za a ba tikitin takara a kowane mataki a zaɓen 2027 da ke tafe

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Jigo a haɗakar ƴan adawa, Salihu Lukman, ya gargadi shugabannin jam’iyyar ADC ƙarƙashin Sanata David Mark da su guji salon ƙaƙaba 'yan takara da karfi da yaji a zaɓen 2027.

Lukman, tsohon mataimakin shugaban APC na ƙasa, ya nuna damuwarsa cewa wasu shugabannin ADC na nuna kamar sun riga sun ci zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Bayan tafiyar Atiku, an yi hasashen matsayi da PDP za ta ƙare a sakamakon zaɓen 2027

Tsohon mataimakin shugaban APC, Salihu Lukman.
Salihu Lukman ya yi zargin cewa jagororin adawa na neman mamaye jam'iyyar ADC Hoto: Salihu Lukman
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a baya, haɗakar ƴan adawar Najeriya ta amince da amfani da jam’iyyar ADC a matsayin dandalin kalubalantar APC a zaɓen 2027.

Jagororin adawa da ke cikin tafiyar sun haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar; tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai; tsohon gwamnan Jihar Rivers Rotimi Amaechi da sauransu.

Sun amince da nada Sanata David Mark a matsayin shugaban rikon kwarya na ADC, sai kuma tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, da ya zama sakatare na riko.

2027: Lukman ya hango ɓaraka a ADC

Amma a cikin wata sanarwa da ya fitar yau Talata, Lukman ya ce lokacin da aka raba mukaman ADC ga kowane yanki, shugabannin haɗaka sun ɗora kansu a matsayin jagororin yankunansu.

Lukman, wanda tsohon Darakta Janar na kungiyar gwamnonin APC ne, ya ce:

“Gaskiyar magana ita ce, mummunan hali na yawancin jagororin ƴan adawa ya fara bayyana. Da dama daga cikinsu na ƙoƙarin sa son zuciya a tsarin sauya fasalin shugabancin ADC, kai kace an riga an ci zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya fara gano gaskiya, ya aika sako ga gwamnonin APC

Tsohon jigon APC ya ce wannan karfa-karfa da ƙaƙaba magoya baya da shugabannin ADC ke yi ya sauka daga tubalin gaskiya da adalci.

Jigo ya bai wa shugabannin ADC mafita

Ya ƙara da cewa:

“Dole ne mu ja kunnen shugabanninmu, ‘yan Najeriya ba za su yarda a yaudare su ba, ta hanyar kawo sabuwar jam'iyya da za ta ceto su amma ta zama irin tsofaffin da ake da su.
"Idan al'amura suka tafi a haka, jagororin haɗaka sune za su zama iyayen gida, ta yadda sai wanda suke so za a naɗa shugabanci a kowane mataki a ADC.
"Hakan zai ba su damar ƙaƙaba duk ɗan takarar da suke so a zaɓen 2027, don haka aikin farko da ke gaban David Mark shi ne shawo kan waɗannan matsaloli, ka da ya bari ADC ta zama ƴar amshin shatar wasu."
Baraka ta kunno kai a ADC.
Lukman ya gargaɗi shugabannin ADC su gaggauta hawo kan matsalar ubangida Hoto: @Atiku
Source: Twitter

Gwamnoni 2 na shirin komawa ADC

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta yi ikirarin cewa nan ba da jimawa ba, wasu gwamnoni biyu za su shiga cikin haɗaka.

Kara karanta wannan

2027: Shugaba Tinubu ya hada 'yan hadaka wuri guda, ya yi musu saukale

Mataimakin shugaban ADC na ƙasa mai kula da Kudu maso Kudu, Chilos Godsent ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

A cewarsa, tuni tattaunawa da neman shawarwari suka yi nisa kuma nan ba da jimawa ba waɗannan gwamnoni za su fito su sanar da jama'a

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262