Tsohon Mutumin Buhari Yana Tare da Kwankwaso da ya Soki Tinubu kan Arewa

Tsohon Mutumin Buhari Yana Tare da Kwankwaso da ya Soki Tinubu kan Arewa

  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal ya yi magana kan watsi da Arewa a gwamnatin Bola Tinubu
  • Babachir ya zargi gwamnatin Tinubu da nuna wariya ga Arewa, yana goyon bayan Rabiu Kwankwaso kan batun rashin ayyukan gwamnati
  • Ya ce babu wani aikin gine-gine ko na gwamnatin tarayya da ke gudana a Arewa a zahiri da gani

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya bayyana goyon bayansa ga tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Lawal ya ce gwamnatin Bola Tinubu na nuna wariya ga yankin Arewa musamman a fannin ayyukan ci gaban ababen more rayuwa.

Babachir ya goyi bayan Kwanwkaso kan sukar Tinubu
Babachir ya fadi gaskiya kan sukar da Kwanwkaso ya yi ga Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Babachir ya soki Tinubu game da Arewa

Babachir ya bayyana haka ne yayin wani shiri na "Sunday Politics" a Trust TV, inda ya caccaki gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Noma: Hadimin Buhari ya goyi bayan Tinubu, ya fadi kuskuren da aka samu a zamaninsu

Ya ce babu wani aikin gwamnati na zahiri da ake gudanarwa a Arewa da za a iya gani da ido.

Ya ce:

"Duk wanda ke da alaka da Arewa ya sani babu wani aiki da ake yi a can da za a iya gani da ido."

Babachir ya kara da cewa ko a mafarki ne kawai ake cewa akwai ayyuka, domin babu wani aiki a hakikanin gaskiya.

Babachir ya gaskata maganar Kwankwaso kan Tinubu

Ya bayyana cewa Kwankwaso, wanda injiniya ne, kamar shi, ya san abin da yake fada dangane da wannan batu.

Babachir ya ce kowane ɗan Najeriya mai gaskiya da hankali zai fahimci cewa Arewa na fuskantar wariya.

Ya ce yawancin ‘yan Arewa na ganin wannan gwamnati ba wai kawai tana watsi da yankin ba, har ma tana lalata abin da ta gada.

Babachir ya kuma kalubalanci jam’iyyar APC a Arewa kafin babban zaɓen 2027, yana cewar babu wanda zai tsaya takara da ita.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya hango kuskuren da Kwankwaso ya yi a kalamansa kan Arewa

Ya kara da cewa:

"Wane ɗan Arewa ne zai fito neman takara ƙarƙashin APC a zaɓen 2027, sai dai idan ba ya shirin yin nasara."
Kwankwaso ya zargi Tinubu da watsi da Arewa
Babachir ya marawa Kwankwaso baya kan sukar Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Babachir ya zargi Tinubu da lalata Arewa

Babachir ya ce idan har ‘yan Arewa ba su fice daga jam’iyyar APC zuwa ADC ba, to za su sha kaye a zaɓe.

Ya kira APC jam’iyya mai rushe-rushe da manufarta ita ce lalata yankin Arewa da duk wani ci gaba da aka samu.

Babachir ya zargi gwamnatin Tinubu da cewa tana da wata manufa ta rushe Arewa baki ɗaya da abubuwan ci gabanta.

Zargin nasa ya yi daidai da na Kwankwaso, wanda ya zargi gwamnatin tarayya da fifita wani yanki fiye da sauran.

Ministan Tinubu ya dura kan Kwanwkaso

Kun ji cewa Ministan Ayyuka, David Umahi ya yi magana kan zargin Rabi'u Kwankwaso cewa Bola Tinubu yana fifita Kudu fiye da Arewa.

Umahi ya ce Kwankwaso na kokarin yaudarar ’yan Arewa ne da burin gaje irin farin jinin da Muhammadu Buhari ya samu a yankin a siyasance.

Umahi ya bayyana jerin manyan ayyuka a yankunan biyu, yana cewa Arewa na da kashi 52% na ayyukan da ake yi yanzu haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.