"Dole Ka Sauka," Mambobin APC Sun Ɗauki Zafi, Sun Buƙaci a Tsige Shugaban Jam'iyya

"Dole Ka Sauka," Mambobin APC Sun Ɗauki Zafi, Sun Buƙaci a Tsige Shugaban Jam'iyya

  • Mambobin APC sun gudanar da zanga-zangar adawa da shugaban jam'iyyar APC reshen jihar Legas, Cornelius Ojelabi
  • Masu zanga-zangar sun mamaye zauren Majalisar Dokokin Jihar Legas yau Litinin, inda suka buƙaci a sauke Ojelabi daga muƙaminsa
  • Sun zarge shi da yunƙurin kakaba mutanen da za a naɗa a matsayin ƴan Majalisar Zartarwa na kananan hukumomin jihar Legas

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Legas - Mambobin APC sun gudanar da zanga-zanga a ranar Litinin a gaban Majalisar Dokokin Jihar Legas, suna neman a sauke shugaban jam’iyya na jiha, Cornelius Ojelabi.

Masu zanga-zangar sun buƙaci a tsige Ojelabi ne bisa zarginsa da yunkurin ƙarfa-ƙarfa da ƙaƙaba mutanen da za a naɗa a gwamnatocin ƙananan hukumomin Legas.

Yan APC sun mamaye Majalisar Dokokin Legas.
Mambobin APC sun nemi a sauke shugaban jam'iyya na jihar Legas Hoto: @Rilwan_Ola
Source: Twitter

Wakilan ƙananan hukumomi 20 da yankunan ci gaban ƙananan hukumomi (LCDA) 37 da ke faɗin jihar Legas sun halarci wannan zanga-zanga, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun hallaka jagororin 'yan ta'adda 3 da suka addabi jama'a

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mambobin APC sun yi zanga-zanga a Legas

Masu zanga-zangar sun fito da dimbin yawa, suna rera taken nuna adawa da shugaban APC na Legas, kuma suna ɗauke da alluna masu rubuce-rubuce iri-iri.

Wasu daga cikin rubuce-rubucen allunan sun ce: “Dole a sauke Ojelabi,” “Faleke ma ci amana ne,” da sauransu.

Rahoton The Nation ya nuna cewa zanga-zangar ta jawo hankalin jama’a sosai kuma hakan ya sa an ƙara tsaurara tsaro a harabar majalisar dokokin Legas.

Mataimakin Gwamna, Dakta Obafemi Hamzat, wanda ya isa wurin da tawagarsa, bai samu damar magana da ƴan jam'iyyar APC masu zanga-zanga ba.

Masu zanga-zangar sun miƙa buƙatarsu

Jagoran masu zanga-zangar, Segun Faleye, ya miƙa wata takarda a madadin tawagarsa, inda ya bayyana cewa ba za su iya jurewa halayen da suke ganin sun wuce gona da iri na shugaban APC ba.

Faleye ya zargi Ojelabi da gurɓata zaɓen kananan hukumomi da aka kammala, inda ya ce ya tara mutane ƴan son zuciya sun gudanar da abin da ya kira “zaben fitar da gwani mafi muni a tarihin jihar Legas."

Kara karanta wannan

Yobe: Wata mata, Hadiza Mamuda ta kashe mijinta kan abin da yake kawo mata kullum

"Mun gaji da shugabancinsa na son kai da makircin da tawagarsa ke shiryawa, waɗanda suka saɓa wa manufofin cigaba da Shugaba Bola Tinubu ke jagoranta," inji shi.
Yan APC sun dauki zafi a Legas.
An taso shugaban APC na jihar Legas a gaba Hoto: @Rilwan_Ola
Source: Twitter

Jam'iyyar APC ta mayar da martani

Da yake mayar da martani, mai magana da yawun jam’iyyar APC a Legas, Seye Oladejo, ya ce:

“Zanga-zangar lumana halak ne a dimokuraɗiyya, kuma mun yaba wa waɗanda suka gudanar da ita cikin lumana da natsuwa.”

Ya tabbatar wa masu zanga-zangar cewa za a bi ƙa'ida wajen naɗa mambobin majalisar zartarwa na kananan hukumomin jihar Legas.

APC ta yi gyara a kwamitin gudanarwa (NWC)

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta ƙasa ta ƙara yin garambawul a kwamitin gudanarwa watau NWC.

APC ta naɗa Murtala Aliyu Kankia daga Katsina a matsayin sabon mai ba da shawara kan harkokin shari’a da Abdulkarim Kana a matsayin mataimakin sakatare.

Hakan ya zo ne bayan sauye-sauyen tsarin raba mukamai a tsakanin shiyyoyin kasar nan da aka amince da su a taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC).

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262