ADC Ta Samu Ƙaruwa, Babban Jigon PDP a Kaduna Ya Sauya Sheƙa
- John Ayuba, tsohon ɗan takarar mataimakin gwamna na PDP a jihar Kaduna, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC
- Ya bayyana cewa matsalolin da suka sako PDP a gaba tun a shekarar 2023 na ci gaba da bibiyar jam'iyyar har yanzu
- Ayuba ya ce bayan dogon nazari da shawarwari, ya yanke shawarar barin PDP domin ci gaba da siyasa a wata jam’iyya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Tsohon ɗan takarar mataimakin gwamnan jihar Kaduna karkashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, John Ayuba, ya fice daga jam’iyyar.
Ya sanar da cewa ya yanke shawarar barin PDP ne saboda ɗimbin matsaloli, tare da cewa ya koma jam'iyyar hadakar ƴan adawa ta ADC.

Asali: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa wannan na ƙunshe a cikin wasiƙar da ya aika ga Shugaban PDP na mazabar Ungwan Gaiya da ke karamar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin jigon PDP na koma wa ADC
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa Ayuba ya ce rashin tsari da rashin shugabanci nagari a matakin ƙasa ne suka tilasta masa barin jam’iyyar.
John Ayuba ya ce:
“Zuciyata cike da damuwa nake rubuta wannan takarda domin bayyana matakin da na ɗauka na ficewa daga tsohuwar babbar jam’iyyarmu.”
Tsohon ɗan takarar ya zargi wasu jiga-jigai na kasa da lalata makomar jam’iyyar ta hanyar shiga ayyukan da suka ci karo da manufar PDP.
Ya ce:
“Na shafe fiye da shekaru uku ina kallon yadda ake lalata makomar jam’iyyarmu a matakin ƙasa ta hannun wasu da bana ganin suna da kyakkyawan fata a kanta.”
Ya kara da zargin cewa wasu daga cikin ƴan jam'iyyar sun ci amanar PDP, musamman a zaɓen 2023 da ya gabata.
Tsohon jigon PDP ya godewa jam'iyyar adawa
Ayuba ya ce har yanzu PDP ba ta ɗauki matakin kirki kan batutuwan da suka bulla tun bayan zaɓen 2023 ba, lamarin da ya jefa ƴaƴanta a cikin halin ni ƴa su.
'Dan siyasar ya bayyana cewa matakin sauya shekar tasa ta biyo bayan shawarwari da abokan siyasa da magoya bayansa, yana mai cewa ci gaba da zama a PDP ba shi da amfani a yanzu.

Asali: Twitter
Yayin da yake nuna godiyarsa ga PDP kan damar da ta bashi da kuma amincewar da aka yi da shi a matsayin ɗan takarar mataimakin gwamna a 2023, Ayuba ya ce lokaci ya yi da zai nemi mafita.
Sauya shekar tasa na daga cikin jerin ficewar jiga-jigai daga PDP a jihar Kaduna da ma kasa baki daya, biyo bayan rikicin cikin gida da ya dabaibaye ta.
ADC ta yi magana kan zaɓen Najeriya
A baya, mun wallafa cewa Mukaddashin sakataren ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa jam’iyyarsu ba ta da wani ɗan takarar shugaban ƙasa da take goyon baya a 2027.

Kara karanta wannan
Bayan tafiyar Atiku, PDP ta fara hangen wanda za ta tsayar takarar shugaban ƙasa a 2027
Abdullahi ya bayyana haka ne a ranar Asabar, yayin taro da ƙungiyar Northern Political Consultative Group (NPCG) ta shirya a babban birnin Abuja.
Ya bayyana cewa jam’iyyar ta fi maida hankali kan ƙarfafa shirinta na samar da ingantaccen tsari fiye da fara tattaunawa kan ɗan takarar shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng