Fadar Shugaban Kasa Ta Sake Magana kan 'Haduwar' Tinubu da Kwankwaso

Fadar Shugaban Kasa Ta Sake Magana kan 'Haduwar' Tinubu da Kwankwaso

  • Hadimin shugaban kasa ya ce babu laifi idan Bola Tinubu ya hada hanya da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a siyasa
  • Abdulaziz Abdulaziz ya ce Tinubu da Kwankwaso sun dade suna mu'amala tun lokacin da suka fara siyasa a shekarun baya
  • Ya ce shugaba Tinubu mutum ne mai karɓar kowa, wanda hakan ya jawo sauya sheƙar wasu gwamnoni biyu zuwa APC

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Hadimin shugaban kasa, Abdulaziz Abdulaziz, ya ce ba laifi ba ne shugaba Bola Tinubu ya hada hanya da Rabiu Musa Kwankwaso.

Abdulaziz ya ce siyasa ce ke kawo haɗin kai, rabuwar kai da sake haɗuwa, don haka abokantaka tsakanin Kwankwaso da shugaban kasa ba zai zama abin zargi ba.

Fadar shugaban kasa ta ce alakar Tinubu da Kwankwaso ta dade
Fadar shugaban kasa ta ce alakar Tinubu da Kwankwaso ta dade. Hoto: Bayo Onanuga|Saifullahi Hassan
Source: Twitter

Hadimin ya bayyana hakan ne a hirar da aka yi da shi a tashar Channels TV a wani shiri na musamman a yau Litinin, inda ya ce tuntubar juna tsakanin ‘yan siyasa ba abin mamaki ba ne.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya hango kuskuren da Kwankwaso ya yi a kalamansa kan Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tarihin dangantakar Kwankwaso da Tinubu

A cewarsa, Tinubu da Kwankwaso sun dade suna hulɗa da juna tun kafin su zama gwamnoni a 1999, kuma sun fara siyasa tare tun a 1993 lokacin da aka zabe su a majalisar dokoki ta ƙasa.

Daily Post ta rahoto ya ce:

“Kwankwaso da shugaban kasa sun daɗe da sanin juna. Sun yi aiki a majalisa a shekarar 1993 sannan duka suka zama gwamnoni a 1999.
"Don haka ba abin mamaki ba ne idan sun sake haɗuwa,”

Maganar tattaunawar Tinubu da 'yan adawa

Abdulaziz ya ce tattaunawa tsakanin shugaban kasa da ‘yan adawa kamar Kwankwaso ba ta sabawa tsarin dimokuraɗiyya ba.

Ya ce:

“Siyasa ce ke kawo canji da gyara. Ba laifi ba ne idan shugaban kasa ya tattauna da Kwankwaso ko wani ɗan adawa. Abin da ya kamata shi ne a fahimta cewa tattaunawa siyasa ce.”

Gwamnonin da suka sauya sheƙa zuwa APC

Kara karanta wannan

Sukar gwamnati: Jam'iyyar NNPP ta ba Tinubu shawara kan Kwankwaso

Mista Abdulaziz ya bayyana cewa gwamnoni biyu daga jam’iyyar PDP sun koma APC ne saboda irin kyakkyawar alaƙar da suke da ita da shugaban kasa Tinubu, ba saboda tilas ba.

Gwamna Umo Eno na Akwa Ibom da Gwamna Sheriff Oborevwori na Delta ne suka bar PDP suka koma APC a cikin shekarar 2025.

Kwankwaso tare da Tinubu a shekarar 2023
Kwankwaso tare da Tinubu a shekarar 2023. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

'Tinubu mutum ne mai son kowa' - Abdulaziz

Abdulaziz ya ce Tinubu shugaban kasa ne mai sauƙin kai, wanda ke da kyakkyawar alaƙa da mutane daga kowane sashe.

A cewarsa:

“Tun da ya hau mulki, yana da kyakkyawar alaƙa da abokansa, wanda hakan ke taimaka masa wajen fahimtar matsalolin ƙasa da kuma jawo mutane daga kowane bangare.”

Siyasar Kwankwaso da 'yan siyasar Arewa

A yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan halin da Najeriya ke ciki karkashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, wasu fitattun ‘yan siyasa, ciki har da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na kokarin fito da sabbin tsare-tsare da hangen nesa da za su gina kasa ta hanyar samar da madogarar da ta fi ta yanzu.

Kwankwaso, wanda ya kafa tafiyar NNPP kuma ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023, na ci gaba da jan hankalin jama’a da sabbin matasa da ke sha’awar sauyi mai ma’ana.

Kara karanta wannan

Gwamnonin 1999 sun nemi Tinubu ya ajiye raba tallafi, ya samar da ayyuka ga matasa

Wani babban burinsu shi ne nuna cewa akwai hanyoyi daban da za a tafiyar da mulki fiye da tsarin da gwamnatin Tinubu ke bi, musamman kan tattalin arziki, ilimi da aikin yi.

Duk da cewa ana jin dadin ganinsa yana cudanya da shugaban kasa, akwai alamun cewa yana shirin sake gina wata kafa mai karfi da za ta iya kalubalantar APC a nan gaba.

Sauran ‘yan siyasa da suka taba mulki ma na kokarin hada kai don samar da sabuwar hanya da za ta maida martabar kasa, tare da karfafa bangarori da dama da ke jin ana tauye su. Wannan na nuni da cewa fafatawar siyasa mai zafi na tafe kafin 2027.

An neni Kwankwaso ya ba Tinubu hakuri

A wani rahoton, kun ji cewa ministan ayyuka na tarayya ya nuna rashin jin dadi kan wasu kalaman da Rabiu Kwankwaso ya yi.

Sanata David Umahi ya bayyana cewa zargin da Kwankwaso ya yi na cewa Bola Tinubu ya yi watsi da Arewa ba gaskiya ba ne.

A kan haka, ministan ayyuka ya bukaci jagoran NNPP ya ba shugaba Bola Tinubu hakuri tare da janye kalaman da ya yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng