SDP Ta Jikawa Nasir El Rufa'i Aiki, Ta Jefa Shi Matsalar Siyasa Ta Shekara 30

SDP Ta Jikawa Nasir El Rufa'i Aiki, Ta Jefa Shi Matsalar Siyasa Ta Shekara 30

  • Kwamitin gudanarwar SDP na ƙasa ya dakatar da Malam Nasir El-Rufai daga jam’iyyar har na tsawon shekara 30
  • Jam’iyyar ta zargi tsohon gwamnan da cewa yana yaudarar jama’a da cewa ya shiga SDP ba tare da yin rajista ba
  • Rahoto ya nuna cewa SDP ta ce El-Rufa'i ya haɗa kai da jam’iyyar ADC kuma yana ƙoƙarin rikita SDP ta bayan fage

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jam’iyyar SDP ta sanar da dakatar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai har na tsawon shekara 30.

Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Ƙasa (NWC) ne ya yanke wannan hukunci bayan gudanar da bincike kan ikirarin El-Rufai da kuma alakar da ake zarginsa da ita da jam’iyyar ADC.

Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i. Hoto: Kaduna State Government
Asali: Twitter

The Nation ta wallafa cewa jam’iyyar ta bayyana cewa El-Rufai ba ya da izinin shiga ko mu’amala da SDP a kowanne mataki har tsawon shekara 30 masu zuwa.

Kara karanta wannan

SDP ta fice daga haɗakarsu Atiku, za ta fito da ɗan takarar shugaban ƙasa a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

SDP ta ce El-Rufa'i ba shi da rajista

A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Araba Rufus Aiyenigba, ya fitar a Abuja, ya bayyana cewa El-Rufai bai taɓa yin rajista da SDP a matakin mazabarsa ba.

Sanarwar ta ce duk da hakan, El-Rufai ya yi iƙirarin a shafukan sada zumunta cewa ya shiga SDP, har ya nuna wasu takardu da hotunansa tare da wasu shugabannin jam’iyyar da aka dakatar.

SDP ta ce irin waɗannan ayyuka sun nuna rashin da’a, yaudarar jama’a da ƙoƙarin rikita jam’iyyar da manufofinta ta hanyar yaudara da dabaru na siyasa marasa gaskiya.

An ce El-Rufa'i zai shigar da SDP a rikici

Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa El-Rufai yana ƙoƙarin jawo SDP cikin wata haɗaka da ba a amince da ita ba, wanda ya haɗa da jam’iyyar ADC.

A cewarta:

“Bayan tabbatar da cewa El-Rufai ya bayyana kansa a fili a matsayin ɗan ADC, kuma yana ci gaba da aikata abubuwan da suka saba da dokokin SDP, babu wani zaɓi da ya rage face a kore shi gaba ɗaya.”

Kara karanta wannan

Ana maganar haɗaka, zaman El Rufai na tangal tangal a SDP bayan matsayar jam'iyyar

Jam’iyyar ta ƙara da cewa daga yau El-Rufai ba zai sake da’awar zama ɗan jam’iyyar ba, ko amfani da sunanta, tutarta, ko alamar jam’iyyar a kowane mataki har tsawon shekaru 30.

SDP ta kori El-Rufa'i har na tsawon shekara 30
SDP ta kori El-Rufa'i har na tsawon shekara 30. Hoto: Nasir El-Rufa'i
Asali: Twitter

Dakatar da El-Rufa'i: SDP ta sanar da INEC

SDP ta bukaci hukumar INEC da sauran hukumomi da su lura da wannan matsayi, tare da gargadin cewa El-Rufai ba shi da wani hurumi da zai wakilci jam’iyyar ko magana da sunanta.

Jam’iyyar ta sake jaddada cewa tana kan turbar gaskiya da bin doka da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya.

Ortom ya caccaki Atiku da El-Rufa'i

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya caccaki Atiku Abubakar, Nasir El-Rufa'i da sauran masu hadaka.

Ortom ya ce batun hadaka da suka dauko a ADC domin kifar da Bola Tinubu a 2027 ba za ta cimma nasara ba.

Tsohon gwamnan ya kuma bayyana dalilan da suka sanya shi juya wa PDP baya a zaben 2023 da Bola Tinubu ya lashe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng