Sukar Gwamnati: Jam'iyyar NNPP Ta Ba Tinubu Shawara kan Rabiu Kwankwaso
- Jam'iyyar NNPP ta koma mai ba da shawara ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan Rabiu Musa Kwankwaso
- NNPP ta bukaci Shugaba Tinubu da ya daina tankawa tsohon dan takarar shugaban kasan a zaben shekarar 2023
- Jam'iyyar ta yi nuni da cewa Kwankwaso na sukar Tinubu domin a tanka masa ta yadda za a rika yin magana a kansa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Jam’iyyar NNPP ta nuna rashin jin daɗinta kan yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke tankawa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Jam’iyyar NNPP ta kuma bayyana ikirarin da Sanata Kwankwaso ya yi cewa gwamnatin Shugaba Tinubu na nuna wariya ga yankin Arewa a matsayin karya ce kuma magana mai tayar da hankali.

Asali: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na kasa, Olaposi Oginni, ya fitar a ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPP ta bayyana cewa zarge-zargen Kwankwaso ba su da tushe ko makama, kuma an tsara su ne don tayar da hargitsi a kasa.
NNPP ta ragargaji Kwankwaso
Olaposi Oginni ya bayyana Kwankwaso a matsayin ɗan siyasa wanda ta kare masa, da ke amfani da dabarun yaudara domin bata aikin alherin da shugaban ƙasa ke yi, musamman a yankin Arewa.
Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin NNPP a zaɓen 2023, ya yi zargin cewa gwamnatin Tinubu na nuna banbanci wajen rabon ayyukan tituna a Najeriya, inda yake watsi da yankin Arewa.
"Kwankwaso ɗan siyasa ne da ta ƙare masa, yana rayuwa ne cikin tunanin nasarorin da suka wuce."
"An kore shi daga NNPP bisa wasu laifuka da ya aikata, kuma yanzu haka jam’iyyar NNPP ta miƙa shi ga hukumar EFCC domin a bincike shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu."
- Olaposi Oginni
Olaposi Oginni ya bayyana cewa kuri'un Kano da ake ta magana a kansu a yanzu ba sa tare da Kwankwaso, domin yawancin fitattun ‘yan siyasar Kano da suka taimaka wa NNPP samun nasara a zaɓen 2023 sun rabu da shi.

Asali: Twitter
An bukaci Tinubu ya daina kula KwankwasoAn bukaci Tinubu ya daina kula Kwankwaso
"Jam’iyyar NNPP na sanar da Shugaba Bola Tinubu gaskiya cewa Sanata Kwankwaso ta ƙare masa a siyasa. Yana neman jan hankalin jama’a ne ta hanyar ɓata sunan shugaban kasa da ayyukansa, musamman a Arewacin Najeriya."
- Olaposi Oginni
Daga ƙarshe, jam’iyyar NNPP ta gargadi Shugaba Tinubu da kada ya bar Kwankwaso ya yi amfani da ofishin shugaban ƙasa da gwamnatin tarayya a matsayin wata hanya ta tallata kansa a matsayin sabon “Mai Ceto na Arewa” bayan rasuwar Buhari.
Afenifere ta soki Kwankwaso kan taba Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta yi kalaman suka kan Rabiu Musa Kwankwaso.
Kungiyar Afenifere ta caccaki Kwankwaso ne bayan ya zargi gwamnatin mai girma Bola Tinubu da maida yankin Arewa saniyar ware.
Ta nuna cewa kalaman na Kwankwaso ba su dace ba kuma suna iya haddasa rikici a kasa.
Asali: Legit.ng