Jonathan ko Peter Obi: Jigon PDP Ya Gano Dan Takarar da Ya Fi Dacewa da Arewa a 2027

Jonathan ko Peter Obi: Jigon PDP Ya Gano Dan Takarar da Ya Fi Dacewa da Arewa a 2027

  • Jigo a jam'iyyar PDP ya tabo batun dan takarar da ya fi dacewa yankin Arewa ya marawa baya a zaben shekarar 2027
  • Umar Sani ya bayya cewa Goodluck Jonathan ya fi kamata a marawa baya fiye da Peter Obi na jam'iyyar LP
  • Ya bayyana cewa Jonathan ya fi dacewa ne saboda doka ta tilasta masa yin shekara hudu ne kacal a kan mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jigo a jam'iyyar PDP, Umar Sani, ya yi magana kan dan takarar da ya fi dacewa da yankin Arewa tsakanin Peter Obi da Goodluck Jonathan.

Umar Sani ya bayyana cewa zai fi dacewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP fiye da Peter Obi, ɗan takarar jam’iyyar LP a zaɓen 2023.

Wasu na son Goodluck Jonathan ya fito takara
Jigon PDP na son Jonathan ya samu tikitin takara a 2027 Hoto: @GEJonathan
Source: Twitter

Umar Sani, ya bayyana hakan ne a cikin shirin Daily Politics na tashar Trust tv a ranar Asabar, 26 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

2027: ADC ta raba gardama kan dan takarar da take goyon baya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Umar Sani, ya bayyana hakan ne a cikin shirin Daily Politics na tashar Trust TV a ranar Asabar, 26 ga watan Yulin 2025.Umar Sani, ya bayyana hakan ne a cikin shirin Daily Politics na tashar Trust TV a ranar Asabar, 26 ga watan Yulin 2025.

An tabo batun takarar Jonathan a 2027

Ya mayar da martani ne kan jita-jitar cewa PDP na ƙoƙarin jawo Peter Obi zuwa jam’iyyar, da kuma yiwuwar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sake tsayawa takara a 2027.

A cewarsa, ko da jita-jitar gaskiya ce ko ƙarya ce, Arewacin Najeriya zai fi son Goodluck Jonathan fiye da Peter Obi.

Yayin da yake bayani, Umar Sani, wanda ya kasance mai taimaka wa tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo a harkokin yaɗa labarai, ya ce dawowar Jonathan mulki na tsawon shekaru huɗu zai cika wa yankin Kudu adadin shekaru takwas

"Zan fi son Shugaba Jonathan ya samu tikitin, ba don ina ƙin Peter Obi ba, amma saboda hakan zai tabbatar da cewa yankin Kudu ya shekaru huɗu."

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: An ji dalilan da suka jawo naɗa Ministan Tinubu a matsayin shugaban APC

- Umar Sani

Meyasa Jonathan ya fi Peter Obi dacewa

Ya bayyana cewa, a ƙarƙashin doka, Jonathan ba zai iya zarce shekaru huɗu a mulki ba, yayin da alkawarin Peter Obi na yin mulki na tsawon shekaru huɗu kawai magana ce kawai ta siyasa.

Ana rade radin Jonathan zai yi takara a 2027
Jonathan ya taba zama shugaban kasan Najeriya Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa, ko da yake Peter Obi mutum ne mai gaskiya da riƙon amana, ya fi dacewa ga jam’iyyar PDP da kuma Arewa su marawa Jonathan baya, wanda doka ta tilasta masa sauka bayan shekaru huɗu, fiye da Obi wanda kawai alkawari ya ɗauka.

Ya ƙara da cewa, ko da yake Peter Obi mutum ne mai gaskiya da riƙon amana, ya fi dacewa ga jam’iyyar PDP da kuma Arewa su marawa Jonathan baya, wanda doka ta tilasta masa sauka bayan shekaru huɗu, fiye da Obi wanda kawai alkawari ya ɗauka.

"Idan za a zaba tsakanin wanda ya yi alkawari da wanda doka ta tilasta masa sauka bayan shekaru huɗu, wanne za ka fi zaɓa? Wannan ɗin doka ce ta tilasta masa, ba sai ya yi alkawari ba. Bayan shekaru huɗu sai ya tafi."

Kara karanta wannan

Ganduje ya sauka, Yilwatda ya hau: Jerin shugabannin APC 9 daga 2013 zuwa 2025

"Amma wancan ya yi alkawari ne kawai. Alkawari ana iya cika kuma an iya ƙaryawa. Amma a nan, ka tabbata dole ne ya tafi. Saboda haka, a wurin Arewa, ina ganin Goodluck Jonathan shi ne mafi dacewa."

- Umar Sani

Ana fargabar Peter Obi na iya barin hadaka

A wani labarin kuma, kun ji cewa alamu sun nuna cewa baraka na shirin kunno kai a jam'iyyar ADC ta 'yan hadaka.

Peter Obi da Nasis El-Rufai na adawa da burin Atiku Abubakar na tsayawa takara a zaben shugaban kasa na 2027.

Rashin samun matsaya mai kyau kan dan takarar jam'iyyar a zaben 2027 na oya kawo rarrabuwar kawuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng