Ministan Tinubu Ya Lashe Amansa, Ya Faɗi Dalilin Janye Neman Takarar Gwamna

Ministan Tinubu Ya Lashe Amansa, Ya Faɗi Dalilin Janye Neman Takarar Gwamna

  • Tsohon gwamnan Osun, Gboyega Oyetola, ya ce ba zai tsaya takarar gwamna a 2026 ba domin ba wa sabbin jiga-jigai dama
  • Ya ce akwai masu cancanta da kwarewa da za su iya jagorantar APC zuwa nasara a zaben 2026, ya kuma gargadi rikici cikin jam’iyya
  • Oyetola ya ce zai ci gaba da jagorancin APC amma ba a matsayin dan takara ba, ya soki hadin gwiwar da ke adawa da Bola Tinubu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Shakatawa ya yi magana kan takarar gwamna a jihar Osun.

Adegboyega Oyetola wanda kuma shi ne tsohon gwamnan jihar, ya bayyana dalilin da yasa ba zai tsaya takara ba.

Minista ya bayyana dalilin kin shiga takarar gwamna
Ministan Tinubu ya fasa neman takarar gwamna a Osun. Hoto: Gboyega Oyetola.
Source: Twitter

Ministan Tinubu ya janye daga neman takara

Oyetola wanda ya mulki jihar daga 2018 zuwa 2022, ya bayyana haka ne a wani taron jam’iyyar APC da aka yi a Osogbo ranar Juma’a, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

'Yadda matata ta hana ni sukar Buhari bayan ya mutu': Tsohon gwamna ya magantu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce janyewarsa daga takarar ba ficewa ba ne daga siyasa, illa dai wata dabara ce domin bai wa sabbin shugabanni damar bayyana.

Ya ce:

“Akwai wasu mutane masu cancanta da tarihi mai kyau da za su iya takara, hakan wata dama ce ta nasara."

Alkawarin da Oyetola ya dauka wa APC

Kodayake ba zai tsaya takara ba, Oyetola ya ce zai ci gaba da taka rawar gani wajen ganin APC ta lashe zaben 2026 a jihar Osun.

Ya bukaci mambobin jam’iyyar su kasance masu hadin kai, yana gargadi game da siyasar gaba da cin mutunci.

“Ina kira ga duk masu sha’awar takara su rungumi zaman lafiya kuma su daina kamfen din batanci da kiyayya."

- Cewar Oyetola

Minista ya yaba wa salon mulkin Tinubu
Ministan Tinubu ya faɗi dalilin janye neman takarar gwamna. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Oyetola ya yabawa salon mulkin Tinubu

Oyetola ya ce dawo da APC kan mulki a Osun ba abu ne da za a yi wasa da shi ba, ya ce za su yi duk mai yuwuwa don ganin hakan, Punch ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ana rade radin gwamnan Yobe zai fita daga APC zuwa ADC, hadiminsa ya yi magana

Ya bayyana kwarin gwiwarsa a jam’iyyar, yana cewa APC na da karfin da za ta iya fitar da Gwamna Ademola Adeleke daga mulki.

A matakin kasa, ya ce hadin gwiwar ‘yan adawa da ake kokarin yi kan Tinubu ba wata barazana bace ga jam’iyyar APC.

“Yana da matukar bayyani cewa wannan kawance na fuskantar rugujewa, ba shi da wata illa a kanmu, musamman ma a Osun."

- Cewar Oyetola

Ya jinjinawa mambobin APC saboda goyon bayan da suka ci gaba da bayarwa tun bayan faduwar jam’iyyar a Osun a 2022.

Ya bukace su da su fita domin rajistar katin zabe da kuma karbarsa, yana cewa hakan ne hanyar tabbatar da nasara a zabe.

Ministan Tinubu zai tsaya takara a Oyo

Mun ba ku labarin cewa ministan wuta a gwamnatin Bola Tibubu zai nemi takarar gwamna domin bunkasa siyasarsa yayin da zabe ke kwaratowa.

Bayo Adelabu, ya fara tuntubar jiga-jigan APC a jihar Oyo domin cimma burinsa na tsayawa takarar gwamna a 2027.

Adelabu ya roki gafara daga mambobin jam’iyya da suka fusata, ya ce ba za a tilasta dan takara ba a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.