2027: Bayan Rasuwar Buhari, Shehu Sani Ya Faɗi Abin da Zai Faru da Tinubu a Zaɓe

2027: Bayan Rasuwar Buhari, Shehu Sani Ya Faɗi Abin da Zai Faru da Tinubu a Zaɓe

  • Tsohon Sanata Shehu Sani ya yi magana kan zaɓen 2027 duk da mutuwar marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
  • Ya ce ba wanda zai gaji goyon bayan Buhari a Arewa saboda mutane sun gane gazawarsa duk da soyayyarsu da sadaukarwarsu
  • Shehu Sani ya bayyana cewa Tinubu zai lashe zabe a 2027 domin babu cikakken dan takara da zai iya kalubalantarsa a Arewa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya Shehu Sani, ya yi fashin baki kan zaben 2027 da ake tunkara.

Sanatan ya kuma tattauna kan rasuwar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, yanayin siyasa a Arewa da hasashen zaben 2027.

Shehu Sani ya magantu kan zaben Tinubu a 2027
Shehu Sani ya ce Tinubu zai lashe zabe duk da rasuwar Buhari. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Shehu Sani.
Source: Facebook

Shehu Sani ya bayyana tasirin Buhari

Shehu Sani ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da Ismaeel Uthman da jaridar Punch ta bibiya a jiya Asabar 26 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa ta ɓullo kan jinyar da Shugaba Buhari ya riƙa zuwa Landan kafin ya rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehu Sani ya ce akwai karancin tarihi duba da irin martani da aka rika yi bayan mutuwar Muhammadur Buhari.

Sanatan ya ce:

“Karancin tarihi ne a Najeriya mu ga irin wannan martani mai cike da tausayawa da fushi bayan mutuwar shugaba ko tsohon shugaba.”

Ya kara da cewa matasan Najeriya suna bayyana fushinsu cikin yanci, kuma shugabanni su sani za a hukunta su bayan mutuwa.

“A lokacin Yar’Adua, mutane sun nuna tausayawa, amma a Buhari, wasu suna yabawa yayin da wasu ke zagi da la’anta."

- Shehu Sani

Waye zai gaji farin jinin Buhari?

Kan wanda zai gaji farin jinin Buhari, ya ce a yau babu wanda zai iya samun farin jinin Buhari saboda talakawa sun sadaukar da rayuwarsu saboda shi.

Ya kara da cewa:

“Tun bayan rasuwar Malam Aminu Kano, babu wanda ya karfafa dangantaka da talakawa irin Buhari.
“Mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu don Buhari sune suka fi fusata da gazawar da suka gani daga mulkinsa.

Kara karanta wannan

'Yadda matata ta hana ni sukar Buhari bayan ya mutu': Tsohon gwamna ya magantu

"A yau, babu wani dan siyasar Arewa da talakawa za su sake kashe kudi ko rayuka kamar Buhari.”
Shehu Sani ya yi hasashen nasarar Tinubu a 2027
Duk da rasuwar Buhari, Shehu Sani ya ce Tinubu zai lashe zabe. Hoto: Shehu Sani.
Source: Twitter

Shehu Sani ya magantu kan nasarar Tinubu a 2027

Game da gazawar Buhari, ya ce ya daukaka musu buri fiye da yadda zai iya cikawa, kuma bai gina tawagar masu gaskiya ba.

Ya ce Buhari mutum ne mai gaskiya, amma shugabanci yana bukatar hangen nesa da tawagar masu irin ra’ayinsa da nagarta.

Har ila yau, ya ce Buhari yana da gaskiya, amma “an kewaye shi da mutanen da ba su da gaskiya kuma ba su tare da ra’ayinsa da akidarsa.

Game da Tinubu a 2027, ya ce:

“Zaben zai dogara da jagorancin ‘yan siyasar yankuna da kuma tasirin ayyukan gwamnati.
“Ina da yakini Tinubu zai yi nasara saboda babu babbar jam’iyyar adawa da ke da karfi a Arewa yanzu.
"Kusan duk kudin da aka samu bayan cire tallafin man fetur na zuwa ayyuka a jihohi, amma mutane na sukar Tinubu kawai.”

Ya ce yan a dawa a Arewa na amfani da kabilanci da yankin don sukar Tinubu, duk da cewa Buhari ya bai wa Arewa manyan mukamai.

Kara karanta wannan

'Ya yi mani albishir zan yi tazarce,' Tinubu ya fadi wanda ya taimaka ya zama shugaban kasa

Tsohon sanatan ya ce a lokacin Buhari, dukkan manyan mukaman tsaro sun kasance a hannun ‘yan Arewa, amma ba su kawo cigaba ba.

Shehu Sani ya ce Tinubu ya nada ‘yan Arewa manyan mukamai, amma wasu na kara yunkurin janyo kiyayya a Arewa.

Shehu Sani ya shawarci yan Arewa kan Tinubu

Kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya buƙaci ƴan Arewa da su marawa Bola Tinubu baya a zaɓen 2027.

Shehu Sani ya nuna cewa kamata ya yi yankin Arewa ya bari yankin Kudu ya kammala shekara takwas a mulki.

Tsohon sanatan ya kuma caccaki tsofaffin shugabannin da suka fito daga Arewa kan yadda suka kasa kawo ci gaba a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.