'Abin da Ya Sa Gwamnonin PDP da APC ba Su Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar ADC ba'

'Abin da Ya Sa Gwamnonin PDP da APC ba Su Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar ADC ba'

  • Jam’iyyar ADC ta yi magana kan gwamnonin Najeriya da take hasashen za su dawo cikinta duba da shirin haɗaka
  • ADC ta ce rashin gwamnoni masu ci a cikinta ba zai hana ta karfi ba, saboda suna fuskantar barazana daga gwamnatin Tinubu
  • Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce mutane sun gaji da halin rayuwa, suna fatan jam’iyyar ADC ce mafita ta gaskiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC da ke samun goyon bayan gamayyar ƙungiyoyi, ta sha alwashin kwace mulki a 2027.

Jam'iyyar ta jaddada cewa za ta fatattaki gwamnatin Bola Tinubu duk da ba ta da gwamnoni masu ci.

ADC ta yi tone tone kan barazanar Tinubu ga gwamnoni
ADC ta fadi dalilin da ya sa gwamnoni ba su shiga cikinta ba. Hoto: Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

Jam'iyyar ADC ta yi magana kan gwamnoni

Mai magana da yawun jam’iyyar, Bolaji Abdullahi ya bayyana hakan bayan taron da aka yi a Abuja, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi sabon aikin da Ganduje zai yi wa APC a matakin kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam’iyyar ta ce gwamnoni ba su shiga cikinta ba saboda fargabar barazana daga gwamnatin Tinubu, amma jama’a na fushi kuma sun shirya faɗa da APC.

ADC ta bayyana shirinta na yin takara da APC kafada da kafada, tana mai cewa zai yi wahala a yi magudin zaɓe a 2027.

Taron ya fara da girmama marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta hanyar yin shiru na dakika guda.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma shugaban rikon kwarya na ADC, Sanata David Mark, da wasu manya sun halarci taron.

Abdullahi ya ce:

"Ba sai mun nemi gwamnoni masu ci ba, saboda muna sanin irin barazanar da ake musu daga gwamnatin APC. "
ADC tana da goyon bayan mafi yawan ’yan Najeriya da ba su gamsu da tafiyar da kasar ba."
ADC ta yi magana kan zaben 2027
ADC ta sha alwashin kwace mulkin Tinubu. Hoto: Bolaji Abdullahi.
Asali: Twitter

ADC ta caccaki masu mata fatan tsiya

Game da hasashen rugujewar jam'iyyar ADC, Bolaji ya ce duk maganar karya ce saboda tun farko suka ce za ta ruguje tun kafin a fara.

Kara karanta wannan

Ana rade radin gwamnan Yobe zai fita daga APC zuwa ADC, hadiminsa ya yi magana

"Da aka fara, sun ce za ta mutu tun kafin ta fara. Yanzu kuma suna ce mata watanni shida ne.
"Amma gaskiya, ko wane talaka ya san cewa halin da ake ciki ba za a cigaba da shi ba. ADC ce mafita."

- Bolaji Abdullahi

Ya ce akwai tsarin da zai hana wata ƙungiya ko mutum ya mallaki jam’iyyar ko ya karkatar da ita da kansa.

Tun da farko, David Mark ya ce Arewa na fama da matsaloli da yawa, kuma ADC na da ikon gyara yankin, Punch ta ruwaito.

Ya bukaci a hada kai da zaman lafiya domin ceto Arewa daga rikici da tashin hankali da ke addabar yankin.

Atiku ya magantu kan salon mulkin Tinubu

Kun ji cewa Ofishin Atiku Abubakar ya zargi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da rashin kulawa da matsalolin tattalin arziki da na tsaro.

Hadimin Atiku ya ce shugaban kasar yana rura wutar rikici a jam’iyyun adawa da amfani da hukumomin gwamnati don dakile su.

Yan ADC sun gargadi Tinubu da ya daina shisshigi cikin harkokin jam’iyyar adawa, ya mayar da hankali kan wahalhalun ‘yan kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel