Bayan Tafiyar Atiku, An Yi Hasashen Matsayi da PDP Za Ta Ƙare a Sakamakon Zaɓen 2027

Bayan Tafiyar Atiku, An Yi Hasashen Matsayi da PDP Za Ta Ƙare a Sakamakon Zaɓen 2027

  • Tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose ya ce jam'iyyar PDP ba za ta iya taɓuka komai ba a babban zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa a 2027
  • Fayose ya yi hasashen cewa duba da rigingimun da suka addabi jam'iyyar adawa ta PDP, yana ganin za ta kare a matsayi na huɗu
  • Ya kuma soki shugabannin PDP na yanzu, yana mai zarginsu da wulaƙanta ƴaƴan jam'iyya da suka sadaukar da kansu wajen yiwa PDP aiki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yi hasashen cewa jam’iyyar adawa ta PDP za ta fuskanci mummunan sakamako a zaben 2027.

Ayodele Peter Fayose ya yi ikirarin cewa jam'iyyar PDP za ta iya zuwa na huɗu a sakamakon zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa a 2027.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: An ji dalilan da suka jawo naɗa Ministan Tinubu a matsayin shugaban APC

Tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose.
Ayo Fayose ya yi hasashen faduwar PDP a zaben 2027 Hoto: Ayo Fayose
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan, wanda dan PDP ne kuma daya daga cikin tsofaffin Gwamnonin G5, ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na Channels TV a ranar Juma’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane matsayi PDP za ta ƙare a zaɓen 2027?

Fayose dai na ɗaya daga cikin tawagar G5, wacce ta yaƙi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar a zaɓen 2023.

“Addu’ata ita ce PDP ta zo ta hudu. Yau, ina fada muku da ƙarfin gwiwa ta cewa PDP za ta zo ta hudu a babban zaben 2027,” inji shi.

A cewar tsohon gwamnan, rikicin cikin gida da kuma korar manyan jiga-jigai daga jam’iyyar PDP sun raunana karfinta a fagen siyasa.

Fayose ya faɗi abin da ke kassara PDP

A ruwayar Vanguard, Fayose ya ci gaba da cewa:

“A mafi yawan jihohi, sun riga sun samu matsala. Sun kori shugabanni da dama, wataƙila hakan alheri ne gare su, amma bari in tunatar da ku, ni na kasance cikin tawagar G5.”

Kara karanta wannan

Bayan tafiyar Atiku, PDP ta fara hangen wanda za ta tsayar takarar shugaban ƙasa a 2027

Ya soki shugabancin PDP saboda abin da ya kira “wulakanci da cin amanar da suke yi wa ’yan jam’iyya masu mutunci,” irin shi.

Fayose da muƙaddashin shugaban PDP na kasa, Umar Damagum.
Fayose ya nuna ɓacin ransa kan yadda PDP ke wulaƙanta ƴaƴanta masu mutunci Hoto: Ayo Fayose, @OfficialPDPNig
Asali: Facebook

Tsohon gwamna ya caccaki shugabannin PDP

“Na sadaukar da kaina ga PDP. Ba zai yiwu a ci gaba da wulakanta mutum kamar ni ba. Lokacin da na shigo PDP ba ni da abokai, ni kaɗai na shigo.
“Ta yaya jam’iyya za ta wulaƙanta mutumin da ya yi gwamna karo biyu, wanda ya yi duk mai yiwuwa don dorewar jam’iyyar, amma a wulaƙanta shi, so kuke na yaba masu? Ba zai yiwu ba."
“Haɗa alaka da PDP a yau abin kunya ne, jam’iyyar ta yi raunin da ba za ta iya cin kowane irin zaɓe ba, ba ma a kawo batunta a sahun farko, ina addu'ar kar ta ƙare a na huɗu a zaɓen 2027."

- Ayo Fayose.

2027: PDP za ta ɗauko ɗan takara daga Kudu

A wani labarin, kun ji cewa ƙungiyar waɗanda suka kafa jam’iyyar PDP ta amince da ɗauko ɗan takarar shugaban ƙasa daga Kudancin Najeriya a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Damagum: Shugaban PDP ya fito fili ya fadi wadanda suka assasa matsalolin jam'iyyar

Wannan matsaya na zuwa ne makonni kaɗan bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar PDP.

Farfesa Jerry Gana, tsohon Ministan Yaɗa Labarai kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa PDP, ya jaddada bukatar miƙa tikitin shugaban ƙasa na 2027 zuwa Kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262