"Labarin Ƙarya," An Ji Gaskiyar Abin da Ya Faru kan Batun Ganawar Tinubu da Kwankwaso
- A kwanakin baya an yaɗa labarin cewa Shugaba Bola Tinubu ya gana da Rabiu Kwankwaso a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja
- Sai dai bayanai daga na kusa da Kwankwaso da hadiman fadar shugaban ƙasa sun nuna cewa wannan rahoton ba gaskiya ba ne
- Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabir Masari ya ƙaryata labarin ganawar Tinubu da Kwankwaso
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - A ranar Litinin, wasu kafafen yada labarai sun ruwaito cewa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, sun yi ganawar sirri a Aso Rock.
Rahoton ya yi ikirarin cewa Shugaba Tinubu da jagoran NNPP na ƙasa, sun keɓe a fadar shugaban kasa kuma sun tattauna batun siyasa da abin da ya shafi ƙasa.

Kara karanta wannan
Gaskiya ta fito: An ji dalilan da suka jawo naɗa Ministan Tinubu a matsayin shugaban APC

Source: Twitter
Punch ta kawo rahoton, tana mai cewa ganawar na zuwa ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin cewa Shugaba Tinubu na ƙoƙarin jawo Kwankwaso ya dawo APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka zalika, an yaɗa jita-jitar cewa da yiwuwar Tinubu ya ajiye Kashim Shettima, ya ɗauki Kwankwaso, tsohon ɗan takarar shugaban kasa na NNPP a matsayin abokin takara a 2027.
Abin da rahoton ganawar Kwankwaso-Tinubu ya ƙunsa
A cewar rahoton da ake ta yadawa:
“Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso, ya yi ganar sirri da Shugaba Bola Tinubu a gidansa na fadar shugaban ƙasa a ranar Litinin.
"Hakan ta faru lokacin da Kwankwaso ya halarci buɗe taron tattalin arzikin jeji a Aso Rock. Wannan shi ne karo na biyu da jagororin biyu suka gana cikin fiye da shekaru biyu.
“Da yake hira da manema labarai a fadar shugaban kasa, Kwankwaso ya ce sun tattauna ne kan siyasa da batun shugabanci. Ya kuma ce akwai yiyuwar ya yi aiki da Tinubu, amma bai fayyace bayani ba.”

Kara karanta wannan
"An yi watsi da Arewa," Kwankwaso ya soki Gwamnatin Tinubu, ya faɗi kalamai masu daci
Da gaske Shugaba Tinubu ya gana da Kwankwaso?
Sai dai majiyoyi na kusa da tsohon Gwamnan Jihar Kano da kuma wasu sahihan hanyoyin samun labarai daga fadar shugaban kasa sun musanta wannan rahoto ga Daily Trust.
Ɗaya daga cikin majiyoyi na kusa da Kwankwaso ya ce,
“Wannan labarin ba gaskiya ba ne. Kwankwaso ya je Aso Rick ne kawai domin halartar taron da aka ambata, ba don wata ganawa ba.”

Source: Facebook
Fadar shugaban ƙasa ta musanta labarin
Haka kuma, wasu majiyoyi biyu daga fadar shugaban kasa sun tabbatar da cewa babu wata ganawa da ta gudana tsakanin Tinubu da Kwankwaso.
Mai baiwa shugaban ƙasa shawara ta musamman kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabir Masari, ya bayyana rahoton cewa Tinubu ya gana da Kwankwaso a matsayin “labarin karya”.
Wata majiya daga fadar shugaban kasar ta ce:
“Babu wani abu makamancin haka da ya faru. Idan an yi taron ko a ofis ko a gidan shugaban kasa, da za a sani. Ku ji wannan daga gare ni, babu wani abu makamancin haka da ya faru.”
Kwankwaso ya caccaki Gwamnatin Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Rabiu Kwankwaso, ya caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu bisa abin da ya kira watsi da yankin Arewacin Najeriya.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP a 2023 ya zargi gwamnati mai ci karkatar da mafi tsokar albarkatun ƙasa zuwa yanki guda na ƙasar nan.
Tsohon gwamnan ya ce galibin titunan Arewa sun lalace matuka, yayin da gwamnatin APC ke ci gaba da ware kuɗaɗen manyan ayyuka a yankin Kudu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
