An Rasa Kwankwaso a Taron da Tinubu Ya Yi da Tsofaffin Gwamnonin 1999
- Bola Tinubu ya shiga ganawa da wasu daga cikin tsofaffin gwamnoni a Najeriya da suka yi mulki bayan dawowa dimokuraɗiyya
- Shugaba Tinubu ya karɓi tsofaffin gwamnonin ne da suka yi mulki tare a shekarar 1999 a fadar Aso Villa da ke birnin tarayya Abuja
- Tsohon gwamna, James Ibori ne ya jagoranci tsofaffin gwamnoni, waɗanda suka taka muhimmiyar rawa tun farkon mulkin dimokuradiyya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu yana ganawa da tsofaffin gwamnoni da suka yi mulki tare a birnin Abuja.
Tinubu ya karɓi tsofaffin gwamnoni na shekarar 1999 a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Juma’a 25 ga watan Yulin 2025.

Source: Facebook
Tinubu ya yi zama da tsofaffin gwamnonin 1999
Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkar kafafen sadarwa, Dada Olusegun ne ya tabbatar da haka a shafin X a yammacin Juma'a 25 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan
Gaskiya ta fito: An ji dalilan da suka jawo naɗa Ministan Tinubu a matsayin shugaban APC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsofaffin gwamnoni su ne farkon rukunin da aka zaɓa a farkon Jamhuriyar Najeriya ta Hudu a 1999.
Tsohon gwamna, James Ibori na jihar Delta shi ya jagoranci abokan nasu zuwa fadar shugaban ƙasa.
Ko da yake ba a bayyana cikakken abin da suka tattauna ba yayin rubuta wannan rahoto, ana ganin ganawar wani ɓangare ne na shawarwarin siyasa da Tinubu ke yi.

Source: Twitter
A ina Kwankwaso ya makale bai cikin taro?
Rukunin gwamnoni na 1999 ana kallon su a matsayin masu tasiri wajen tafiyar da dimokradiyya, inda suka taka rawar gani tun dawowar mulkin farar hula.
Wannan ganawar na daga cikin jerin abubuwan da Shugaba Tinubu ke yi don ƙarfafa haɗin kai da goyon bayan siyasa kafin ɗaukar manyan matakai.
Sai dai kuma ba duka ba ne suka halarci taron saboda ba a gano Sanata Rabi'u Kwankwaso ba.
Kwankwaso daga jihar Kano da sauran gwamnonin sun yi mulki tare da Tinubu a 1999 wanda ya mulki Lagos.
Sauran wadanda ba a gani ba sun hada da Ahmad Makarfi da Attahiru Bafarawa da suka mulki jihohin Kaduna da Sokoto a lokacin.
Tsofaffin gwamnonin da suka halarci taron da Tinubu
Daga cikin mahalarta taron akwai tsohon gwamnan Delta, James Ibori wanda shi ne jagorar tafiyar sai Jolly Nyame wanda ya mulki jihar Taraba.
Sai tsohon gwamnan, Akwa Ibom Obong Victor Attah da tsohon gwamnan Kebbi, Sanata Adamu Aliero da na Adamawa, Boni Haruna.
Har ila yau, a taron akwai tsohon gwamnan jihar Bauchi, Ahmed Mu'azu da na Benue, George Akume wanda shi ne sakataren gwamnatin taraya.
Sauran sun hada da Donald Duke wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Cross River da kuma na jihar Ebonyi, Sam Ominyi Egwu da sauransu.
Kwankwaso ya soki Tinubu kan watsi da Arewa
Mun ba ku labarin cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Rabiu Kwankwaso ya caccaki gwamnatin Shugaba Tinubu kan abin da ya kira watsi da Arewacin Najeriya.
Kwankwaso ya zargi gwamnati mai ci da karkatar da hankalinta wajen gina yankin Kudu da albarkatun ƙasar nan.
Ya ce titunan Arewa sun lalace matuƙa, inda ya shawarci shugaban ƙasa ya yi adalci wajen raba albarkatu tsakanin Arewa da Kudu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
