Gaskiya Ta Fito: An Ji Dalilan da Suka Jawo Naɗa Ministan Tinubu a Matsayin Shugaban APC

Gaskiya Ta Fito: An Ji Dalilan da Suka Jawo Naɗa Ministan Tinubu a Matsayin Shugaban APC

  • A ranar Alhamis, 24 ga watan Yuli, 2025 jam'iyyar APC ta zaɓi ministan jin ƙai, Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugabanta na kasa
  • Wannan lamari ya haifar da ruɗani kan dalilin Shugaba Tinubu na goyon bayan Kirista daga Arewa ta Tsakiya tare da ba shi shugabancin APC
  • Dataktan yaɗa labarai na APC ta kasa, Bala Ibrahim ya bayyana wasu daga cikin dalilin da suka sa Tinubu da tawagarsa suka ɗauki wannan mataki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Naɗa Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa a ranar Alhamis ya haifar da ruɗani kan lissafin siyasa da ya sa aka zaɓe shi.

Nentawe, wanda ke rike da kujerar Ministan Harkokin Jin ƙai, ya zama shugaban APC na 5 a hukumance a taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) karo na 14 da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Ganduje ya aiko saƙo daga Landan kan naɗin sabon shugaban APC na ƙasa

Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe.
An samu ƙarin bayani kan dalilin naɗa Nentawe a matsayin shugaban APC Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Ya maye gurbin Dr Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya yi murabus a ranar 27 ga Yuni, yana mai danganta hakan da dalilan rashin lafiya, kamar yadda APC ta fitar a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa aka naɗa Minista ya shugabanci APC?

Majiyoyi sun ce an naɗa shi biyo bayan shawarwari da matsin lamba daga jiga-jigan yankin Arewa ta Tsakiya, waɗanda suka nace cewa a bar yankin ya kammala wa’adin Abdullahi Adamu.

Daraktan Yaɗa Labarai na APC, Bala Ibrahim, a wata hira ta waya da Daily Trust, ya ce naɗin Nentawe ya kawo ƙarshen tsohuwar al’ada ta zaɓar tsofaffin gwamnoni a matsayin shugabannin jam’iyya.

Bala Ibrahim ya ce:

“Abin da na fahimta shi ne, ana buƙatar mutum mai ƙwarewa, wanda ba tsohon gwamnan da aka saba naɗawa a matsayin shugaban jam'iyya ba, wanda zai iya jan ragama har zuwa babban taro na ƙasa.

Da aka tambaye shi ko an yi wannan zaɓi ne domin lallashin yankin Arewa ta Tsakiya da daidaita batun addini, musamman saboda sukar da ake wa tikitin Musulmi da Musulmi, Bala ya ce:

Kara karanta wannan

2027: Sabon shugaban APC ya yi magana kan yiwuwar sauya shekar Kwankwaso

"Eh hakan na na yiwuwa. Wadannan dalilai na iya taka rawa sosai.

Nentawe zai iya jagorantar APC zuwa ga nasara?

Kan ko sabon shugaban zai iya kawo nasara ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da APC a 2027, ya ce:

“Shi ne Darakta Janar na kamfen ɗin Tinubu/Shettima a Jihar Filato a 2023, kuma duk da cewa jihar ba ta zaɓi APC ba, sun yi iya kokarinsu.”

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa Shugaba Tinubu da tawagarsa na ƙoƙarin jawo goyon bayan jihohin da ba su zaɓe shi a 2023 ba.

Masana sun hango dalilan naɗa ministan Tinubu

A sharhinsa kan wannan ci gaba, masani a harkokin siyasa, Jackson Lekan Ojo, ya ce an zaɓi Nentawe ne saboda ana bukatar shugaban jam’iyya mai biyayya ga Shugaba Tinubu kafin 2027.

Ojo ya ce:

“Babban dalilin da ya sa aka kawo shi shi ne suna neman mutum wanda zai yi biyayya ga Shugaba Tinubu. Wani da za su iya amfani da shi. Wani da ba zai ci amanarsa ba.

Kara karanta wannan

Nentawe: Sabon shugaban APC ya fadi salon mulkin da zai yi a jam'iyyar

“Al-Makura ya cancanta, Sanata Sani Musa daga Jihar Neja ma ya dace, dukkansu daga Arewa ta Tsakiya suke amma waɗannan mutane ne masu dogara ra'ayin kansu."
Shugaban APC tare da Bola Tinubu da Shettima.
Masana sun ce an naɗa Nentawe ne saboda ya yiwa Tinubu ladabi da biyayya Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Ganduje ya yaba da naɗin sabon shugaban APC

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yaba da nadin Farfesa Nentawe Yilwatda.

Ganduje, wanda yanzu haka yake Landan a ƙasar Burtaniya, ya jinjinawa shugaban ƙasa bisa yadda ya yi nazari da wanda ya dace ya shugabanci jam'iyyar APC.

Ya bukaci sabon shugaban APC da ya ɗora daga inda ya tsaya, kamar yadda shi ma ya ɗora daga nasarorin da magabacinsa, Sanata Abdullahi Adamu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262