2027: Sabon Shugaban APC Ya Yi Magana kan Yiwuwar Sauya Shekar Kwankwaso

2027: Sabon Shugaban APC Ya Yi Magana kan Yiwuwar Sauya Shekar Kwankwaso

  • Sabon shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa ƙofar jam’iyyar a buɗe take ga Rabiu Kwankwaso da duk 'yan adawa
  • Farfesa Yilwatda ya ce lokacin da nasarar Bola Tinubu ta bayyana, za a ga da dama daga cikin waɗanda suka fita suna komawa APC
  • Nentawe Yilwatda ya karɓi shugabancin jam’iyyar ne bayan Abdullahi Ganduje, wanda ya sauka daga kujerar bisa wasu dalilai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sabon shugaban jam’iyyar APC, Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa jam’iyyar na maraba da tsofaffin ’ya’yanta da suka bar ta, ciki har da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

A jiya Alhamis ne jam'iyyar APC ta rantsar da Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin shugaba bayan saukar Abdullahi Umar Ganduje.

Shugaban APC ya ce za su yi maraba da Kwankwaso
Shugaban APC ya ce za su yi maraba da Kwankwaso. Hoto: All Progressive Congress|Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Yayin wata hira da aka yi da shi a Channels Television, Yilwatda ya ce ko da yake ba zai iya tabbatar da komawar Kwankwaso ba, amma ya ce “ƙofarmu a buɗe take”.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi sabon aikin da Ganduje zai yi wa APC a matakin kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ayyukan Shugaba Bola Tinubu da manufofin jam’iyyar za su janyo hankalin wadanda suka fita daga APC su dawo gida da kansu.

Jam'iyyar APC ta buɗe kofa ga Kwankwaso

Farfesa Yilwatda ya ce jam’iyyar APC ta buɗe kofofinta ga duk wani tsohon ɗan jam’iyya da ke da sha’awar dawowa cikin sahunta.

Ya jaddada cewa babu wani abu da zai hana wanda ya bar jam’iyyar komawa idan ya ga hakan ya dace.

Yayin amsa tambaya a kan yiwuwar komawar tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, Yilwatda ya ce:

“Na faɗa muku cewa ƙofar jam’iyyar mu a buɗe take.”

Tinubu zai jawo ’yan siyasa zuwa APC

A cewar sabon shugaban na APC, ayyukan Shugaba Tinubu da matakan da yake ɗauka zai sa ’yan siyasa da dama da suka fita daga jam’iyyar su dawo.

Ya ce:

“Idan lokacin kowa ya yi, zai bayyana da kansa. Ku bari lokaci ya yi, mutane za su fahimci manufar jam’iyya da abin da gwamnati ke yi.”

Kara karanta wannan

Ganduje ya aiko saƙo daga Landan kan naɗin sabon shugaban APC na ƙasa

Ya ƙara da cewa:

“Idan kai gwamna ne kuma ka ga kudin shigan gwamnati ya ƙaru da kaso 40 cikin wata guda, ba za ka so ci gaba da wannan gwamnatin ba?”

Kwankwaso dai ya kasance cikin jam’iyyar APC kafin ya sauya sheƙa zuwa PDP a watan Yulin 2018.

Daga bisani kuma ya koma jam’iyyar NNPP a watan Maris na 2022, inda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Sabon shugaban APC, Farfesa Yilwatda
Sabon shugaban jam'iyyar APC, Farfesa Yilwatda. Hoto: All Progresive Congress
Source: Twitter

Farfesa Nentawe Yilwatda ya karɓi shugabancin jam’iyyar APC ne bayan mambobin kwamitin NEC na jam’iyyar sun amince da nadinsa a wani zama na jam’iyyar a fadar shugaban ƙasa.

Makomar siyasar Kwankwaso a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa wani masani ya yi magana kan makomar siyasar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a Najeriya.

Dr Sani Yakubu Wudil ya bayyana cewa Kwankwaso na tsaka mai wuya a yadda siyasar Najeriya ta nuna.

Ya ce zama a NNPP ba lallai ya ba shi damar zama shugaban kasa ba a 2027, haka zalika shiga ADC ko sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng