Yilwatda: Jam'iyyar APC ta Zabi Sabon Shugaba a Najeriya bayan Ganduje

Yilwatda: Jam'iyyar APC ta Zabi Sabon Shugaba a Najeriya bayan Ganduje

  • Jam’iyyar APC ta zabi Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyya na kasa a taron NEC karo na 14
  • Farfesa Yilwatda ya maye gurbin Abdullahi Umar Ganduje, tsohon gwamnan Kano da ya jagoranci APC tun bayan Abdullahi Adamu
  • Sabon shugaban ya hau wannan mukami ne a wani lokaci da ake fuskantar gyare-gyare da sababbin dabarun siyasa a jam’iyyar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta gudanar da taron kwamitin zartaswa na kasa (NEC), inda aka zabi Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyya na kasa.

Zaben Farfesa Yilwatda ya zo ne bayan saukar Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam’iyyar, wanda ya yi mulkin jam’iyyar kafin yanzu.

Farfesa Yilwatda da ya dawo sabon shugaban APC.
Farfesa Yilwatda da ya dawo sabon shugaban APC. Hoto: All Progressive Congress
Asali: Twitter

Jam'iyyar APC ta tabbatar da labarin a wani sako da ta wallafa a shafinta na X a yau Alhamis, 23 ga Yuni, 2025.

Kara karanta wannan

Nentawe: Sabon shugaban APC ya fadi salon mulkin da zai yi a jam'iyyar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar APC: Wanene Farfesa Yilwatda Nentawe?

Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda kwararren masanin kimiyya ne daga jihar Filato kuma tsohon dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar APC a zaben 2023.

Yana rike da mukamin ministan jin kai a gwamnatin shugaba Bola Tinubu kafin nada shi shugaban jam'iyyar.

Yadda taron APC ya gudana Abuja

A yau Litinin 22 ga watan Yuli, 2025, jam’iyyar APC mai mulki ta gudanar da taronta na kwamitin zartaswa na kasa karo na 14 a dakin liyafa na fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Yadda aka rantsar da sabon shugaban APC na kasa.
Yadda aka rantsar da sabon shugaban APC na kasa. Hoto: All Progressive Congress
Asali: Twitter

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, su ne suka jagoranci taron wanda ya samu halartar manyan shugabanni daga sassa daban-daban.

Taron dai ya kasance mai muhimmanci domin an shirya gudanar da muhimman al'amura da suka hada da tunawa da marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.

Fitattun 'yan siyasa sun halarci taron APC

Daga cikin wadanda suka halarci taron har da tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas.

Kara karanta wannan

Ganduje ya sauka, Yilwatda ya hau: Jerin shugabannin APC 9 daga 2013 zuwa 2025

Haka kuma, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Jibrin Barau, da mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, suma sun halarci taron da ya tara jiga-jigan jam’iyyar APC.

Mambobin kwamitin NWC na jam’iyyar, ministoci da wasu muhimman jami’an gwamnati da ke cikin jam’iyyar APC sun bayyana a taron domin tattauna makomar jam’iyyar.

Abubuwan da aka tattauna a taron APC-NEC

Bisa bayanan da Daily Trust ta gani, an tanadi yin jawabi na girmamawa ga marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya rasu a kwanakin baya a birnin Landan.

Kazalika, za a gudanar da rantsar da sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, wanda aka zaba domin maye gurbin Abdullahi Umar Ganduje.

Gwamna Buni ya ce yana APC har yanzu

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya karyata jita jitar cewa ya sauya sheka.

Mai magana da yawun gwamnan, Mamman Muhammad ne ya karyata haka yayin hira da manema labarai.

Mamman ya bayyana cewa Mai Mala Buni zai cigaba da zama a jam'iyyar APC da ta ba shi dama ya zama gwamna har sau biyu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng