APC Tana Neman Sanatoci 2 domin Cin Karenta babu Babbaka a Majalisar Dattawa

APC Tana Neman Sanatoci 2 domin Cin Karenta babu Babbaka a Majalisar Dattawa

  • Jam'iyyar APC mai mulki na dab da samun babban rinjaye a Majalisar Dattawa bayan shekar Sanatoci hudu daga PDP
  • Bayan sauya shekar wasu ‘yan PDP, APC yanzu na da kujeru 224 cikin 360, wanda ke ƙarfafa matsayinta a majalisar wakilai
  • Masu sharhi na siyasa sun ce rinjayen APC zai kawo tasgaro ga tsarin dimokuraɗiyya da kawo tsarin jam'iyya ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Jam’iyyar APC mai mulki na dab da cimma rinjaye na kaso biyu bisa uku a Majalisar Dattawan kasar nan.

Jam'iyya mai mulki ta samu wannan dama ne bayan wasu ‘yan majalisar daga PDP sun sauya sheka zuwa APC.

Majalisar wakilai da ta dattawa
APC tana ƙara ƙarfi a majalisar Hoto: Nigerian Senate/House of Representatives
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa yawan kujerun APC a Majalisar Dattawa zuwa 70 cikin 109, saura biyu kacal a kai 72 da ake bukata don rinjaye kamar yadda doka ta tanada.

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, Shugaba Tinubu ya nuna wanda yake so ya zama sabon shugaban APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kuri'un Sanatoci 72 cikin 109 ake bukata domin zartar da duk wani hukunci a majalisar dattawa, ma'ana za ta iya kai wa yadda 'yan adawa ba su da ikon hana a yi wani abin.

Sanatocin da suka sauya sheka zuwa APC

Sanatocin da suka sauya sheka sun hada da: Sanata Sampson Ekong (Akwa Ibom ta Kudu) da Sanata Aniekan Bassey (Akwa Ibom Arewa maso Gabas).

Sauran sun haɗa da Sanata Francis Fadahunsi (Osun Gabas) sai kuma Sanata Olubiyi Fadeyi (Osun Ta Tsakiya).

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya karanta takardun sauya shekar sanatocin yayin zaman da ya gudana a ranar Talata.

Majalisar Dattawan Najeriya
Yan adawa na tsoron ƙarfin APC a majalisa Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Wannan ci gaba ya kara tabbatar da ƙarfin APC a majalisa, lamarin da masana ke fargabar zai iya yin illa ga dimokuradiyya da tsarin mulkin Najeriya.

A halin yanzu, PDP na da kujeru 28, LP na da 5, SDP 2, NNPP da APGA kuwa na da kujera guda-guda, sai guraben kujeru biyu da ke jiran zabukan cike-gurbi.

Kara karanta wannan

An tayar jijiyoyin wuya a Majalisar Tarayya da mambobi 3 suka sauya sheƙa zuwa APC

Ana fargabar ƙarfin APC a majalisa

Adnan Mukhtar Tudun Wada, tsohon jigo ne a PDP da ya sauya sheƙa zuwa ADC a Kano, ya sanar da cewa wannan na nufin Najeriya za ta iya komawa kan tsarin jam'iyya ɗaya.

Ya shaida wa Legit cewa:

Barazana ce ga dimokuraɗiyya. Abin takaici ne ganin cewa kowace doka da za ta bi Majalisar Ƙasa za a amince da ita ko da 'yan adawa ba su goyi bayanta ba."
"Zan iya cewa muna dab da komawa tsarin jam’iyya ɗaya.

Ya kara da cewa matakin sauya sheka da zaɓaɓɓun ƴan majalisa ke yi zai kara buɗe wa jama'a ido su gane mutanen da suka zaɓa.

A kalaman Adnan Mukhtar Tudun Wada:

"Yanzu al’ummar Najeriya ne za su buɗe idonsu su gane cewa mutanen da suka zaɓa ba don alfanunsu suke aiki ba, sai don bukatunsu na kai."

APC, NNPP sun tsayar da ɗan takarar majalisa

A baya, mun wallafa cewa an fara shirye-shirye domin gudanar da zaɓen cike gurbi na majalisar wakilai a mazabar Babura/Garki da ke jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun fatattaki zugar 'yan ta'adda, an aika kusan 95 ga mahaliccinsu

Shirin ya biyo bayan rasuwar tsohon dan majalisar, Hon. Isah Dogon Yaro, a ranar 9 ga Mayu, 2024, kuma tuni APC da NNPP sun gudanar da zaɓen fidda gwaninsu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da cewa za a gudanar da zaben cike gurbin a ranar 16 ga watan Agusta, 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng