Magana Ta Ƙare, Shugaba Tinubu Ya Nuna Wanda Yake So Ya Zama Sabon Shugaban APC
- Idan har ba a samu wani sauyi daga baya ba, shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya nuna wanda yake so ya zama sabon shugaban APC na ƙasa
- Majiyoyi da dama daga fadar shugaban kasa da APC sun nuna cewa Tinubu ya fi aminta da ministan jin ƙai, Nentawe Yilwatda ya maye gurbin Ganduje
- Sai dai wasu rahotanni sun nuna cewa Tanko Al-Makura na cikin zaɓi na sahun gaba idan wata matsala ta taso daga nan zuwa taron NEC
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Matuƙar ba a samu sauyi a sa'o'in da ke tafe ba, Ministan Harkokin Jin ƙai da Rage Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda, ne zai zama sabon shugaban APC na ƙasa.
Majiyoyi da dama sun bayyana cewa Nentawe shi ne babban zabin da ake dubawa don maye gurbin tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.

Source: Getty Images
Duk da haka, wasu majiyoyi da suka tattauna da Daily Trust a daren jiya sun ce tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Umaru Tanko Al-Makura, na cikin waɗanda ake nazari a kansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC na dab da yanke magajin Ganduje
A cewar wasu majiyoyi masu tushe, jagororin APC, da suka haɗa da shugaban ƙasa da gwamnoni, sun takaita zaɓinsu ne tsakanin Nentawe da Al-Makura.
Nentawe dan asalin Jihar Filato ne, daga Arewa Ta Tsakiya, yankin da aka ware wa kujerar shugaban APC na ƙasa tun da farko, kafin a naɗa Ganduje, wanda ya yi murabus a farkon wannan wata.
Wasu majiyoyi sun ce shugabannin APC na kallon Al-Makura a matsayin zaɓi na biyu idan har abubuwa ba su tafi a yadda aka tsara ba kan Nentawe.
Hakan dai na zuwa ne yayin da ya rage sa'o'i kaɗan a fara taron kwamitin zartarwa (NEC) na APC ta ƙasa, wanda ke da alhakin yanke wanda za a naɗa.

Kara karanta wannan
Gaskiya ta fito: An ji dalilan da suka jawo naɗa Ministan Tinubu a matsayin shugaban APC
Duk wanda ya zama shugaban APC a yau, ko dai Nentawe ko Al-Makura, zai maye gurbin nuƙaddashin shugaba, Ali Bukar Dalori, rahoton The Nation.
Me yasa APC za ta sauya Ali Dalori?
Wasu majiyoyi sun ce Dalori zai iya cigaba da zama a matsayin shugaban rikon kwarya na dogon lokaci “da ba don wasu dalilai bayyanannu ba."
“Dalori dan Borno ne, jihar da Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima ya fito. Shugaban kasa da jam’iyyar APC na so su warware batun shugabanci gaba ɗaya.
"Tinubu yana neman wanda zai zama mai biyayya gare shi kamar yadda Sanata Adamu ya kasance ga Buhari,” in ji wata majiya.
Jerin masu neman shugabancin APC
Sauran da aka ta ambata a matsayin masu neman kujerar sun haɗa da:
– Sanata Sani Musa (Jihar Neja)
– Sanata Salihu Mustapha (Kwara)
– Tsohon gwamnan Filato Joshua Dariye (Filato)
– Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume (Benuwai)
– Sanata Abu Ibrahim (Katsina).

Source: Twitter
Wanda Tinubu ke son ya maye gurbin Ganduje
Majiyoyi daga hedikwatar APC, fadar shugaban ƙasa da ma’aikatar jinƙai sun tabbatar cewa sunan Nentawe na fitowa akai-akai a cikin tattaunawa na sirri a cikin gida.
Wani babban jami’i a hedikwatar APC ya ce:
“Yadda shugaban kasa Tinubu ke nuna alamu ya bai wa Nentawe gagarumar dama.
“Daga kwamitin gudanarwa (NWC) har zuwa fadar shugaban kasa, mutane da dama sun yarda cewa Nentawe shi ne a sahun gaba, har an fara murnar yiwuwar ɗan asalin Jihar Filato ya zama shugaban jam’iyyar.”
APC ta gama shirya taron NEC
A wani labarin, kun ji cewa APC ta sanya ranar Alhamis, 24 ga watan Yuli, 2025 a matsayin ranar da za ta gudanar da taron NEC.
Taron zai tattauna a kan wadansu batutuwa da ke kokarin barazana ga hadin kan jam'iyyar, daga ciki har da batun maye gurbin Abdullahi Ganduje.
Kafin taron NEC, 'yan kwamitin gudanarwa na APC sun yi taro na sirri da ya dauki tsawon sa’o’i biyu amma ba su faɗi abin da suka tattauna ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

