Hadimin Atiku Ya Yi Murabus daga PDP a Zungureriyar Wasikar Shafi 9

Hadimin Atiku Ya Yi Murabus daga PDP a Zungureriyar Wasikar Shafi 9

  • Hadimin Atiku Abubakar, Demola Olarewaju ya fice daga PDP, yana zargin jam’iyyar da watsi da akidarta na kishin kasa
  • Olarewaju ya kara da zargin cewa yanzu PDP ta koma ƴar amshin shatan APC, ta kuma rungumi siyasar ƙabilanci hannu bibbiyu
  • A kalamansa, ya ce lokaci ya yi da ƴan adawa da su haɗa kai domin tabbatar da cewa an fatattaki APC daga mulkin Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Demola Olarewaju, babban hadimin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya sanar da ficewarsa daga PDP.

Ya ɗauki matakin makonni kaɗan bayan Atiku Abubakar ya fice daga PDP yayin da ake ƙoƙarin ƙara wa jam'iyyar haɗakar ƴan adawa ta ADC ƙarfi kafin 2027.

Kara karanta wannan

Tsohon mai neman takarar shugaban kasa a APC ya faɗa wa Tinubu gaskiya

Hadimin Atiku Abubakar ya bi ubangidansa
Hadimin Atiku Abubakar ya fice daga PDP Hoto: @DemolaRewaju
Asali: Twitter

A wasiƙa mai shafi tara da ya aika wa PDP, kuma ya wallafa a shafinsa na X, Olarewaju ya ce APC ita ce babbar matsalar da ta sako Najeriya a gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin Atiku Abubakar ya caccaki PDP

A cikin wasikar, Demola Olarewaju ya caccaki tsohuwar jam'iyyar bisa zargin cewa ta zama ƴar a bi yarima a sha kiɗa wajen kwaikwayon APC.

Ya nuna takaici game da zargin cewa yanzu PDP ta yi watsi da aƙidarta ta hadin kan Najeriya da tsarin mulkin karɓa-karɓa.

Zungureriyar wasikar da ya rubuta zuwa ga shugabar mazabar Aguda a karamar hukumar Surulere ta jihar Legas, Hon. Thessy Whyte, ta ce PDP ta sauka daga tsari.

Hadimin Atiku ya ce PDP ta sauka daga tsari
Hadimin Atiku ya zargi PDP da zama ƴar amshin shatan APC Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Ya ce:

“Jam’iyyar ta zubar da akidarta ta kishin Najeriya. Yanzu babu haɗin kai a Najeriya kuma ba ta da burin samun nasarar zaɓe mai zuwa."

An yi bayanin karɓa-karɓa a PDP

Hadimin Atiku, ya ƙara da cewa an bijiro da tsarin raba muƙamai a tsakanin shiyyoyin ƙasar nan domin a samun daidaito kuma kada a watsar da wani sashi.

Kara karanta wannan

Ana neman haɗa Atiku da Peter Obi faɗa bayan 'gano' wanda ADC ke shirin ba takara a 2027

A bayaninsa, ya ce tsarin karɓa-karɓa ko raba muƙaman zai zo ne bayan an fitar da ɗan takara ko an yi nasarar zaɓe.

Ya ce:

“A gabanin zaben 2023, PDP ta fada tarkon siyasar kabilanci inda aka ƙirƙiro wani salon siyasa na Kudu ta tunkari yankin Arewa."

Tsohon matashin na PDP ya kira ƴan adawa

Olarewaju ya yi kira da a hada kai domin kalubalantar jam’iyyar APC, musamman gabanin zaben 2027.

Ya bayyana tsarin siyasar APC a matsayin wanda ke janyo rarrabuwar kai, yana mai cewa lokaci ya yi da za a samu hadin kai domin kada ita.

Ya ce:

“Jam’iyyar (PDP) da ya kamata ta nemi dan takarar da zai iya fuskantar Bola Tinubu a 2027, ita ce yanzu ta fi mayar da hankali kan siyasar kabilanci da ke karfafa mulkin Tinubu."

Jam'iyyar PDP za ta yi taron NEC

A wani labarin, mun wallafa cewa PDP ta shirya gudanar da babban taron kwamitinta ƙasa, don yin nazari kan tsarin karɓa‑karɓa da wasu matsalolinta.

Kara karanta wannan

PDP ta yi rashi, tsohon daraktan kungiyar gwamnoni ya koma ADC

Wannan yunkuri na zuwa ne bayan wasu rikice‑rikice na cikin gida da ke jawo ƙaruwar rarrabuwar kai a tsakanin ƴaƴan jam'iyyar, har wasu ma ficewa.

Wannan yunkuri na PDP ya zo ne a daidai lokacin da jam’iyyar APC mai mulki ke shirin gudanar da nata babban taronta da aka mayar fadar shugaban ƙasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel