2027: Sule Lamido Ya Fallasa Makarkashiyar Tinubu kan 'Yan Adawa
- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya soki gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
- Sule Lamido ya zargi gwamnatun Shugaba Tinubu da ƙoƙarin danne ƴan adawa ta hanyar yi musu cinnen hukumomin yaƙi da rashawa
- Hakazalika ya nuna cewa wannan hanyar da gwamnatin ke bi, babbar barazana ce ga dimokuraɗiyyar Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya caccaki gwamnatin tarayya, ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sule Lamido ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da amfani da hukumomin gwamnati a matsayin makami domin danne dimokuraɗiyya.

Source: Facebook
Sule Lamido ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da manema labarai a Kano, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
A yayin tattaunawar dai an tambaye shi game da matsayarsa ta siyasa yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
Wane zargi Sule Lamido ya yi kan Tinubu?
Sule Lamido ya yi zargin cewa hukumomi kamar hukumar yaƙi da cin hanci da Rmrashawa ta EFCC suna zama makamin muzanta jiga-jigan adawa har su miƙa wuya.
“A ɗauki misalin Okowa. Shi ne ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP. Sai kwatsam ya fuskanci tuhuma ta Naira tiriliyan 1.3. Amma yana komawa APC, sai komai ya lafa, babu EFCC, babu shari’a. An rufe komai."
- Sule Lamido
Sule Lamido ya ce wannan yanayi ya tabbatar da fitacciyar magana da ake jinginawa Sanata Adams Oshiomhole cewa "Da zarar ka shiga APC, an gafarta maka zunubanka".
Oshiomhole dai ya sha musanta cewa ya fadi hakan, yana zargin abokan hamayyarsa da amfani da kalmar don ɓata masa suna.
Sai dai Sule Lamido ya yi gargaɗin cewa amfani da hukumomi ta hanyar son rai da cin zarafin ikon gwamnati yana rushe dimokuraɗiyya a Najeriya, yana haifar da rashin tsaro, rashin amana da rashin haɗin kai na ƙasa.
"A yau, Najeriya ba ita ce kasar da muka sani shekaru 25 da suka wuce ba. Babu tsaro, babu kwanciyar hankali, babu amana. Ba za a samu ƙasa ɗaya ba idan sassa daban-daban suna rigima da juna."
- Sule Lamido

Source: Twitter
Sule Lamido ya yi magana kan haɗaka
Game da ƙoƙarin yin haɗaka kafin 2027, Sule Lamido ya ce saɓanin ƙawancen da aka tsara a 2014 wanda ya haifar da jam’iyyar APC, yanzun waɗanda ke ƙoƙarin kafa haɗaka ba su da tsari, rahoton Daily Post ya tabbatar da batun.
Ya ce haɗakar yanzu ta ta'allaka ne kan wasu ƴan tsirarun mutane, kuma ta rasa samun goyon bayan jam'iyyu.
Alhaji Sule Lamido na son a ceto Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana shirinsa na son ganin an ceto Najeriya.
Sule Lamido ya bayyana cewa a shirye yake ya shiga kowace irin tafiya ta siyasa idan har za ta kai ga ceto Najeriya.
Sai dai, ya ba da tabbacin cewa ba zai fice daga jam'iyyarsa ta PDP ba zuwa wata jam'iyyar siyasa ta daban.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

