Tsohon Mai Neman Takarar Shugaban Kasa a APC Ya Faɗa wa Tinubu Gaskiya
- Tsohon mai neman takarar shugaban ƙasa a APC, Adamu Garba ya zargi wasu na kusa da Shugaba Bola Tinubu da ɓoye masa gaskiya
- Ya yi zargin cewa wasu daga cikin waɗanda ke zagaye da shugaban na faɗa masa abubuwan da suka saɓa da halin da ƙasa ke ciki
- Daga cikin shawarwarin da ya bayar, Malam Adamu ya ce dole APC ta farka domin tunkarar ƙalubalen ƴan adawa a inuwar ADC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Adamu Garba, ɗan jam’iyyar APC kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, ya ce akwai matsaloli a gwamnatinsu.
Ya ce kwaɗayayyu ne suka zagaye Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya yi zargin cewa suna gaya masa ƙarya a kan halin da ƴan ƙasa ke ciki.

Kara karanta wannan
Ana neman haɗa Atiku da Peter Obi faɗa bayan 'gano' wanda ADC ke shirin ba takara a 2027

Source: Facebook
Garba ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Talata, 22 ga watan Yuli, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adamu: 'ADC ba za ta taɓuka komai ba'
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa tsohon ɗan takarar ya soki ƙawancen jam’iyyun adawa da aka kafa a ƙarƙashin tutar ADC.
Ya ƙara cewa:
“Waɗannan mutanen (kawancen ADC) suna jiran gazawarmu. Wannan ne dalilin da ya sa dole mu farka. Dole mu zaɓi shugabancin jam’iyya na gari, wanda ke karɓar suka da amincewa da gaskiya ba tare da yaudara ba.”
Ya ƙara da cewa:
“Ina da tabbacin cewa akwai masu kwaɗayi da dama a kusa da shugaban ƙasa; suna gaya masa cewa abubuwa na tafiya daidai – amma gaskiyar magana, abubuwa ba su da kyau.”
Yadda mutuwar Buhari ta haddasa giɓi a APC
Adamu Garba ya bayyana cewa ficewar wasu ƴan APC a Arewa bayan rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ba abin mamaki ba ne.

Source: Facebook
Ya ce rasuwar tsohon shugaban ƙasar, wanda jigo ne mai mabiya sosai a Najeriya ta haifar da gibi a jam’iyyar. A cewarsa:
"A dabi’ance irin wannan rikice-rikice suna faruwa. Kuri’un nan miliyan 12 da Buhari ke samu tun kafin nasarar 2015 sun ɓace kafin ma rasuwarsa a farkon watan Yuli 2025.”
Ya ƙara da cewa:
"Buhari ya sauka daga mulki a 2023, kuma idan aka duba sakamakon zaɓen shekarar nan, APC ta samu kuri’u miliyan 5.5 kawai a Arewa. Ina miliyan 12 ɗin nan suka shiga?"
Ya ƙara da bayyana cewa duk da haka, APC ta yi nasara a zaɓen da ya gabata bisa tsarin da aka ɗora jam'iyyar a kai.
Jam'iyyar APC na shirin babban taro
A wani labarin, mun wallafa cewa jam’iyyar APC mai mulki na shirin gudanar da muhimmin taro na Kwamitin Zartaswa na Kasa (NEC) a ranar Alhamis mai zuwa.
Daga cikin abubuwan da ake sa ran za a tattauna a wajen garin akwai maganar haɗin kan jam'iyya da wanda zai zama sabon shugaban APC mai cikakken iko.
Majiyoyi sun bayyana cewa daya daga cikin dalilan kiran taron NEC shi ne don yanke hukunci kan matsayin mukaddashin shugaban, Ali Bukar Dalori.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
