Jami'an Tsaro Sun Tare Sanata Natasha, Sun Hana Ta Shiga Ofis a Majalisa

Jami'an Tsaro Sun Tare Sanata Natasha, Sun Hana Ta Shiga Ofis a Majalisa

  • Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta isa harabar Majalisar Dokoki bayan ta sanar da cewa kotu ta umarci a mayar da ita kujerarta
  • Natasha da ke wakiltar Kogi ta Tsakiya ta shiga tsaka mai wuya ne bayan majalisar dattawa ta dakatar da ita da sunan ladabtar wa
  • A martanin majalisa ga Natasha, ta ce babu umarnin kotu da ya tilasta mayar da ita, kuma ta umarce ta da kada ta yi yunkurin dawo wa yanzu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, 'yar majalisar Kogi ta Tsakiya a majalisar dattawa, ta bayyana a harabar Majalisar Dokoki ta Ƙasa a yau.

Wannan na zuwa bayan ta yi ikirarin cewa lallai za ta koma ofis, inda ta dogara da hukuncin kotu kan dakatar da ita daga majalisa.

Kara karanta wannan

ICRC ta gano babbar matsalar da ta tunkaro Arewa sakamakon ta'addanci

Sanata Natasha Akpti-Uduaghan
Sanata Natasha ta isa majalisa Hoto: Natasha H Akptoti
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito Sanata Natasha ta isa majalisa a cikin wata mota kirar SUV mai launin baƙi, tare da rakiyar wasu motocin goyon baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta shige matakin farko na binciken tsaro, amma ta fuskanci ƙalubale a ƙofa ta biyu yayin da jami'an tsaro suka hana ta shiga.

Majalisa ta ja kunnen Sanata Natasha

21st Century Chronicle ta ruwaito cewa majalisar dattawa ta yi gargaɗi ga Sanata Natasha da kada ta ƙara yunkurin komawa kujerarta da karfi da yaji.

Wannan gargaɗin na zuwa ne bayan Natasha ta sha alwashin komawa zauren majalisa a ranar Talata, bisa hukuncin Mai shari’a Binta Nyako na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja.

Shugaban majalisa, Godswill Akpabio
Jami'an tsaro sun hana Natasha shiga majalisa Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

A wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi a Abuja, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Yada Labarai, Sanata Yemi Adaramodu, ya ce babu wata hukuncin da ya tilasta a mayar da ita kujerarta.

Ya ce:

Kara karanta wannan

PDP na shirin taron NEC don duba tsarin karɓa karɓa, ta yi wa Tinubu saukale

"Majalisar Dattawan Tarayyar Najeriya na sake nanata wa, karo na uku, cewa babu wani umarnin kotu da ke wajabta mayar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kafin ƙarshen dakatarwarta."

Majalisa ta yi bayanin hukuncin kotu

Sanata Adaramodu ya kara da cewa kotun ta samu Sanata Natasha da laifin raina kotu, tare da kakabawa ta tara ₦5m da za ta biya wa gwamnatin tarayya.

Bugu da ƙari, kotun ta umarce ta da ta wallafa neman afuwa a manyan jaridu biyu da kuma a shafinta na Facebook.

Sanatan ya ce:

"Kotun dai ta bayyana karara cewa Majalisar Dattawa ba ta karya kowace doka ko tanadin kundin tsarin mulki ba a lokacin da ta ɗauki matakin ladabtarwa a kan Sanatar bisa yadda ta gudanar da kanta a zaman majalisa."

Natasha ta magantu kan kifar da gwamnati

A wani labarin, mun wallafa cewa Sanata mai wakiltar yankin Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta 'karyata zargin shirin kifar da gwamantin Bola Tinubu.

Hakazalika, Natasha ta wanke kanta daga ikirarin cewa wai ta zargi gwamnatin Tinubu da fifita kabilar Yarbawa, tana mai jaddada cewa ba ta da wata manufa ta kabilanci a mulkin 'kasar nan.

Wannan martani nata ya biyo bayan zargi daga wata mata mai suna Sandra Duru, wacce ta ce Natasha ta gaya mata cewa tana aiki don ganin bayan gwamnatin Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng