2027: Gwamnan PDP, Shugabanninta Sun ba Maraɗa Kunya, Sun Goyi bayan Tinubu a Fili
- Gwamna Ademola Adeleke da shugabannin PDP na reshen Osun sun fadi matsayarsu game da dan takarar shugaban kasa a 2027
- Gwamnan da shugabannin PDP sun goyi bayan takarar Bola Tinubu a 2027, duk da rade-radin shirin komawarsa jam’iyyar APC
- An ce taron manyan jiga-jigan PDP ya gudana a gidan gwamnati, inda suka yanke hukuncin ci gaba da zama a PDP su goyi bayan Tinubu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Osogbo, Osun - Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke ya bayyana wanda zai goyi baya a zaben shugaban kasa a 2027.
Gwamna Adeleke da shugabannin jam’iyyar PDP a jihar sun goyi bayan shugaban kasa Bola Tinubu na sake tsayawa takara a 2027.

Source: Twitter
Hakan na cikin wata sanarwa da shafin X na Gwamna Ademola Adeleke ya wallafa a yau Talata 22 ga watan Yulin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rade-radin barin Adeleke PDP zuwa APC
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Gwamna Adeleke yana shirin sauya sheka daga jam’iyyar PDP bayan ganawa da wasu shugabanni da suka ce za su bi shi.
Sai dai rahotanni sun ce manyan ‘yan APC a Osun sun ki amincewa da shigowarsa jam’iyyar, inda wasu suka zage shi a kafafen sada zumunta.
An gudanar da taron masu ruwa da tsaki a ranar Litinin a gidan gwamnati dake Oke-Fia, Osogbo, inda PDP ta yanke shawarar marawa Tinubu baya.
Wata sanarwa bayan taron ta samu sa hannun Gwamna Adeleke, mataimakinsa, Kola Adewusi, Kakakin majalisa Egbedun da tsohon gwamna Oyinlola da wasu shugabanni 24.
Matsayar PDP kan makomar Gwamna Adeleke
Sanarwar ta jaddada cewa siyasar gida da ra’ayoyin mabiyansu a ƙasa ne suka shafi wannan hukunci, kuma hakan ya zama wajibi a bi.
Sanarwar ta ce batun sauya shekar Gwamna Adeleke bai samo asali daga gare shi ba, kuma ‘yan APC sun yi masa tofin Allah-tsine a fili.

Kara karanta wannan
'Za mu iya aiki tare,' Abin da Kwankwaso ya fada bayan haduwa da Tinubu a Aso Villa
Ta ce ko da yake ‘yan PDP ba su ji daɗin maganar sauya sheka ba, amma sun yanke shawarar binsa saboda biyayya da ƙauna gare shi.

Source: Facebook
Gwamnan PDP zai goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027
Shugabannin jam’iyyar sun ce Adeleke da gwamnatinsa da PDP su ne mafi shahara da karɓuwa a Osun, ba jam’iyyar da za su koma ba.
Sanarwar ta ce:
"Saboda haka, shugabannin PDP a Osun sun yarda cewa Osun jihar Tinubu ce, don haka sun amince da shi a matsayin ɗan gida.
"Jam’iyyar PDP a Osun ta amince da sake tsayawar Gwamna Ademola Adeleke a zaben gwamna na 2026 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.
"An umurci mambobin PDP su ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar, kuma a isar da wannan matsaya zuwa ga dukan sassan jam’iyyar a jihar.
"Gwamnan jihar ya kamata ya ci gaba da aiwatar da ayyukan mulkinsa tare da bin tsarin abubuwan da ke cikin shirin ci gaban gwamnati guda biyar."
ADC ta shirya zawarcin gwamnan PDP
Kun ji cewa jam'iyyar ADC ta ce shirin ficewar Gwamna Ademola Adeleke daga PDP zuwa APC na iya ba ta damar lashe zaɓen gwamnan Osun cikin sauki.
ADC ta ce 'yan PDP masu yawa sun riga sun shiga jam'iyyarta, wasu kuma na shirin shiga saboda rashin jin daɗin yunkurin Adeleke.
Jam'iyyar hadakar na ƙoƙarin jawo gwamnoni biyar daga PDP, duk da sukar da take fuskanta daga PDP da magoya goyon bayan APC.
Asali: Legit.ng

