'Ka Yi Hankali da Ƴan Arewa': Malami Ya Ja Kunnen Tinubu kan Zaɓen 2027, Lafiyarsa
- Elijah Ayodele ya yi gargadi ga Shugaba Bola Tinubu game da wasu yan Arewa saboda zaɓen shekarar 2027 da ake tunkara
- Faston ya ce akwai wasu manyan Arewa da ke kokarin tumbuke shi a 2027 saboda matsalolin tattalin arziki da yunwa
- Babban malamin kiristan ya ce ya guji dogaro da 'yan amshin shata domin za su cutar da shi, kuma ya nemi masu tsoron Allah
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - An gargadi shugaban kasa, Bola Tinubu game da wasu yan Arewa duba da shirin zaben 2027 da ake yi.
Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church da ke Lagos, Fasto Elijah Ayodele ya ya ja kunnen Tinubu kan shirin manyan Arewa na tumbuke shi a 2027.

Source: Facebook
Fasto Ayodele ya gargadi Tinubu kan zaben 2027
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin, ya fitar a ranar Litinin da Legit.ng ta samu, Ayodele ya ce akwai aniyar cire shi.
Ya danganta hakan da manufofin tattalin arziki da kuma matsin rayuwa da ake fama da shi a Najeriya a halin yanzu.
Fasto Ayodele ya ce Tinubu da APC su guji murna da shigowar wasu sababbin ’yan siyasa zuwa jam’iyyarsu a ’yan kwanakin nan.
Ya ce:
“Manyan Arewa na shirin tumbuke Tinubu da karfi da yaji. Ya gyara manufofinsa domin farashin kaya ya yi tashin gwauron zabo.
“Ya daina tunanin cewa ya riga ya yi tazarce. Jama’a na cikin kunci, kuma ana zagin gwamnatinsa, amma bai fahimta ba.
“Mutane na yunkuri iri-iri amma yana watsi da su. Ya kalli jam’iyyar ADC fiye da zahiri, saboda suna bin hanyar da ta dace."

Source: Getty Images
Fasto Ayodele ya shawarci Tinubu kan lafiyarsa
Ayodele ya kuma gargadi Tinubu ka da ya dogara da wasu kusa da shi, saboda su ne za su haddasa masa rashin nasara.
Faston ya ce ya kamata Tinubu ya kula da lafiyarsa inda ya ce an dade ana nuna masa kiyayya amma bai sani ba, The Eagle Online ta tabbatar.
Ya kara da cewa:
“In ba a gyara ba, jam’iyyar APC za ta fadi a zabe. Sai an yi sauye-sauye sosai idan ana son nasara a 2027.”
“’Yan Najeriya ba su farin ciki, idan ya dogara da masu yabonsa, zai sha kasa. Wasu daga Arewa sun janye goyon bayansu.
“Ya kula da lafiyarsa, ya yi abin da zai sa mutane su yaba masa. Ana ƙiyayya da shi ko da bai gane hakan ba yanzu.
“Za a yaudare shi, kuma wasu gwamnoni ma ba da gaske suke yi ba. Wasu daga cikinsu ma za su fadi a tazarce.”
- Cewar Elijah Ayodele
Ya ce wadanda ke yabonsa yau su ne za su zage shi gobe, ya kamata ya kula da wanda zai zama sabon shugaban jam’iyyar APC.
'Hanyar da za a kayar da Tinubu' - Ayodele
A wani labari mai kama da wannan, Fasto Elijah Ayodele ya bayyana dabarun da ya kamata ƴan adawa su yi idan suna son kayar da jam'iyya mai mulki.

Kara karanta wannan
Batan maciji ya birkita ƴan Kano, Sanusi II ya roƙi kwamishinan ƴan sanda alfarma
Limamin cocin ya faɗi dabarun ne a lokacin da ƴan siyasa suka fara shirye-shiryen zaɓen 2027 a Najeriya.
Ayodele ya ce shugaban ƙasa, Bola Tinubu zai yi duk mai yiwuwa domin ya ci gaba da mulkin ƙasar nan har tsawon shekaru takwas.
Asali: Legit.ng

