APC Ta Ji ba Dadi bayan Jin Labarin Tinubu ba zai Samu Karbuwa ba a 2027
- PDP ta ce babu wani dan Najeriya mai kishin kasa da zai mara wa Bola Tinubu baya a 2027 saboda gazawarsa a mulki
- Jam’iyyar APC ta ce PDP na cikin mawuyacin hali, ba ta da ikon yin hukunci a siyasa ko a kan kimar dan takara
- APC ta ce Shugaba Bola Tinubu yana samun goyon bayan ’yan Najeriya masu kishin kasa da suka aminta da tsare-tsaren shi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zama abin ki a idon jama’a saboda yadda abubuwa suka tabarbare a mulkinsa.
Kakakin jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ne ya bayyana hakan a hira da manema labarai a Abuja, inda ya ce babu dan Najeriya mai kishin kasa da zai sake zabar Tinubu a 2027.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa APC ta ce PDP ta zama tamkar marar hankali da ke kwance a asibiti, don haka ba ta da ikon magana kan siyasa ko yadda ake tafiyar da kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP ta ce Tinubu ba zai yi kasuwa ba
Kakakin PDP ya bayyana cewa jam’iyyarsu ce kadai ke da karfin da za ta fitar da APC daga mulki a 2027 saboda yanda take da tushe a kowane yanki na kasa.
A cewarsa:
“PDP ce kadai jam’iyyar da za ta iya kayar da APC. Muna da goyon bayan al’umma, muna da tushe a kasa baki daya. Babu wani gari da babu ’ya’yan PDP.”

Source: Facebook
Zargin gazawar Tinubu da matsin tattali
Debo Ologunagba ya ce irin halin da al’umma ke ciki na rashin tsaro, matsin tattalin arziki da wahalhalu ya isa ya hana kowa sake zabar Tinubu.
Vanguard ta wallafa cewa ya kara da cewa:
“Babu wani mutum ko kungiya da ke fama da irin wadannan matsaloli da za su sake jefa kuri’arsu ga Tinubu. Shugaba Tinubu zai yi kwantai a kasuwa.’”
Martanin APC: 'PDP ba ta da kima a siyasa'
Daraktan yada labarai na APC na kasa, Bala Ibrahim, ya ce PDP ba ta da wata kima a yanzu, domin tana cikin ICU ne kamar maras lafiya mai fama da tabin hankali.
A cewarsa:
“Wanda ba shi da hankali ba ya da hurumin magana. PDP tana cikin dakin ICU, don haka ba ta da hurumin tantance lafiyar wasu ko kimarsu a kasuwa.”
'Tinubu na samun goyon baya' – APC
Bala Ibrahim ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana samun goyon bayan ’yan Najeriya masu kishin kasa saboda irin gyare-gyaren da ya kawo a fannin mulki.
Ya ce:
“Shugabanmu Bola Ahmed Tinubu ya kawo sauyi a jam’iyyar APC, kuma ya sake gina hadin kai.”
2027: Tinubu ya gana da Kwankwaso a Aso Villa
A wani rahoton, kun ji cewa jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da shugaba Bola Tinubu.
Rahotanni sun bayyana cewa Kwankwaso ya ce zai iya aiki tare da shugaban kasar duk da cewa bai yi karin haske kan maganar ba.
Madugun NNPP ya hadu da shugaba Bola Tinubu ne jim kadan bayan kammala taron tattali da aka shirya a fadar shugaban kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


