PDP na Shirin Taron NEC don Duba Tsarin Karɓa karɓa, Ta Yi wa Tinubu Saukale
- Jam’iyyar PDP za ta gudanar da taron NEC daga 23 zuwa 25 ga Yuli 2025 domin karɓar rahoton tsarin karɓa-karɓa da shirin babban taron kasa
- Wannan na zuwa ne a lokacin da APC ta sanar da shirin gudanar da babban taronta domin duba batun shugabancin jam'iyya na kasa
- PDP ta caccaki gwamnatin APC da shugaban kasa Bola Tinubu, tana cewa kuncin rayuwa da rashin tsaro sun sanya ba za ta koma jagoranci ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Kwamitin Zartaswa na Kasa (NEC) na babbar jam’iyyar adawa ta PDP na shirin gudanar da taronta a makon nan.
Ana sa ran kwamitin zai karɓi rahoton kwamitin tsarin karba-karba da shirin babban taron jam’iyyar na kasa.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a yayin taron NEC na jam’iyyar na 100 da aka gudanar a ranar 30 ga Yuni, an amince da sake haduwa tsakanin ranar 23 zuwa 25 ga watan Yuli.
PDP za ta duba tsarin karba-karba
Trust Radio ta ruwaito cewa mai magana da yawun jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya bayyana cewa shiri ya yi nisa wajen tabbatar da cewa an gudanar da taron a cikin nasara.
A cewarsa:
“Taron NEC da aka shirya tsakanin 23 zuwa 25 ga Yuli zai karɓi sababbin bayanai daga kwamitin duba tsarin karba-karba da na babban taron kasa, musamman game da shirin gudanarwa, wakilcin jihohi da sauran shirye-shiryen jam’iyya."
“NEC zai kuma tabbatar da sakamakon zabukan jam’iyya da aka kammala a wasu jihohi da kananan hukumomi. Wadannan tsare-tsaren tuni NWC ta duba su, kuma za a gabatar da su domin amincewa da su bisa ka’ida.”
PDP ta caccaki gwamnatin APC
Jam’iyyar PDP ta soki gwamnati a kan halin kuncin rayuwa da ake fama da shi a ƙasar, ta ce duk wani ɗan takarar APC da za a tsayar a 2027 ba zai kai labari ba.
Ologunagba ya ce PDP na da isasshen goyon baya, yawan magoya baya da karfin da zai sauke APC daga mulki a 2027.
A cewarsa:
“PDP ce kadai jam’iyyar da za ta iya cire APC daga mulki. Muna da karfi a kasa baki daya. Babu wata unguwa ko gari da babu 'yan PDP, domin jam’iyyar jama’a ce gaske. ’Yan Najeriya na bukatar dawowar PDP.”

Source: Facebook
Ya ce ko da yake an samu masu sauya sheka a baya-bayan nan, hakan ba wani abu ba ne, kuma ba zai girgiza PDP ba.
PDP ta yi wa Bola Tinubu kaca-kaca
A baya, kun ji cewa jam’iyyar adawa ta PDP ta sake caccakar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, tana mai cewa bai cancanci sake samun goyon bayan ƴan Najeriya a zaɓen 2027 ba.
Jam’iyyar ta bayyana cewa Tinubu ya gaza, kuma bai dace a kira shi da matsayin zaɓi ga al’ummar ƙasa ba, yayin da ake tunkarar babban zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.
Mai magana da yawun PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, ne ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a Abuja a ranar Litinin, inda ya ce jam'iyyarsa ce kawai za ta kawar da APC.
Asali: Legit.ng


