APC Ta Sanya Ranar Gudanar da Babban Taro, Ana Neman Magajin Ganduje

APC Ta Sanya Ranar Gudanar da Babban Taro, Ana Neman Magajin Ganduje

  • Hankalin jam'iyya mai mulki ta APC ya koma kan tunkarar wasu daga cikin manyan kalubalen da suka tunkaro ta
  • Rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka ana shirin gudanar da babban taron jam'iyya domin duba wasu daga cikin matsalolin
  • Daya daga cikin abubuwan da ake sa ran zai dauki hankali a yayin taron har da wanda za a zaba ya maye gurbin Abdullahi Ganduje

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Ana sa ran Kwamitin Zartaswa na Kasa (NEC) na jam’iyyar APC mai mulki zai gudanar da taronsa a babban birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis mai zuwa.

Taron zai tattauna a kan wadansu batutuwa da ke kokarin barazana ga hadin kan jam'iyyar, daga ciki har da batun magajin tsohon shugaban jam'iyya, Abdullahi Umar Ganduje.

Kara karanta wannan

Taron APC: Tinubu ya shiga tsaka mai wuya game da zakulo magajin Ganduje

Abdullahi Umar Ganduje, Bola Ahmed Tinubu
APC za ta gudanar da babban taro Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje/Bayo Onanuga
Source: Facebook

Majiyoyi masu tushe daga sakatariyar APC na kasa da ke Abuja sun shaida wa Daily Trust cewa babban batu da zai dauki hankali a taron shi ne batun shugabancin jam’iyyar.

Jam'iyyar APC na shirin babban taro

Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa babban dalilin kiran taron NEC shi ne domin yanke hukunci game da makomar mukaddashin shugaban APC, Ali Dalori da sauran 'yan Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC).

Wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar sun bayyana cewa ana sa ran NEC zai tabbatar da matsayin Dalori tare da ba shi wa’adin shirya babban taron zabe na kasa.

Mukaddashin shugaban APC na kasa
APC za ta fara dubo magajin Abdullahi Umar Ganduje Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Wannan taro dai zai bai wa jam’iyya damar zaben sabon shugaban jam’iyya mai cikakken iko, duk da cewa wasu na ganin cewa shugaban kasa Bola Tinubu ne zai bayyana sabon shugaban jam’iyyar a taron.

Kwamitin APC ya zauna da Tinubu

Kafin taron NEC, 'yan kwamitin gudanarwa na APC sun yi taro na sirri da ya dauki tsawon sa’o’i biyu a ranar Litinin da shugaba Tinubu.

Kara karanta wannan

An gano dalilin Ganduje na rashin tarbar Tinubu a Kano

Sai dai babu wani bayani da aka fitar dangane da abin da aka tattauna a wajen taron, kuma ba a gudanar da wani taron manema labarai ba bayan taron.

A cewarsa:

“Za a gudanar da taron kamar yadda aka tsara, amma ba mu san irin siyasar da shugaban kasa da sauran jiga-jigan jam’iyyar za su buga ba.
“Sai dai a matakin NWC, jadawadin zai kunshi batun sauyin shugabanci a jam’iyya, babban taron zabe, tarukan kasa da kuma rajistar sababbin 'yan jam'iyya."

Kwankwaso zai yi aiki ga gwamnatin APC

A baya, mun wallafa cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi ganawar sirri da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Wannan ganawa ta faru ne a ranar Litinin, bayan Kwankwaso ya bayyana a wajen wani taro da aka gudanar a Aso Villa, inda daga baya ya bayyana cewa yiwuwar aiki tare da gwamnatin.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan shi ne karo na biyu da shugaba Tinubu da Kwankwaso suka gana a cikin fiye da shekara biyu da ta gabata, tun bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng