Ana Maganar Takarar Pantami, Gwamna Inuwa Ya Yi Tsokaci kan Magajinsa a Gombe
- Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya ce addu’a ta fi komai yayin da ake ta rade-radin wanda zai gaje shi a 2027 a Gombe
- Ya ce bai kamata a gaggauta batun magaji ba, domin Allah ne ke ba da shugabanci, amma yana fatan samun wanda zai gaje shi
- Dangane da dokar hana babura da dare, Inuwa ya ce gwamnati za ta samar da bas-bas don saukaka sufuri daga ƙarfe 7:00 na dare
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - Yayin aka fara buga gangar siyasar 2027 a wasu wurare a fadin Najeriya, ana cigaba da maganar takarar gwamna a Gombe.
Yan siyasa da dama sun nuna kwadayinsu game da takarar gwamnan jihar duk da ba su bayyana ba a hukumance.

Source: Twitter
Gwamna Inuwa ya magantu game da magajinsa
A wani bidiyo da sakataren yada labaran gwamnan Gombe ya wallafa a Facebook, Gwamnan Inuwa Yahaya ya yi tsokaci kan haka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon da aka yi hira da shi ma musamman da Isma'ila Uba Misilli ya wallafa, Inuwa ya shawarci mutane kan lamarin.
Inuwa ya ce a kullum fatansa shi ne samun magaji na gari inda ya bukaci a yi ta addu'a kawai.
A yayin hirar a daren jiya Litinin 21 ga watan Yulin 2025, Gwamna Inuwa ya ce zai yi iya kokarinsa domin ganin ya samu magaji na kwarai.
Ya ce:
"Zan yi kokari na a matsayin dan Adam, kuma a yi addu'a."
Da aka tambaye shi ko ya hango maganinsa yayin da ake ta shirye-shiryen zaben 2027 a wasu wurare? Sai ya ce:
"To ai wannan Allah ne mai kawo shi, amma ina addu'a Allah ya ba mu magari, Allah kuma ya haɗa mu da wanda zai yi abin da ya kamata.
"Domin duk yadda zan so abin da nake gani ko wanda aka yi kafin ni ba zan so na ga ya lalace ba.
"Cigaban jihar Gomben nan ya kamata ya zama shi ne a kan gaba ba biyan buƙata ta ko bukatar wani shi kadai ba."

Source: Facebook
Zirga-zirgar babura: Inuwa ya yi maganar dokar
Yan jarida sun sake tambayarsa shin ko babu wani wanda yake ji a jikinsa yake son ya gaje shi, sai Inuwa ya ce:
"To ai kwana ɗaya ma a siyasa wani abu ne bare shekara guda da wani abu, ina ga gaggawa ne na wadanda suke hango dala amma ai har yanzu da dan saura."
Gwamna Inuwa ya kuma tabo batun hana zirga-zirgar babura da dare da aka sanya daga karfe 7:00 na dare zuwa 6:00 na safe.
Mafi yawan mazauna garin Gombe na tsammanin gwamnan zai yi amfani da wannan dama domin dage dokar ko sassauta ta amma sai aka samu akasin haka.
Inuwa ya ce za a samar da bas bas a cikin gari daga ƙarfe 7:00 na dare domin kawo sauki ga al'umma ta fannin sufuri.
Pantami ya yi magana kan takara a 2027
Mun ba ku labarin cewa tsohon minista, Isa Ali Pantami ya bayyana cewa zai sanar da matsayarsa kan fitowa takarar gwamnan jihar Gombe.
Farfesa Pantami ya tabbatar da cewa mutane da yawa sun biyo ta hanyoyin daban-daban suna rokon ya fito takara.
Pantami ya ce saura kaɗan ya kammala tuntuɓa da neman shawari, inda ya roki ƴan Najeriya su sanya shi a addu'a.
Asali: Legit.ng


