Bayan Rasuwar Buhari, Sheikh Pantami Ya Yi Magana kan Takarar da Ake So Ya Nema a 2027

Bayan Rasuwar Buhari, Sheikh Pantami Ya Yi Magana kan Takarar da Ake So Ya Nema a 2027

  • Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana cewa zai sanar da matsayarsa kan fitowa takarar gwamnan jihar Gombe idan lokaci ya yi
  • Tsohon ministan sadarwa ya tabbatar da cewa mutane da yawa sun biyo ta hanyoyin daban-daban suna rokon ya fito takara
  • Pantami ya ce saura kaɗan ya kammala tuntuɓa da neman shawari, inda ya roki ƴan Najeriya su sanya shi a addu'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe - Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami ya ce idan lokaci ya yi zai bayyana matsayar da ya ɗauka kan fitowa takara a 2027.

Pantami, ɗaya daga cikin manyan malaman addinin musulunci a Najeriya ya tabbatar da cewa jama'a na ta kiraye-kiraye da rokon ya nemi kujerar gwamnan Gombe a 2027.

Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Pantami.
Pantami ya ce zai faɗi shawarar da ya yanke kan yiwuwar neman takarar gwamnan Gombe idan lokaci ya yi Hoto: Prof. Isah Ali Pantami
Source: Facebook

A wata hira da aka yi da shi wacce Abdul'aziz Abdullahi ya wallafa a shafin Facebook, Farfesa Pantami ya ce ya kusa gama tuntuɓa da neman shawarwari.

Kara karanta wannan

'Ya yi mani albishir zan yi tazarce,' Tinubu ya fadi wanda ya taimaka ya zama shugaban kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2027: Yadda ake rokon Pantami ya fito takara

A cewarsa, mutane da yawa sun je har gida sun same shi, wasu kuma sun sa manya sun masa magana kan ya nemi zama gwamnan jihar Gombe a zaɓen 2027.

Tsohon ministan ya bayyana cewa zuwa yanzu ya gama tuntuɓar waɗanda ya kamata kan lamarin da kusan kashi 97% kuma ya sha alwashin bayyana matsayarsa idan lokaci ya yi.

Malam Pantami ya ce a yanzu hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta watau INEC ba ta buɗe fagen fara siyasar 2027 ba.

Pantami zai nemi gwamnan Gombe a 2027?

Da aka tambaye shi ko zai nemi takarar gwamnan Gombe kamar yadda jama'a ke ta kiran ya yi, Sheikh Pantami ya ce:

"Wannan kiraye-kiraye (na neman ya fito takara) sun fi shekara ɗaya da rabi ana yi, wasu da dama sun zo gida sun same ni, wasu sun samu waɗanda suke na gaba gare ni.

Kara karanta wannan

Gwamnan Katsina Dikko Radda ya yi bayani daga asibiti bayan haɗarin mota

"To Alhamdulillahi, mun gama neman shawarwari da kashi 97% na abin da za mu yi, idan lokacin da INEC ta sa dokar bayyana manufa za a ji manufar ta mu.
"Kowane abu akwai doka da aka saka kuma mu masu bin doka ne, duk wanda ka ji ya fito a yanzu ya ce yana takara to wataƙila bai karanta dokokin da akw da su a Najeriya ba ne.
Sheikh Isa Pantami.
Malam Pantami ya roki ƴan Najeriya su sanya shi a addu'a kan batun takarar gwamnan Gombe Hoto: Prof. Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Sheikh Pantami ya nemi addu'ar ƴan Najeriya

A ƙarshe, Farfesa Isah Pantami ya bayyana cewa idan lokacin da doka ta tanada na bayyana manufar tsayawa takara ya yi, zai fito ya faɗawa mutane matsayarsa.

Ƙafin lokacin, Pantami ya roki ƴan Najeriya da su sanya shi a cikin addu'a Allah Ya zaɓa abin da ya fi zama alheri domin ba gudu ba ja da baya.

Pantami ya ba wani mutumi kyautar N200,000

A wani labarin, kun ji cewa Farfesa Pantami ya bai wa wani mutumi kyautar N200,000 saboda ya yiwa marigayi Muhammadu Buhari takwara.

Mutumin ɗan asalin jihar Bauchi ya rangaɗawa ɗansa sunan Muhammadu Buhari domin girmama tsohon shugaban ƙasar bayan ya koma ga Allah.

Malam Danladi Mai Kaset ya bayyana cewa yana ɗaya daga cikin masu alfahari da irin gwagwarmayar da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262