PDP Ta Yi Rashi, Tsohon Daraktan Kungiyar Gwamnoni Ya Koma ADC

PDP Ta Yi Rashi, Tsohon Daraktan Kungiyar Gwamnoni Ya Koma ADC

  • Tsohon babban jigo a PDP, C.I.D. Maduabum, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar saboda wasu dalilansa
  • Daga cikin abin da ya ce ya kore shi daga PDP akwai kauce wa turbar da ake kai da kuma hana jama'a faɗin gaskiya
  • Maduabum ya sanar da koma wa ADC da ya bayyana da cewa tana cike da masu kishin ƙasa, gaskiya da riƙon amana

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – C.I.D. Maduabum, tsohon babban daraktan kungiyar gwamnonin PDP, kuma tsohon dan majalisar wakilai, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyya.

Sauya shekar na daga cikin ire-irenta da PDP ke fuskanta tun bayan da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Yadda yan PDP ke rokon Kwankwaso, Abba su sauya sheka a Kano

PDP ta kara rasa jigonta
Jigo a PDP ya sauya sheka Hoto: @OffcialPDPNig/Atiku Abubakar
Source: UGC

Jaridar The Cable ta wallafa cewa Maduabum ya bayyana ficewarsa ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maduabum ya bar PDP

Channels ta wallafa cewa Maduabum ya ce ya bar PDP saboda jam’iyyar ta ɗauki wata hanya ta daban da ta saɓa da tafarkin da ake kai a baya.

Ya ce a yanzu, PDP ba ta da karsashi, sannan ta tsunduma a cikin rikice-rikicen cikin gida da suka hana ta ci gaban da ake buƙata.

Alamar jam'iyyar adawa ta ADC
Jigon PDP ya koma ADC Hoto: ADC Coalition
Source: Twitter

Sanarwar ta ƙara da cewa:

"A PDP yanzu, ana korar masu faɗa wa jam'iyya gaskiya, ana kuma ƙaƙaba wa masu son yin gyara takunkumi."

Ya kara da cewa bai jin daɗi a zuciyarsa kuma yana fuskantar rashin kwanciyar hankali a wajen ci gaba da zama a cikin jam’iyyar.

Jigon PDP ya koma ADC

Maduabum ya ce ya yanke shawarar komawa ADC ne saboda yadda jama'a ke ƙara amincewa da ita a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Zai dawo': PDP ta yi watsi da ficewar Atiku, ta faɗi babban abin da zai dawo da shi

Ya bayyana cewa alamu sun nuna ADC ta mayar da hankali kan gaskiya, rikon amana, da shugabanci nagari.

Ya ce ADC na ba da dama wajen sake gina kasa bisa jagorancin da ke da nagarta da kula da jama’a.

A kalamansa:

"Na shiga ADC ba don sauya sheka kawai ba, amma a matsayin mai kishin gyara."

Ya kuma bayyana cewa ADC na da mutane masu manufa irin su Mista Peter Obi, yana mai kira ga duk ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su goyi bayan jam’iyyar.

Maduabum ya bayyana cewa zai ci gaba da yin aiki domin adalci, daidaito da yi wa al’umma hidima.

Atiku ya fara samun matsala a ADC

A baya, mun wallafa cewa Dumebi Kachikwu, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC a zaɓen 2023, ya ce akwai wata alaƙa tsakanin Atiku Abubakar da Kudu.

Ya yi zargin cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da ya ƙullaci ƴan Kudi, kuma baya son ganin suna shugabantar Najeriya.

Ya ce tun a 2003, Atiku ya yi ƙoƙarin hana shugabanci ya ci gaba da kasancewa a Kudancin Najeriya, inda ya ƙalubalanci tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng