Gwamnan Taraba Na Shirin Barin PDP zuwa ADC, Hadiminsa Ya Tsage Gaskiya
- An yaɗa wasu rahotanni a kafafen sada zumunta masu cewa gwamnan Taraba, Agbu Ƙefas na shirin barin PDP zuwa jam'iyyar ADC
- Gwamnatin jihar ta fito ta musanta jita-jitar cewa Gwamna Kefas na shirin barin PDP wacce ya lashe zaɓe a ƙarƙashinta
- Hadiminsa ya bayyana cewa gwamnan zai ci gaba da zama daram a PDP kuma biyayyarsa ba za ta yanke ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Taraba - Gwamnatin jihar Taraba, ta yi magana kan jita-jitar cewa Gwamna Agbu Kefas na shirin barin jam'iyyar PDP zuwa ADC.
Gwamnatin Taraba ta ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa Gwamna Agbu Kefas yana shirin komawa wata jam’iyya.

Source: Facebook
Mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da sadarwar zamani, Emmanuel Bello, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana iƙirarin a matsayin maras tushe kuma wanda yake cike da yaudara.
An yaɗa jita-jita kan Gwamna kefas
Cece-kuce ya ɓarke ne bayan da aka yaɗa hotunan wani shirin tallafawa al’umma da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Bali/Gassol, Jafaru Chiroma, ya shirya.
A cikin hotunan, an ga hoton gwamnan tare da harafin “ADC,” wanda hakan ya haifar da jita-jitar cewa wataƙila yana shirin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar.
Me gwamnati ta ce kan shirin barin PDP zuwa ADC
Emmamuel Bello ya ce Gwamna Agbu Kefas yana nan daram a cikin jam’iyyar PDP.
“A matsayinsa na tsohon shugaban PDP a matakin jiha, ya ci gaba da kula da cigaban jam’iyyar da haɗin kanta a jihar Taraba. Biyayyarsa ga jam’iyya ba ta taɓa kasancewa cikin shakka ba."
- Emmanuel Bello
Ya ƙara da cewa gwamnan yana mayar da hankali kan cika alƙawuran da ya ɗauka, kuma bai damu da jita-jita kan siyasar ƙasa ba.
“Hadin gwiwarsa da gwamnatin tarayya ƙarƙashin shugabancin Shugaba Bola Tinubu ba don wata manufa ta siyasa ba ce, sai don tabbatar da kyakkyawan mulki da kawo fa’idar dimokuraɗiyya ga mutanen Taraba."
- Emmanuel Bello
Meyasa aka ga Gwamna Kefas da ADC?
Da yake fayyace rikicin da ya ɓulla kan harafin “ADC” da aka gani a wurin taron, Emmanuel Bello ya bayyana cewa kalmar ba ta da alaƙa da jam’iyyar ADC illa dai sunan laƙabi ne da ake kiran Hon. Chiroma da shi.

Source: Twitter
"An fi sanin Hon. Chiroma da laƙabin ‘ADC’, wanda ya samo asali ne daga tsohon muƙaminsa na dogarin Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal lokacin da ya kasance kakakin majalisar wakilai sannan daga bisani gwamnan jihar Sokoto."
A cewar Emmanuel Bello, shugaban PDP na jihar Taraba, Alhaji Abubakar Bawa, ne ya wakilci Gwamna Kefas a wurin taron, kuma wurin taron ya cika da tutoci da allunan jam’iyyar PDP.
Mai taimakawa gwamnan ya bukaci jama’a da su yi watsi da jita-jitar, yana jaddada cewa Gwamna Agbu Kefas na nan daram da PDP.
Sanatan PDP ya fice daga jam'iyyar
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Osun ta samu naƙasu bayan ficewar ɗsya daga cikkn sanatocinta.

Kara karanta wannan
Ficewar Atiku Abubakar daga PDP ta girgiza siyasar Najeriya, gwamnoni sun fara magana
Sanata Francis Adenigba Fadahunsi wanda ke wakiltar Osun ta Gabas a majalisar dattawa ya yi murabus daga PDP.
Ya bayyana cewa rigingimun shari'a da suka addabi jam'iyyar na ɗaya daga cikin dalilan da suka sanya ya rabu da ita.
Asali: Legit.ng

