Binani: Tsohuwar 'Yar Takarar Gwamna Ta Watsar da APC, Ta Koma Jam'iyyar ADC
- Jam'iyyar APC mai adawa a jihar Adamawa ta gamu da koma baya yayin da ɗaya daga cikin manyan ƙusoshinta ta fice daga cikinta
- Sanata Aishatu Dahiru Binani ta raba gari da jam'iyyar APC wacce ta yi takarar gwamnan jihar Adamawa a ƙarƙashinta a zaɓen 2023
- Bayan barin APC, Sanata Binani ta shiga jam'iyyar haɗaka ta ADC, inda ta ce za su yi tafiya a cikinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Adamawa - Jam'iyyar haɗaka ta ADC ta samu ƙaruwa bayan shigowar Sanata Aishatu Dahiru Binani cikinta.
Ƴar takarar gwamnan a jihar Adamawa a zaɓen shekarar 2023, Sanata Aishatu Dahiru Binani, ta yanki katin jam'iyyar haɗakar ƴan adawa ta ADC.

Source: Facebook
Jaridar BBC Hausa ta kawo rahoto kan sauya sheƙar tsohuwar ƴar takarar gwamnan zuwa jam'iyyar ADC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A zaɓen shekarar 2023, Sanata Binani ta fafata takarar gwamnan jihar Adamawa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC.
Sanata Binani ta zo ta biyu a zaɓen bayan da ta yi rashin nasara a hannun Gwamna Ahmadu Fintiri na jam'iyyar PDP.
A lokacin da ake ta shirin kafa haɗakar ƴan adawa, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya taɓa sanya labule da Sanata Binani.
Atiku ya gana da Sanata Binani
Atiku Abubakar ya ziyarci Sanata Binani ne a gidanta da ke babban birnin tarayya Abuja.
Sai dai, Sanata Binani da Atiku Abubakar ba su yi magana kan dalilin tattaunawar da suka yi ba.
Sanata Binani dai na fuskantar barazana a siyasar jihar Adamawa bayan da abokin hamayyarta Nuhu Ribadu, ya zama mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro.
Ana ganin cewa dai Binani za ta sake jaraba sa'arta wajen neman takarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen shekarar 2027 da ake tunkara.
Sanata Binani ta koma jam'iyyar ADC
An hango tsohowar sanatar wadda ta wakilci Adamawa ta Tsakiya a majalisar dattawa tana bayanin nuna goyon bayanta ga ADC.

Source: UGC
A cikin bidiyon dai, Sanata Binani tana zagaye da matasa yayin da take yin jawabin na ta.

Kara karanta wannan
Sauya sheƙar Atiku ta rikita PDP da APC, tsofaffin gwamnoni da jiga jigai sun bi sahunsa
"Mu mun ɗauki jam'iyyar ADC kuma za mu yi tafiya a cikinta. Muna roƙon Allah ya taimake mu ya raba mu da mutanen da muke tafiya da su amma suna gurɓata jam'iyya."
- Sanata Aishatu Dahiru Binani
Bayan da sanatar ta kammala jawabin na ta ne, aka ganta ɗauke da katin jam'iyyar ADC cikin wasu hotuna.
Sanatan PDP ya fice daga jam'iyyar
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta rasa ɗaya cikin sanatocin da take da su a jihar Osun da ke yake yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.
Sanata Francis Adenigba Fadahunsi wanda ke wakiltar mazaɓar Osun ta Gabas a majalisar dattawa ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP.
Ya bayyana cewa ya yanke shawarar ficewa daga PDP ne saboda saɓanin da take fama da shi da kuma rigingimun shari'a da suka ƙi ƙarewa.
Asali: Legit.ng
