"An Yi Abin Kunya," ADC Ta Tona Abin da Gwamnatin Tinubu Ta Yi a Rasuwar Buhari

"An Yi Abin Kunya," ADC Ta Tona Abin da Gwamnatin Tinubu Ta Yi a Rasuwar Buhari

  • Jam'iyyar haɗaka ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da sanya siyasa a rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari
  • Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi ya ce gwamnati mai ci ta yi amfani da rasuwar Buhari wajen neman tausayawar ƴan Arewa
  • Ya ce abin kunya ne yadda aka tilasta wa Yusuf Buhari yin godiya a gaban kamara da sunan taron FEC na karrama mahaifinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Jam’iyyar haɗaka watau ADC ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da sanya siyasa a jana'izar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a Landan

ADC ta zargi gwamnati mai ci da amfani da rasuwar Muhammadu Buhari wajen ƙoƙarin ɓoye wanke kanta a wurin ƴan Najeriya.

Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi.
Jam'iyyar ADC ta caccaki gwamnatin Tinubu kan rasuwar Buhari Hoto: @BolajiADC
Source: Twitter

Mai magana da yawun ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi ne ya yi wannan zargin a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X jiya Juma'a.

Kara karanta wannan

Buhari, Sheikh Abubakar Gumi da wasu jagororin Najeriya 5 da suka rasu a birnin Landan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana taron girmamawa da Majalisar Zartaswa ta Tarayya (FEC) ta gudanar domin karrama Buhari a matsayin “wasan kwaikwayon siyasa.”

Buhari: ADC ta caccaki gwamnatin Tinubu

Bolaji Abdullahi ya ce taron FEC na tunawa da Buhari ba komai ba ne face wata dabarar siyasa ta ƙoƙarin ɗauke hankulan ƴan ƙasa daga ainihin abin ke faruwa.

Ya ce Yusuf Buhari, ɗan marigayin tsohon shugaban ƙasa, “an tilasta masa bayyana godiya a gaban kyamarori.”

Abdullahi ya bayyana cewa irin wannan gwamnati da ta shafe sama da shekara guda tana zargin Buhari da jefa Najeriya cikin matsin tattalin arziki, ita ce ta dawo tana jingina kanta da shi bayan ya rasu saboda siyasa.

ADC ta fallasa manufar gwamnatin Tinubu

"Tun farko wannan gwamnatin ta nesanta kanta daga manufofin Buhari musamman dangane da cire tallafin man fetur, tattalin arziki da harkokin shugabanci."
“Yanzu kuma saboda rashin kunya tana ƙoƙarin juyawa ta jingina kanta da mutumin da ta shafe watanni tana cin mutuncinsa.”

Kara karanta wannan

"Kamar ya sani," Kalaman da Buhari ya faɗa game da mutuwarsa kafin ya sauka daga mulki

“Wace irin gwamnati ce ke amfani da radadin zuciyar iyalin da suka yi rashin uba a matsayin hanyar gyaran martabar ta?”

- Bolaji Abdullahi.

ADC ta tona shirin gwamnatin Tinubu.
ADC ta zargi gwamnatin Tinubu da amfani da Yusuf Buhari wajen ɗaga martabarta a idon ƴan Arewa Hoto: @BolajiADC
Source: Twitter

ADC ta yi zargin an yi amfani da Yusuf Buhari

Mai magana da yawun ADC ya ƙara da cewa abin da ya faru a taron FEC wani ɓangare ne na shiri da gwamnati ke yi don amfani da rasuwar Buhari wajen neman tausayin Arewa da kuma magoya bayan Buhari.

"Tun farko, mun gargaɗi iyalan marigayi shugaban ƙasa game da wannan shiri. Abin da muka gani a taron FEC, somin taɓi ne kawai.
"Amfani da dansa wanda ke cikin baƙin ciki tare da tilasta masa nuna godiya a gaban kamara, abin kunya ne kuma ya kamata ƴan ƙasa su yi Allah wadai.

Dalilin Buhari na kin korar ministoci

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban ma'aikatan faɗar shugaban ƙasa, Ibrahim Gambari ya bayyana dalilin Muhammadu Buhari na ƙin korar ministoci.

Farfesa Gambari ya bayyana marigayi Buhari a matsayin mutum mai tausayi wanda ya yiwa Najeriya hidima da duk abin da ke hannunsa.

A cewarsa, Shugaba Buhari bai sallami wasu daga cikin mukarrabansa ba ne domin yana ƙaunar su kamar yadda yake ƙaunar ‘yan Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262