PDP Ta Kara Birkicewa, Babban Sanata Ya Yi Murabus daga Jam'iyyar
- Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Osun ta gamu da koma baya yayin da ɗaya daga cikin sanatocin da take da su a majalisar dattawa ya yi murabus daga cikinta
- Sanata Francis Adenigba Fadahunsi ya sanar da ficewarsa daga PDP ne a cikin wata wasiƙa da ya aikawa shugaban jam'iyyar na mazaɓarsa
- Ya zayyano dalilan da suka sanya shi ya rabu da jam'iyyar PDP wacce ya lashe zaɓen sanarta a 2023 domin wakiltar Osun ta Gabas a majalisar dattawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Osun - Jam'iyyar PDP ta samu naƙasu a jihar Osun bayan ficewar ɗaya daga cikin sanatocinta.
Sanata Francis Fadahunsi wanda yake wakiltar Osun ta Gabas a majalisar dattawa ya yi murabus daga jam’iyyar PDP mai mulki a jihar Osun.

Source: Twitter
Jaridar The Nation ta rahoto cewa sanatan ya yi murabus daga PDP ne a cikin wata wasiƙa da ya rubuta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan PDP ya fice daga jam'iyya a Osun
Wasiƙar da sanatan ya rubuta na ɗauke da kwanan watan 12 ga watan Yulin 2025.
Francis Fadahunsi, wanda ɗan siyasa ne mai ƙarfi a Osun ta Gabas, musamman a ƙasar Ijesa, sanata ne mai ci wanda ke a wa'adi na biyu kuma ɗaya daga cikin manyan magoya bayan Gwamna Ademola Adeleke.
Sanatan ya bayyana murabus ɗinsa a cikin wata wasiƙa da aka rubuta a ranar 12 ga Yuli, 2025, wadda aka aika wa shugaban jam’iyyar PDP a gunduma ta 4, ƙaramar hukumar Obokun ta jihar Osun.
Meyasa sanatan ya fice daga PDP?
Ya danganta matakin da ya ɗauka da saɓani wanda aka gaza sulhuntawa da kuma rikice-rikicen shari’a da suka addabi jam’iyyar PDP a matakin ƙasa bayan zaɓen 2023.
"Ina so na sanar da ku a hukumance cewa na yi murabus daga kasancewata ɗan jam’iyyar PDP nan take, saboda saɓani da aka gazawa sulhuntawa da kuma rikice-rikicen shari’a da suka dabaibaye jam’iyyar a matakin ƙasa tun bayan zaɓen gama-gari na 2023."
"Na yanke wannan shawara ne bayan tuntuba da tattaunawa da abokan siyasa na, iyalina da abokai. Fatan na shine za ku karɓi murabus ɗina cikin gaskiya da amana."
- Sanata Francis Adenigba Fadahunsi

Source: Original
Sanatan dai bai bayyana jam'iyyar da zai koma ba bayan ya tattara ƴan komatsansa daga PDP.
Ficewar Sanata Francis dai na zuwa ne yayin da ake ta magana kan shirin Gwamna Ademola Adeleke na sauya sheƙa daga PDP zuwa jam'iyyar APC.
PDP na zawarcin Peter Obi
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta fara zawarcin tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, zuwa cikinta.
Mataimakin sakataren yaɗa labarai na ƙasa na PDP, Ibrahim Abdullahi, ya bayyana cewa PDP na son sake yin aiki tare da Peter Obi.
Ya bayyana tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan na LP a zaɓen 2023 a matsayin babban jari na siyasa wanda zai iya taimakawa PDP lashe zaɓe, idan har ya yarda ya dawo cikinta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

