"Nan ba da Jimawa ba," Wasu Gwamnonin Adawa Sun Shirya Sauya Sheƙa zuwa APC
- Jam'iyyar APC ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba, wasu gwamnonin adawa a Najeriya za su sauya sheƙa zuwa cikinta gabanin zaɓen 2027
- Sakataren APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru ya faɗi hakan a wurin wani taron horarwa da jam'iyyar ta shirya a Abuja ranar Juma'a
- Ya ce a yanzu APC na da gwamnoni 23 amma akwai wasu da dama da suka nuna sha'awar shiga cikinta nan ba da daɗewa ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ga dukkan alamu guguwar sauya sheƙa ta manyan ‘yan siyasa zuwa jam’iyyar APC mai mulki na iya ƙaruwa gabanin zaɓen 2027.
Jam’iyyar APC, a ranar Juma’a, ta bayyana cewa wasu gwamnoni adawa a ƙasar nan sun shirya sauya sheƙa zuwa inuwarta nan ba da jimawa ba.

Source: Twitter
Sakataren APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru ne ya bayyana hakan a wani taron kwana guda da jam'iyyar ta shirya a Abuja, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Bayan tafiyar Atiku, PDP ta bayyana shirinta na dawo da Peter Obi cikin jam'iyyar
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An shirya wannan taro ne domin horar da sakatarorin yaɗa labarai na jam’iyyar APC daga matakan jihohi da na yankuna a faɗin Najeriya.
2027: APC ta soki wasu halayen ƴan adawa
Da yake jawabi a wurin taron, Sanata Basiru ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda wasu 'yan adawa ke amfani da ƙarya, ƙabilanci da addini a matsayin makamai na yaƙin neman zaɓe tun kafin zaɓen 2027.
“Wannan taro yana da matuƙar muhimmanci domin tun kafin zaɓen 2027, mun fara ganin yadda ake amfani da ƙarerayi da gangan a matsayin hanyar neman nasara a siyasa a Najeriya.
"Yanzu, mutane na ɗaukar hotuna daga Somalia, daga Chadi, ko daga yankunan da ke fama da yaƙi, su haɗa da adireshin Najeriya domin yaɗa ƙarya da yaudarar jama’a.
“Muna da mutanen da suka shugabanci jihohinsu amma ba su yi wani abin a-zo-a-gani ba, amma sai su dawo suna kwatanta ci gaban China ko Malaysia, da namu alhali ba su yo komai ba tsawon shekara takwas.

Kara karanta wannan
Najeriya ta yi martani ga Turkiyya kan zargin bullar sabuwar kungiyar yan ta'addan FETO
- Ajibola Basiru.
Sakataren jam'iyyar APC ya ce wannan taro yana da amfani domin fuskantar waɗanda suka mayar da ƙabilanci makami.

Source: Twitter
Waɗanne gwamnoni ne za su shiga APC?
Ya ce a yanzu APC na da gwamnoni 23 kuma akwai wasu da dama da suka nuna sha'awar suna son a ba su dama su sauya sheƙa zuwa inuwarta, rahoton Punch.
Sanata Basiru ya ƙara da cewa:
“A yanzu haka, muna da gwamnoni 23 a jam’iyyarmu ta APC, kuma akwai wasu gwamnoni da suka nuna sha’awar shigowa.
Wasu ma ba su da tasiri sosai amma suna neman shigowa. Ba zan yi cikakken bayani ba, amma muna buƙatar nuna wa duniya ayyukan da gwamnoninmu ke yi, domin mu tabbatar musu cewa ba hayaniya kawai muke ba.
Wani jigon APC a Ɗanja, jihar Katsina, Usman Kabir ya shaidawa Legit Hausa cewa, jam'iyyarsu na aiki tukuru don ganin ta sake samun nasarori a 2027.
A cewarsa, ba ya tunanin wata haɗakar ƴan adawa za ta yi ƙarfi har ta iya kwace mulkin Najeriya.
Usman ya ce:
"Kamar yadda shugabannin mu na ƙasa ke koƙarin jawo gwamnoni da manyan jiga-jigai, mu a nan tushe muna ƙoƙarin wayar da kan ƴan ƙasa su gane inda aka dosa.
"Ƴan haɗaka a ADC ba za su kai labari ba, ina ji a jikina kafin zaɓe za su tarwatse, kwanan nan kun ji PDP na shirin dawo da Peter Obi, daga nan sai wa? Bana tunanin za su iya kai labari."
Gwamnan Osun zai sauya sheka zuwa APC?
Kuna da labarin alamu sun fara tabbatar da jita-jitar da ake yaɗawa cewa gwamnan Osun, Ademola Adeleke na shirin sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.
Mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, shi ne ya tabbatar da jita-jitar sauya sheƙar gwamnan Jihar Osun, wanda yake kawu a wurinsa.
Davido ya yi wasu baituka a sabuwar waƙarsa da ke nuna gwamnan zai rungumi APC mai alamar tsintsiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
