2027: Atiku Ya Fara Fuskantar Matsala a ADC Kwanaki Kaɗan bayan Ya Fice daga PDP

2027: Atiku Ya Fara Fuskantar Matsala a ADC Kwanaki Kaɗan bayan Ya Fice daga PDP

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya fara fuskantar tangarɗa a jam'iyyar haɗaka ADC kwanaki kaɗan bayan ya fice daga PDP
  • Ɗan takarar ADC a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, ya ce duk wannan tsalle-tsallen da Atiku ke yi da sunan haɗaka, so yake ya yaudari Peter Obi
  • Dumebi Kachikwu ya ce a tarihi, kwata-kwata Atiku ba ya ƙaunar ɗan Kudu ya karɓi kujerar shugaban ƙasa tun daga 2003 har zuwa yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar ADC a zaɓen 2023, Dumebi Kachikwu ya zargi Atiku Abubakar da ƙin jinin ɗan Kudu ya mulki Najeriya.

Kachikwu ya ce a tarihin siyasar Najeriya, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku ya daɗe yana nuna adawa da tsarin miƙa shugabanci ga ƴan Kuduncin ƙasa.

Kara karanta wannan

"Babu irin Buhari": Jigo a ADC ya gano kalubalensu wajen kifar da Tinubu a 2027

Dan takarar ADC, Dumebi Kachikwu.
Kachikwu ya zargi Atiku da nuna wa Kudu ƙiyayya wajen shugabancin ƙasa Hoto: Dumebi Kachikwu
Source: Facebook

Kamar yadda The Cable ta ruwaito, Dumebi Kachikwu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kachikwu ya dauko tarihin Atiku tun 2003

Ya ce Atiku ya yi ƙoƙarin hana tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo neman wa’adin mulki na biyu, saboda yana ganin lokacin shi ne ya kamata ya hau mulki.

Kachickwu ya ce:

"Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku mutum ne da tarihinsa ya nuna ba ya son ɗan Kudu ya shugabanci Najeriya, yana shirya wannan shirmen don amfanin kansa kawai.”

Kachikwu ya kara da cewa tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Jonathan ma ya dandana irin wannan halin na Atiku.

Ana zargin Atiku bai ƙaunar mulkin ɗan Kudu

A cewarsa, bayan shekaru takwas da marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a kan mulki, Atiku ya sake nuna halinsa na cewa shi ne zai yi takara a inuwar PDP a 2023.

Kara karanta wannan

"An karya doka," Abin da Atiku ya yi ana jimamin rasuwar Buhari ya harzuƙa Ministan Tinubu

Haka kuma, a yanzu Kachikwu ya zargi Atiku da kokarin ruɗar Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a 2023, da cewa yana da goyon bayan yawancin ƴan Arewa.

A rahoton Vanguard, jigon ADC ya ƙara da cewa:

“Yanzu haka yana amfani da wasu baragurbi don ruɗar tsohon gwamna Peter Obi cewa shi kaɗai, wato Atiku, ne zai iya lashe zaɓe saboda yana iya samun mafi yawan kuri’un Arewa.”
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Jigon ADC ya zargi da Atiku da kokarin kwace jam'iyyar daga hannunsu Hoto: @Atiku
Source: Twitter

Jigon ADC ya ƙalubalanci Atiku Abubakar

Kachikwu ya kalubalanci Atiku da ya tabbatar da adalci da gaskiya ta hanyar fitowa fili ya bayyana cewa Kudu ce ta dace da shugabancin ƙasa a 2027.

“Idan tsohon mataimakin shugaban ƙasa yana ganin abin da na faɗa ba gaskiya ba ne, kuma burinsa shi ne ceto Najeriya, to ina kalubalantarsa yau da ya fito fili ya yi adalci.
"Ya faɗawa duniya cewa Kudu ce ya kamata ta ci gaba da rike shugabancin ƙasa na tsawon shekaru shida masu zuwa."

- Dumebi Kachikwu.

Kachikwu ya ƙara da cewa jam'iyyar ADC za ta ci gaba da kasancewa jam’iyya mai maraba da kowa, amma ba za ta faɗa tarkon tsofaffin ƴan siyasa ba.

Kara karanta wannan

Ficewa daga PDP: Lokuta 5 da Atiku ya sauya jam'iyya da dalilinsa

Ciyamomin ADC a jihohi 5 sun kai ƙara kotu

A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin ADC na jihohi biyar sun maka Sanata David Mark da wasu a kotu bisa zargin kwace jam’iyyar ta bayan gida.

Masu karar sun nemi kotu ta dakatar da shirin ƴan haɗakar jam'iyyun adawa, waɗanda suke zargin suna shirin kwace ADC gaba ɗaya.

Wannan rikici na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kokarin kafa kawancen ‘yan adawa gabanin zaben 2027, wanda ADC ta zama jam'iyyar za a yi amfani da ita.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262