Hadimin Wike Ya Taso Atiku a Gaba kan Ficewa daga PDP

Hadimin Wike Ya Taso Atiku a Gaba kan Ficewa daga PDP

  • Hadimin ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya caccaki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar
  • Lere Olayinka ya caccaki Atiku ne kan matsayar da ya ɗauka ta ficewa daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya bayan shekaru kusan 10
  • Babban mai taimakawa Nyesom Wike wajen harkokin yada labarai ya zargi Atiku da rusa PDP bayan ya fice daga cikinta a shekarar 2023

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Babban mataimaki na musamman ga ministan Abuja, Nyesom Wike, kan harkokin yaɗa labarai, Lere Olayinka, ya caccaki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Lere Olayinka ya caccaki Atiku Abubakar ne kan ficewarsa daga jam’iyyar PDP mai hamayya.

Hadimin Wike ya yi kalamai kan Atiku
Hadimin Wike ya ragargaji Atiku kan ficewa daga PDP Hoto: @GovWike, @atiku
Source: Facebook

Hadimin na Wike ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da tashar Channels tv a ranar Alhamis, 17 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

Bayan tafiyar Atiku, shugaban yaƙin neman zaɓen PDP ya yi murabus daga jam'iyyar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me hadimin Wike ya ce kan Atiku?

Ya bayyana ficewar Atiku daga PDP a matsayin abin da ya fi alheri ga jam'iyyar.

A cewar Lere Olayinka, ɗan takarar shugaban ƙasan na PDP a zaɓen 2023, mutum ne mai yawan sauya jam’iyya, wanda ya mayar da kansa tamkar makami da ake amfani da shi wajen rusa PDP.

"Ra’ayina na farko? Allah ya raka taki gona. Kanun jaridu ya kamata ya kasance: ‘Atiku ya sake barin PDP’ saboda tun 2007 yake yin hakan."

- Lere Olayinka

Lere Olayinka ya kuma yi watsi da tasirin Atiku, inda ya soki yadda kafafen yaɗa labarai ke kiran Dele Momodu da sunan 'babban jigo' a PDP.

"Ta yaya wanda ya shiga jam’iyya a 2022 zai zama babban jigo? Shin Momodu zai iya lashe rumfar zaɓensa? Ɗaukar hoto da wallafa littattafai ba ya nufin ƙarfi a siyasa."

- Lere Olayinka

Ya zargi Atiku da yi wa PDP zagon ƙasa a yaƙin neman zaɓen jihar Legas a 2003 a matsayin mataimakin shugaban ƙasa, yana mai cewa Atiku ya nemi afuwa daga baya a shekarar 2018.

Kara karanta wannan

Ficewa daga PDP: Hadimin Atiku ya yi wa ministan Tinubu wankin babban bargo

“Da mun lashe Legas a wancan lokacin, tafiyar siyasar Najeriya da ta sha bamban. Amma a maimakon haka, shi ne mataimakin shugaban ƙasa na farko da ke kan kujera da ya sauya jam’iyya zuwa AC a 2007."

- Lere Olayinka

Hadimin Wike ya ragargaji Atiku
Hadimin Wike ya soki Atiku kan ficewa daga PDP Hoto: @GovWike, @atiku
Source: Facebook

An zargi Atiku da rusa jam'iyyar PDP

Olayinka ya ce ficewar Atiku zuwa jam’iyyar APC a 2014 ce ta jefa PDP cikin ruɗani, yana mai cewa:

“Yanzu ya sake barin jam’iyyar bayan kasa gyara ta. Ina mamaki, likita ne ya rubuta masa takardar neman mulki a matsayin magani? Yadda yake nemansa ido rufe ya yi yawa."

Da aka tambaye shi dangane da damar PDP a 2027, Olayinka ya amince da cewa jam’iyyar ta raunana, amma yanzu akwai damar a farfaɗo da ita.

"Jam’iyyar ta samu rauni, amma yanzu za mu iya farfado da ita ba tare da wannan matsala da ke dawowa lokaci-lokaci ba. Ko da yake 2027 ta yi kusa sosai domin murmurewa gaba ɗaya."

- Lere Olayinka

Dele Momodu ya soki Wike

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Dele Momodu, ya caccaki ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

"An karya doka," Abin da Atiku ya yi ana jimamin rasuwar Buhari ya harzuƙa Ministan Tinubu

Dele Momodu ya zargi Wike da yi wa abokan tafiyarsa na baya wulakanci don cimma muradun ƙashin kansa.

Tsohon ɗan takarar ya bayyana cewa kamfaninsa ne ya koyawa Wike yadda zai riƙa saka kaya tare yin magana a bainar jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng