Atiku ko Tinubu: Kungiya Ta Fadi Wanda Zai Gaji Kuri'un Buhari a Arewa

Atiku ko Tinubu: Kungiya Ta Fadi Wanda Zai Gaji Kuri'un Buhari a Arewa

  • Ƙungiyar Arewa Think Thank ta yi magana kan wanda zai gaji goyon bayan da Muhammadu Buhari yake da shi a Arewacin Najeriya
  • Jagoran ƙungiyar ya bayyana cewa mai girma Bola Tinubu ne zai gaji ƙuri'un da Buhari yake samu a Arewacin Najeriya
  • Hakazalika, ya kuma shugaban ƙasan kan jana'izar da ya shiryawa Muhammadu Buhari domin karrama shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wata ƙungiyar zamantakewa da siyasa daga Arewa mai suna Arewa Think Tank (ATT) ta yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ƙungiyar ATT ta yabawa Tinubu ne bisa girmamawa da ya yi wa marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta hanyar shirya masa jana’izar karramawa a garinsa na Daura, jihar Katsina.

ATT ta yabawa Tinubu kan Buhari
ATT ta ce Tinubu zai gaji kuri'un Buhari a Arewa Hoto: @MBuhari
Source: Twitter

Jaridar The Nation ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jagoran ƙungiyar, Muhammad Alhaji Yakubu, ya fitar a ranar Laraba, 16 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

Bayan suka daga 'yan Arewa, Peter Obi ya fadi dalilin rashin zuwa jana'izar Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana jana'izar da aka shirya a matsayin alamar girmamawa ta musamman ga marigayi Buhari da kuma tabbacin cewa Shugaba Tinubu na da niyyar tabbatar da haɗin kan ƙasa.

Wanene zai gaji ƙuri'un Buhari a Arewa?

Yakubu ya ce wannan abu ya ƙara jawo wa Tinubu ƙauna daga al’ummar Arewa, tare da sanya shi zama wanda zai iya gadar magoya bayan da Buhari ya samu a yankin.

Ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa kamar yadda Buhari ya samu ƙuri’u sama da miliyan 12 daga yankin Arewa a zaɓen shugaban ƙasa na 2019, Shugaba Tinubu ma na da damar samun irin wannan goyon baya, la’akari da yadda mutane ke ƙara aminta da salon mulkinsa.

"Jana’izar da aka shirya wa Buhari ba kawai girmamawa ce ga gudummawar da ya bayar ba, har ila yau alamar ƙwarin gwiwa ce ga ƙarfin shugabancin Tinubu da kuma niyyarsa ta ƙarfafa haɗin kan ƙasa."

Kara karanta wannan

Atiku da El Rufa'i sun ziyarci kabarin Buhari kwana 1 da birne shi

- Muhammad Alhaji Yakubu

Shugaba Bola Tinubu ya samu yabo

Ya kuma roƙi ƴan Najeriya da su ba Shugaba Tinubu dama ya cika alƙawurran da ya ɗauka, da kuma gina ci gaban da aka samu a lokacin mulkin Buhari, musamman a fannonin da suka shafi daidaita tattalin arziki, tsaro da mulkin dimokuraɗiyya.

Tinubu ya samu yabo kan Buhari
Kungiyar ATT ta yabi Tinubu kan jana'izar Buhari Hoto: @Mbuhari
Source: Facebook
"Mutanen Arewacin Najeriya sun yaba da wannan kyakkyawar alama da Shugaba Tinubu ya nuna, kuma tabbas za su mayar masa da ƙuri’u a nan gaba."
"Masu kaɗa ƙuri’a daga Arewa koyaushe suna goyon bayan shugabanni masu nuna ƙwazo da gaskiya wajen ciyar da ƙasa gaba."
"Daga abin da muke gani, Shugaba Tinubu na kan turbar gina ginshiƙan da waɗanda suka gabace shi suka kafa, tare da daidaita ƙasar nan da kai ta matakin ci gaba."

- Muhammad Alhaji Yakubu

Muhammad Alhaji Yakubu ya bayyana cewa za a riƙa tunawa da marigayi Buhari saboda ƙoƙarinsa wajen daidaita tattalin arziki, inganta tsaro da zurfafa tsarin dimokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

"Bai so": Buba Galadima ya fadi dalilin jawo Buhari cikin harkar siyasa

Lokutan da Atiku ya sauya sheƙa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar PDP.

Ficewarsa ta sa ya ƙara yawan lokutan da ya sauya sheƙa daga wannan jam'iyya zuwa waccan a tarihin siyasarsa.

Tun daga shekarar 1999 ne dai Atiku Abubakar ya fara sauya sheƙa daga jam'iyyar SDP zuwa PDP.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng