2027: A ƙarshe, Atiku Abubakar Ya Yi Murabus daga Jam'iyyar PDP Mai Adawa
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi murabus daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya bayan shafe shekaru a cikinta
- Atiku ya bayyana hakan a wata wasika da ya sanyawa hannu a ranar 14 ga Yuli, 2025 da ya aike ga shugabannin PDP da ke Jada a Adamawa
- Ficewar tasa na zuwa ne a lokacin da ake kokarin haɗaka a sabuwar jam’iyyar ADC kafin zaben 2027 da ake tunkara a fadin Najeriya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Rahotannin da muke samu sun tabbatar da cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bar PDP.
Wannan na zuwa ne yayin da aka ƙaddamar da jam'iyyar ADC a matsayin dandalin siyasar yan adawa domin zaben 2027.

Source: Twitter
Atiku ya rubuta takardar murabus daga PDP

Kara karanta wannan
'Zai dawo': PDP ta yi watsi da ficewar Atiku, ta faɗi babban abin da zai dawo da shi
Hakan na cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren sadarwa ta zamani, @Rasheethe ya wallafa a shafin X a yau Laraba 16 ga watan Yulin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar mai kwanan wata 14 ga watan Yulin 2025 da Atiku ya sanyawa hannu, ya yi godiya ga jam'iyyar saboda damarmaki da ta ba shi.
Ficewar na cikin wata wasika da ya aike zuwa ga shugaban jam’iyyar PDP na mazabar Jada 1 da ke karamar hukumar Jada a jihar Adamawa
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa yana da hannu a kafa wata sabuwar jam’iyyar ADC kan zaben 2027.
A cikin wasikar ficewar, Atiku Abubakar ya ce dalilin ficewarsa shi ne yadda jam’iyyar PDP ta karkata daga ainihin tsarin da aka kafa ta.

Source: Facebook
Godiya ta musamman ga PDP daga Atiku
Atiku ya nuna godiyarsa matuka bisa damarmakin da jam’iyyar ta ba shi, ciki har da zama mataimakin shugaban kasa har na tsawon wa'adi biyu.
Har ila yau, ya nuna godiya ta musamman kan damar da ya samu na takarar shugabancin kasa har sau biyu a karkashin jam’iyyar da ke adawa a Najeriya.
Ya ce:
“A matsayina na daya daga cikin wadanda suka kafa wannan jam’iyya mai daraja, abu ne mai matukar ciwo a zuciyata yanke wannan hukuncin.
“Sai dai na ga cewa dole ne in rabu da jam’iyyar saboda tafarkin da ta dauka yanzu ba ya da alaka da ginshikan da muka gina ta a kai."
Har ila yau, Atiku ya yi fatan alheri ga jam’iyyar PDP da shugabanninta a dukkan abubuwan da suka sanya a gaba
Masoyin Atiku Abubakar ya zanta da Legit Hausa
Kwamred Aliyu Kwami ya ce tun tuni ya san PDP ba wurin zaman Atiku Abubakar ba ne.
Ya ce:
"PDP ta riga ta kama hanyar durkushewa duba da yadda Wike ke cigaba da shake mata wuya."
Kwami ya shawarci jam'iyyar hadaka ta ADC da ta yi abin da ya dace domin ba nagartaccen dan takara tikiti.
Ganduje ya yi murabus daga shugabancin APC
A baya, mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyar APC ta kasa.
An maye gurbinsa da mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ali Bukar Dalori wanda zai riƙe muƙamin har zuwa lokacin babban taronta da za a yi a Disamba.
Wannan matakin ya biyo bayan matsin lamba daga yankin Arewa ta Tsakiya da kuma rikice-rikicen cikin gida da ke kara ƙaruwa inda ake zargin an tilasta Ganduje yin murabus ne.
Asali: Legit.ng

