Bayan Katoɓarar Wike, Coci Ya Ɗauki Mataki, Ya Hana Ƴan Siyasa Hawa Mimbari

Bayan Katoɓarar Wike, Coci Ya Ɗauki Mataki, Ya Hana Ƴan Siyasa Hawa Mimbari

  • Cocin Anglican ya haramta wa 'yan siyasa yin jawabi daga mimbari bayan kalaman siyasa da Nyesom Wike ya yi a Abuja
  • Sabon tsarin ya bukaci hana sake amfani da mimbari wajen yada siyasa, domin kare mutuncin coci daga son rai
  • Shugaban cocin, Henry Ndukuba, ya ce ana maraba da kowa zuwa ibada, amma dole ne a guji duk wani abu da ke da alamar siyasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Cocin Najeriya na 'Anglican Communion' ta fitar da sababbin ka’idoji dangane da karɓar ‘yan siyasa a cocin.

Cocin ya dauki mataki domin hana yan siyasa da jami’an gwamnati jawabi yayin tarukan ibada da sauran shirye-shirye.

Bayan kalaman Wike, coci ya hana yan siyasa hawa mimbari
Coci a Abuja ya sanya doka kan yan siyasa bayan kalaman Wike. Hoto: Nyesom Wike, Peter Obi.
Source: Facebook

Abin Wike ya ce a coci da ya jawo magana

Wannan na biyo bayan ce-ce-ku-ce da kalaman siyasa da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya furta a wani taron godiya, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Kungiyar Musulmi ta bayyana gwamnan da zai iya zama shugaban ƙasa a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya je cocin domin godewa Allah bisa kammala wasu ayyukan gine-gine, amma ya yi amfani da mimbarin wajen furta kalaman siyasa masu zafi.

Ya soki cocin da ce sun kusa yin “babban kuskure” a zaben 2023, ya kuma caccaki Peter Obi, yana cewa “ba zai taɓa zama shugaban kasa ba.”

Ya kuma yi tsokaci kan halin da Najeriya ke ciki kafin Bola Tinubu ya hau mulki, wanda hakan ya janyo martani daga jama’a.

An hana yan siyasa hawa mimbari

A cikin wata takarda da Henry Ndukuba ya sanya wa hannu, cocin ya ce ya yanke wannan hukunci ne a wani taron da aka yi a Enugu.

Sabon tsarin ya bayyana cewa hakan na da nufin dakile amfani da dandalin cocin wajen yada sakonnin siyasa da kare mutuncin ibada.

An kuma bukaci tabbatar da cewa cocin ya ci gaba da kasancewa wurin ibada da haɗin kai, ba wuri na rarrabuwa da rikicin siyasa ba.

Kara karanta wannan

'APC, PDP, ADC, duk ɗaya ne': Shettima ya tura saƙo ga ƴan adawa ana batun haɗaka

Kalaman Wike sun jawo kakabawa yan siyasa dokar hawa mimbari
Coci ya haramtawa yan siyasa hawa mimbari bayan kalaman Wike. Hoto: Nyesom Wike.
Source: Facebook

Ka'idojin da aka gindayawa yan siyasa

Daya daga cikin ka’idojin shi ne hana baki amfani da mimbari sai don karanta kalmar Allah, domin kara girmama wurin ibada.

An bayyana damuwa kan yadda ake yi amfani da cocin wajen yada siyasa, wanda bisa cewarsa, na iya ɓata matsayin cocin.

Takardar da aka raba ga dukkan Fastoci ta jaddada cewa kowa ana maraba da shi, amma dole ne a kauce wa nuna goyon bayan siyasa.

Dukkan baki da za su yi jawabi dole su tattauna da shugabannin cocin da farko domin tabbatar da dacewar abubuwan da za su fada, Premium Times ta ruwaito.

Wike ya fadi dalilin shiga gwamnatin Tinubu

Kun ki cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan dalilin da ya sa ya shiga gwamnatin mai girma Bola Tinubu.

Nyesom Wike ya bayyana cewa ya shiga gwamnatin Tinubu a 2023 ne don ya yi amanna cewa ƴan Najeriya za su amfana da ita.

Ministan ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri domin ƙalubalen da ake fuskanta a ƙasar nan zai wuce nan ba ɗa jimawa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.