PDP Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Ministan Shari'a Ya Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar ADC
- Tsohon minista Hon. Musa Elayo Abdullahi ya sanar da ficewarsa daga PDP tare da komawa jam’iyyar hadaka ta ADC a Nasarawa
- A cikin wasiƙar murabus dinsa, Musa Elayo ya bayyana ficewarsa a matsayin sakamakon nazari mai zurfi da la’akari da manufofinsa
- Sauya shekar da Elayo ya yi zuwa ADC na iya ƙarfafa jam’iyyar a Nasarawa tare da janyo sababbin ƙawayen siyasa gabanin zaɓen 2027
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Nasarawa – A wani gagarumin sauyin siyasa, tsohon minista kuma fitaccen ɗan siyasa, Hon. Musa Elayo Abdullahi, ya fice daga jam’iyyar PDP a hukumance.
Musa Elayo Abdullahi, wanda tsohon karamin ministan shari’a ne, ya bayyana ficewarsa zuwa jam’iyyar hadaka ta ADC bayan barin PDP.

Source: Twitter
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata takardar murabus mai kwanan wata 10 ga Yulin 2025 kuma aka tura wa shugaban PDP na Iwagu Ward, karamar hukumar Keana, kamar yadda aka gani a shafin X na Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar.

Kara karanta wannan
ADC: An fara ƙoƙarin canza wa Atiku tunani, haɗaka na fuskantar gagarumar matsala
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin ficewar Musa Elayo daga PDP
A cikin takardar, Musa Elayo ya bayyana cewa shawarar da ya yanke ta biyo bayan nazari mai zurfi da kuma la'akari da ra'ayinsa na siyasa da ƙa'idojinsa.
Ya rubuta cewa:
"Na rubuta wannan takarda don sanar da ficewa ta a hukumance daga mamba na jam'iyyar PDP, mai tasiri daga 10 ga Yuli, 2025. Wannan shawarar ta biyo bayan dogon nazari da kuma la'akari da akidun siyasa da ka'idoji na."
Hon. Musa Elayo ya nuna godiya ga damarmaki da kuma kyakkyawar alakar da ya kulla da PDP tsawon shekaru 26 da suka gabata.
Ya ce:
"Duk da cewa ina gode wa jam'iyyar bisa damarmaki da alaƙar da PDP da al'ummar ta suka ba ni a cikin shekaru 26 da suka gabata, na yanke shawarar cire kaina daga mamba na jam'iyyar."
Tsohon ministan, wanda ya kasance mai ƙwazo wajen nuna muhimmancin dimokuraɗiyya da bin dokokin jam'iyya, ya kuma bayyana cewa ya fuskanci dakatarwa da kuma kalubalantar shari'a a ƙoƙarinsa na tabbatar da ƙa'idojin PDP.
Sakonsa ga shugabannin PDP da tasirin ficewarsa
Ga dukkan shugabannin PDP, Musa Elayo ya ce:
"Bana ɗauke da wata ƙiyayya ga kowane mamba na jam'iyyar, duk da cewa na taɓa shigar da ni ƙara kotu tare da fuskantar dakatarwa daga shugabancin jam'iyyar na jihar a ƙoƙarina na tabbatar da dimokuraɗiyyar cikin gida, da mutunta kundin tsarin mulkin jam'iyyar, da ka'idoji, da kuma hana cin zarafi. Ko yanzu,, na yafe wa duk wanda yake tunanin ya ɓata mini rai."

Source: Twitter
Sauya shekar da Elayo ya yi zuwa jam'iyyar ADC tana nuna wani babban ci gaba a fagen siyasar Nasarawa, inda manazarta ke hasashen yiwuwar sake daidaitawar siyasa gabanin babban zaɓen 2027.
Ana sa ran ficewarsa zai ƙara ƙarfin ADC a jihar kuma hakan na iya jawo karin ficewar manyan 'yan siyasa daga wasu jam'iyyu zuwa ADC yayin da ake tunkarar zaɓukan 2027.
Tsofaffin gwamnoni da ministocin da suka koma ADC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jiga-jigan siyasa a Najeriya sun sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC, inda suka kafa hadakar adawa mai karfi gabanin zaben 2027.

Kara karanta wannan
Tsohon jigo a PDP ya gano babbar matsalar jam'iyyar gabanin zaben 2027, "Atiku ne"
ADC na ci gaba da karbuwa a Najeriya yayin da rahotanni ke nuna cewa wasu gwamnoni da ministoci suna dab da sauya sheka zuwa jam'iyyar.
A wannan rahoton mun jero tsofaffin ministoci da tsofaffin gwamnoni irinsu Rotimi Amaechi, Mallam Nasir El-Rufai da suka shiga ADC domin kalubalantar AP da PDP a 2027.
Asali: Legit.ng
