'Allah Ya Kashe Su': Sheikh Ya Yi Addu'o'i ga Azzaluman Shugabanni a gaban Peter Obi

'Allah Ya Kashe Su': Sheikh Ya Yi Addu'o'i ga Azzaluman Shugabanni a gaban Peter Obi

  • Wani bidiyo ya bayyana lokacin da Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria ya yi addu’ar fatan mutuwar shugabannin da ba su da cancanta
  • Malamin ya yi addu'o'in ne a gaban dan takarar shugaban kasa a 2023, Peter Obi yayin ziyararsa a Kaduna
  • Sheikh ya yi addu'ar duk wanda ba zai zama alheri ba ga Najeriya idan ya ci zabe, Allah ya karɓi ransa kafin zabe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria yana addu’a mai zafi a gaban Peter Obi a Kaduna.

Yayin wata ziyara da Peter Obi ya kai jihar Kaduna, Sheikh Zaria ya yi addu’a mai tsanani game da azzaluman shugabanni a Najeriya.

Sheikh ya yi addu'o'i ga gurbatattun shugabanni
Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria ya yi addu'o'i ga azzaluman shugabanni a gaban Peter Obi. Hoto: Alkali Ustaz Abubakar Salihu Zaria.
Source: Facebook

Hakan na cikin wani faifan bidiyo da malamin ya wallafa a shafinsa na Facebook wanda mutane da dama ke tsokaci a kai.

Kara karanta wannan

Peter Obi: Siyasa za ta rikita Izala, Jingir ya yi wa Yusuf Sambo zazzafan raddi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Obi ya ziyarci Rigachukun a Kaduna

Wannan addu'o'i da Shehi ya zuba ya yi su ne a yayin da dan takarar shugaban kasa a 2023, Peter Obi ya kai musu ziyara.

Obi ya kai ziyara ta musamman a gidan Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun a gidansa da ke Rigachukun a jihar Kaduna.

Sheikh Rigachukun ya nuna jin dadinsa.kan wannan ziyara inda ya ba shi kyautar babbar riga da hula ta Hausawa.

Malam ya yi munanan addu'o'i ga shugabanni
Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria ya yi addu'o'i ga azzaluman shugabanni. Hoto: Peter Obi, Sheikh Alkali Abubakar Zaria.
Source: Facebook

Ruwan addu'o'i da Obi ya yiwa shugabanni

A lokacin da Peter Obi ya ziyarci cibiyoyin ilimi a Kaduna, malamin ya yi addu’ar Allah ya karɓi ran shugabanni marasa cancanta kafin zaɓe.

Sheikh ya ce:

“Duk wanda ba zai zama alheri ba ga Najeriya idan ya ci zabe, Allah ya karɓi ransa kafin zabe.
“Duk wanda zai zama masifa ga Najeriya, wanda a zamaninsa za a ci gaba da satar mutane da cin hanci, Allah ya kashe shi.”

Kara karanta wannan

ADC ta yi martani kan maganar yi wa Tinubu juyin mulki a Najeriya

Sheikh ya bayyana cewa cancanta, ba addini ba, ya kamata a duba wajen zaɓen shugabanni a Najeriya domin samun ci gaba da daidaito.

“Duk wanda zai zama alheri ga Najeriya, ko Musulmi ne ko Kirista, Allah ya ba shi nasara a zaɓen.”

- A cewarsa

Sheikh ya ja ayoyin Alkur'ani kan shugabanni

Sheikh Alkali ya ja ayoyi a Alƙur’ani yana nuna Allah ya halicci bambance-bambance domin a zauna lafiya tare a matsayin al’umma ɗaya.

Addu’ar ta haifar da muhawara, inda wasu ‘yan Najeriya ke yaba da irin ƙarfin zuciyar Sheikh wajen fuskantar rashin cancantar shugabanni.

An soki Sheikh kan halartar shirin Gabon

Mun ba ku labarin cewa amsa gayyatar Sheikh Alƙali Abubakar Salihu Zariya a shirin Hadiza Gabon ya haifar da muhawara a kafafen sada zumunta.

Wasu sun soki halartarsa, suna cewa bai dace malami ya shiga irin wannan dandali ba saboda yana rage daraja da mutuncinsa.

Sai dai wasu sun kare shi, suna cewa irin wannan dandali yana ba mutane dama su fahimci wasu ɓangarorin rayuwar shahararrun mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.